Tuwon Wake
i. Ruwa
ii. Wake
Ana tuwon wake ne kamar yadda ake tuwon alabo. Ana kai waƙe niƙa sannan a tankaɗe bayan an dawo da shi. Kamar dai yadda ake tuwon alabo, ana talgen tuwon wake da garin dawa ne. Bayan talge ya nuna, sai a sanya garin waken da aka tankaɗe a niƙa. Akwai mutanen da ba sa son tuwon wake.
Tuwon Ƙwai (Masar Ƙwai)
i.
Albasa
ii.
Attarugu
iii.
Gishiri
iv. Magi
v. Mai
vi. Ƙwai
Ƙwai ake fasawa daidai adadin tuwon da ake buƙatar
yi. Daga nan za a sanya magi da gishiri da tarugu da albasa cikin ƙwan.
Haka nan za a juye shi cikin firayin fan marar kamawa. Nan da nan zai kumbura
sai a juya ɗaya ɓangaren
domin shi ma ya gasu.
Bayan wannan nau’in da aka yi bayani a sama, ana iya soya
shi kamar yadda ake soya ƙwai
amma ba na tuwo ba, wato ta hanyar amfani da mai. Bambancin kawai shi ne,
wannan da yawa ake sanyawa sannan ba a kaɗa shi kafin a soya. Ana cin sa da
miyar ƙwai ko miyar
ganye.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.