Wanda Ya Ganni A Mafarki Zai Ganni A Fili

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Akramakallah shin akwai hadisin da ya tabbata daga manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) cewa yace '' man ra'ani fil manami fasayarani fil yaqzwa'' wato wanda ya ganni a mafarki to tabbas zai ganni a fili. To shin malam hakan tana yiwuwa, kuma har ma Annabin ya bada wata falala?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Ɗan'uwa wannan hadisi ne tabbatacce daga Annabi Sallallahu alaihi Wasallam kamar yadda Bukhari ya rawaito shi a hadisi mai lamba ta: 6592

    Saidai malamai sun yi saɓani game da lafazin zai ganni a fili, wasu sun ce: ma'anarsa: zai gan shi ranar alkiyama da sifa ta musamman , wasu kuma sun ce zai gan shi a duniya, saidai wannan zancen yana da rauni sosai, tun da hadisi ya tabbata cewa Annabawa suna cikin kabarinsu, wasu malaman kuma sun ce hadisin yana Magana ne akan wadanda suka zo a zamaninnsa, ma'ana duk wanda ya gan shi a mafarki, to zai haɗu da shi.

    Malamai suna cewa abin da ake nufi shi ne ka gan shi da siffofinsa wadanda suka tabbata a hadisi, inda za ka gan shi bakikkirin ba gemu, ko da mafarkin ya nuna maka Annabi ne to ba shi ba ne, tun da hakan ya saɓawa siffarsa a hadisi, wannan ya sa idan mutum ya zo ya cewa: Muhammad dan Siirin (RA) ya ga Annabi Sallallahu alaihi Wasallam a mafarki yakan ce masa siffanta min shi, in ya fadi kamannin da suka saɓawa hadisai, sai ya ce ba shi ka gani ba, an rawaito kwatankwacin haka daha Ibnu Abbas.

    Ba'a karɓar wani hukunci ko wata falala daga Annabi Sallallahu alaihi Wasallam a cikin mafarki, saboda hakan yana nuna tawayar addini, tare da cewa aya ta uku a cikin suratul Ma'ida ta nuna cikar addini, tun fiye da shekara dubu

    الْيَوْمَ أَكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُمْ وَأَتْمَمْتُ عَلَيْكُمْ نِعْمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ الْإِسْلَامَ دِينًا

    A yau Na kammala muku addininku, Kuma Na cika ni'imaTa a kanku, Kuma Na yarda da Musulunci ya zama addini a gare ku. (Suratul Maida aya 3)

    Don neman Karin bayani duba: Alminhaj na Nawawy 1/50 da kuma Fathul-bary 12/386.

    Allah ne mafi sani

    Jamilu Zarewa

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/EbkKRXdFzNu4F8aQZbZ1Vx

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.