𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Miji ne ya saki matarsa saki ɗaya,
amma sai yace ta zauna a gidansa ta yi iddah, to tana iddar kuma ya je mata
kamar sau uku yana Saduwa da ita sai daga baya ya ga ta yi jini uku saiya ce
wai iddarta ta kare za ta iya tafiya gida. to ya ya wannan mu'amalar da yayi da
ita akwai aure ko ya lalace sai an sake sabon daurin aure?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Idan mutum ya saki matarsa, kuma wannan sakin ya kasance shi
ne na farko ko na biyu to bata fita daga idda ba, idan ya so zai iya maido ta
da furuci, misali ya ce na maidoki ko na cigaba da rikonki. Ko ya maidata ta
hanyar wani aiki da yake nufin mayarwa, kamar ya kusanceta da niyyar mayarwa to
mayarwar ta yi.
Iddar macen datake haila shi ne: Al'ada uku (jini uku) idan
ta samu tsarki daga wannan jini ukun ta yi wanka, to tagama iddarta.
Iddar macen da bata haila saboda yarinta kota daina hailar,
wata uku ne za tayi.
Iddar mai ciki kuwa shi ne ta haife abinda ke cikinta,
abinda ya gudana na jima'i bayan wannan aikin haramun ne.
Wajibine Wannan mijin yatuba zuwaga Allah maɗaukakin sarki akan afkawa
jima'in dayayi tareda ke, bisa rashin kudurce komai na dawo dake ba, kuma ya
zama wajibi Ku sake daura wani auren da Sharuddansa na waliyyi da shedu da siga
da sadaqi idan kowannenku ya na kwadayin hakan.
Ba ya halatta a gareshi ya sake kusantar ki, harsai ansake
daura muku sabon Aure.
Saboda haka wannan kusantarki dayayi batareda qudurce yai
maidake ta sigogin da malamai suka tattauna wanda suke nuna mutum yadawo da
matarsa ba, haramunne yanzu agareshi yasake yi miki duk wani abu daya halatta
tsakanin miji da matarsa harsai an daura muku sabon Aure da sadaki da shaidu da
waliyyi.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.