Abubuwan da ake bukata idan za a yi masa 'yaryau:-
1- Gero.
2- Fulawa.
3- Sugar.
4- Yis.
5- Gishiri.
Mataki na farko
Da farko za ki surfa geronki gwangwani biyu ki bushe ki wanke sosai ki kai a markaɗa miki. (Kar a saka ruwa sosai a markaɗen mai kauri za a yi.)
Mataki na biyu
Bayan an markaɗa sai ki saka fulawa kamar rabin gwangwani a ciki.
Mataki na uku
Ki saka yis yadda zai isa.
Mataki na huɗu
Ki saka gishiri rabin cokali.
Mataki na biyar
Ki saka sugar kamar cokali uku.
Mataki na shida
Ki gauraya sosai komai da aka saka ya haɗe sosai. (A nan kina iya taɓawa idan akwai abin da bai miki ba sai ki qara, kamar sugar ko gishiri.)
Mataki na bakwai
Ki rufe ki bar shi ya tashi.
Mataki na takwas
Bayan ya tashi sai ki saka Baking powder rabin cokali ki gauraya sosai.
Mataki na tara
Ki ɗaura mai a kan wuta ya yi zafi daidai.
Mataki na goma
Ki dinga ɗiban wannan ƙullun kina jefawa a cikin mai kamar ƙosai haka har ki gama.
Mataki na sha ɗaya
Bayan kin gama sakawa ki dinga juyawa har ya soyu shikenan.
Mataki na sha biyu
Daga nan kin kammala, ana ci da yajin ƙarago. Yana da daɗi sosai.
A ci daɗi lafiya.
Ummu Amatulqahhar kitchen (Humaira'u) 📝🖊️
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.