𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Meye abun da yake wajibi akan
dattijo da bazai iya azumi ba, da mara lafiya da ba'a tsammanin warkewarsa??
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Imam Bukhari Allah ya masa rahama
yace "Amma tsoho mai girman shekaru da bazai iya azumi ba, Sahabi Anas ya
ciyar da abinci bayan ya girma tsawon shekara daya ko biyu, akowace rana yana
ciyar da miskini khubz da nama". Sahabi ibnu Abbas Allah ya masa rahama
yana cewa gameda mutumin da ya girma bazai iya azumi ba zai ciyar akowane rana
miskini guda ɗaya.
البخاري ٦/٣٠
Shaikh Ibnu baaz Allah ya masa
rahama yana cewa "Abinda yake kan wanda bazai iya azumi ba saboda girman
shekaru ko rashin lafiya da ba'a tsammanin warkewarsa ya ciyar da miskini guda ɗaya akullum idan zai iya,
kamar yadda dayawa daga cikin Sahabbai Allah ya ƙara yarda dasu sukayi fatawa akai, daga
cikinsu harda ibnu Abbas".
سبعون مسألة مهمة في الصيام
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.