Addu'ar Sallar Dare

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Wacce Addu'a Ce Idan Za'ai Sallar Dare Kiyamul Laili Ake Fada?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Muslim yaruwaito hadisi (771) da Nisa'i (897) daka Aliyu bin Abu dhalib Allah yakara masa yarda daka Annabi Sallallahu Alaihi wasallam (Idan yatashi zaiyi Sallah yana cewa

    ﻭَﺟَّﻬْﺖُ ﻭَﺟْﻬِﻲَ ﻟِﻠَّﺬِﻱ ﻓَﻄَﺮَﺍﻟﺴَّﻤَﺎﻭَﺍﺕِ ﻭَﺍﻟْﺄَﺭْﺽَ ﺣَﻨِﻴﻔًﺎ، ﻭَﻣَﺎ ﺃَﻧَﺎ ﻣِﻦَ ﺍﻟْﻤُﺸْﺮِﻛِﻴﻦَ، ﺇِﻥَّ ﺻَﻠَﺎﺗِﻲ، ﻭَﻧُﺴُﻜِﻲ، ﻭَﻣَﺤْﻴَﺎﻱَ ﻭَﻣَﻤَﺎﺗِﻲ ﻟِﻠَّﻪِ ﺭَﺏِّ ﺍﻟْﻌَﺎﻟَﻤِﻴﻦَ، ﻟَﺎ ﺷَﺮِﻳﻚَ ﻟَﻪُ، ﻭَﺑِﺬَﻟِﻚَ ﺃُﻣِﺮْﺕُ ﻭَﺃَﻧَﺎ ﻣِﻦَ ﺍﻟْﻤُﺴْﻠِﻤِﻴﻦَ، ﺍﻟﻠﻬُﻢَّ ﺃَﻧْﺖَ ﺍﻟْﻤَﻠِﻚُ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻟَّﺎ ﺃَﻧْﺖَ ﺃَﻧْﺖَ ﺭَﺑِّﻲ، ﻭَﺃَﻧَﺎ ﻋَﺒْﺪُﻙَ، ﻇَﻠَﻤْﺖُ ﻧَﻔْﺴِﻲ ، ﻭَﺍﻋْﺘَﺮَﻓْﺖُ ﺑِﺬَﻧْﺒِﻲ، ﻓَﺎﻏْﻔِﺮْ ﻟِﻲ ﺫُﻧُﻮﺑِﻲﺟَﻤِﻴﻌًﺎ،ﺇِﻧَّﻪُ ﻟَﺎ ﻳَﻐْﻔِﺮ ُﺍﻟﺬُّﻧُﻮﺏَ ﺇِﻟَّﺎ ﺃَﻧْﺖَ، ﻭَﺍﻫْﺪِﻧِﻲ ﻟِﺄَﺣْﺴَﻦِ ﺍﻟْﺄَﺧْﻠَﺎﻕِ ﻟَﺎ ﻳَﻬْﺪِﻱ ﻟِﺄَﺣْﺴَﻨِﻬَﺎ ﺇِﻟَّﺎ ﺃَﻧْﺖَ ، ﻭَﺍﺻْﺮِﻑْ ﻋَﻨِّﻲ ﺳَﻴِّﺌَﻬَﺎ ﻟَﺎ ﻳَﺼْﺮِﻑُ ﻋَﻨِّﻲ ﺳَﻴِّﺌَﻬَﺎ ﺇِﻟَّﺎ ﺃَﻧْﺖَ، ﻟَﺒَّﻴْﻚَ ﻭَﺳَﻌْﺪَﻳْﻚَ ﻭَﺍﻟْﺨَﻴْﺮُ ﻛُﻠُّﻪُ ﻓِﻲ ﻳَﺪَﻳْﻚَ، ﻭَﺍﻟﺸَّﺮُّ ﻟَﻴْﺲَ ﺇِﻟَﻴْﻚَ، ﺃَﻧَﺎ ﺑِﻚَ ﻭَﺇِﻟَﻴْﻚَ، ﺗَﺒَﺎﺭَﻛْﺖَ ﻭَﺗَﻌَﺎﻟَﻴْﺖَ، ﺃَﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭَﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ ‏

    Ibnul Qayyeem Allah yajikansa darahama acikin Zhadul Ma'adi ((1/196) yace: " Abun kiyayewa shi ne wannan addu'ar Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yakasance yana yinta asallar dare.

    Muslim yaruwaito hadisi (770) Daka Uwar Muminai Aisha Allah yakara mata yarda An tambayeta : Da wanne Abu Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yake buɗe sallah idan zaiyi Qiyamul Laili,? Sai tace: Yakasance idan zai sallar dare yana buɗe sallarsa da:.

    ﺍﻟﻠﻬُﻢَّ ﺭَﺏَّ ﺟَﺒْﺮَﺍﺋِﻴﻞَ ، ﻭَﻣِﻴﻜَﺎﺋِﻴﻞَ، ﻭَﺇِﺳْﺮَﺍﻓِﻴﻞَ ، ﻓَﺎﻃِﺮَ ﺍﻟﺴَّﻤَﺎﻭَﺍﺕِ ﻭَﺍﻟْﺄَﺭْﺽِ ، ﻋَﺎﻟِﻢَ ﺍﻟْﻐَﻴْﺐِ ﻭَﺍﻟﺸَّﻬَﺎﺩَﺓِ ، ﺃَﻧْﺖَ ﺗَﺤْﻜُﻢُ ﺑَﻴْﻦَ ﻋِﺒَﺎﺩِﻙَ ، ﻓِﻴﻤَﺎ ﻛَﺎﻧُﻮﺍ ﻓِﻴﻪِ ﻳَﺨْﺘَﻠِﻔُﻮﻥَ ، ﺍﻫْﺪِﻧِﻲ ﻟِﻤَﺎ ﺍﺧْﺘُﻠِﻒَ ﻓِﻴﻪِ ﻣِﻦَ ﺍﻟْﺤَﻖِّ ﺑِﺈِﺫْﻧِﻚَ ، ﺇِﻧَّﻚَ ﺗَﻬْﺪِﻱ ﻣَﻦْ ﺗَﺸَﺎﺀُ ﺇِﻟَﻰ ﺻِﺮَﺍﻁٍﻣُﺴْﺘَﻘِﻴﻢٍ ‏

    Bukhari yaruwaito (7499) da Muslim (1758) Daka Abdullahi dan Abbas Allah yakara yarda dasu yace: " Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yakasance idan zai sallar dare yana buɗe sallarsa da

    ‏ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻟَﻚَ ﺍﻟﺤَﻤْﺪُ ﺃَﻧْﺖَ ﻧُﻮﺭُ ﺍﻟﺴَّﻤَﻮَﺍﺕِ ﻭَﺍﻷَﺭْﺽِ، ﻭَﻟَﻚَ ﺍﻟﺤَﻤْﺪُ ﺃَﻧْﺖَ ﻗَﻴِّﻢُ ﺍﻟﺴَّﻤَﻮَﺍﺕِ ﻭَﺍﻷَﺭْﺽِ، ﻭَﻟَﻚَ ﺍﻟﺤَﻤْﺪُ ﺃَﻧْﺖَ ﺭَﺏُّ ﺍﻟﺴَّﻤَﻮَﺍﺕِ ﻭَﺍﻷَﺭْﺽِ ﻭَﻣَﻦْ ﻓِﻴﻬِﻦَّ، ﺃَﻧْﺖَ ﺍﻟﺤَﻖُّ، ﻭَﻭَﻋْﺪُﻙَ ﺍﻟﺤَﻖُّ ، ﻭَﻗَﻮْﻟُﻚَ ﺍﻟﺤَﻖُّ، ﻭَﻟِﻘَﺎﺅُﻙَ ﺍﻟﺤَﻖُّ ، ﻭَﺍﻟﺠَﻨَّﺔُ ﺣَﻖٌّ ، ﻭَﺍﻟﻨَّﺎﺭُ ﺣَﻖٌّ ، ﻭَﺍﻟﻨَّﺒِﻴُّﻮﻥَ ﺣَﻖٌّ، ﻭَﺍﻟﺴَّﺎﻋَﺔُ ﺣَﻖٌّ ، ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻟَﻚَ ﺃَﺳْﻠَﻤْﺖُ ، ﻭَﺑِﻚَ ﺁﻣَﻨْﺖُ، ﻭَﻋَﻠَﻴْﻚَ ﺗَﻮَﻛَّﻠْﺖُ ، ﻭَﺇِﻟَﻴْﻚَ ﺃَﻧَﺒْﺖُ ، ﻭَﺑِﻚَ ﺧَﺎﺻَﻤْﺖُ، ﻭَﺇِﻟَﻴْﻚَ ﺣَﺎﻛَﻤْﺖُ ، ﻓَﺎﻏْﻔِﺮْ ﻟِﻲ ﻣَﺎ ﻗَﺪَّﻣْﺖُ ﻭَﻣَﺎ ﺃَﺧَّﺮْﺕُ، ﻭَﻣَﺎ ﺃَﺳْﺮَﺭْﺕُ ﻭَﻣَﺎ ﺃَﻋْﻠَﻨْﺖُ ، ﺃَﻧْﺖَ ﺇِﻟَﻬِﻲ ﻻَ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻟَّﺎ ﺃَﻧْﺖَ .

    Waɗannan sune addu'o'i da'ake idan Mutum zaiyi sallar dare (Qiyamul laili).

    Wanda kesan karin bayani akan Abunda yashafi Addu'ar da'ake asallar nafila ta dare data rana da Sallar farillah yaduba (" Zhadul Ma'adi" Na Ibnul qayyem rahimahullah (1/195-199) da Sifatus salatin Nabiyyi Na shaik Albani rahimahullahu (shafi na 91-94)

    WALLAHU A'ALAM.

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.