Ticker

6/recent/ticker-posts

Alalen Zamani Da Yadda Ake Yin Su (Alalen Wake, Alale Mai Miya, Alale Mai Kwai, Alale Mai Ganye, Alale Mai Kayan Ciki, Alale Mai Kwai Da Kifi)

Abubuwan Da Ke Ciki

Gabatarwa

Alale  dai abinci ne mai saurin ƙosar da mutum kai tsaye, kamar dambu. Yayin samar da alale, akan yi amfani da wake  ne wanda ake markaɗawa bayan an gyara an wanke . Yanayin kayan haɗin da ake sanya masa kuma ya danganta da nau’in alalen da ake son yi. A ƙasa an kawo wasu daga cikin nau’o’in alale da ake samu a ƙasar Hausa . Wasu daga cikinsu gadajju ne daga iyaye da kakanni. Wasu kuwa an samu ilimin yin su ne a zamanance.

Alalen Wake

Kayan haɗin da za a tanada:

i. Albasa

ii. Gishiri

iii. Hanta

iv. Kabeji

v. Kayan Ƙamshi

vi. Kifi

vii. Man gyaɗa

viii. Ruwa

ix. Wake

Za a jiƙa wake  da ruwa, bayan ya jiƙa, sai a wanke  a surfe ; sannan a gyara a cire hancin. Daga nan, a wanke tarugu da tattasai da albasa  a zuba a ciki a niƙo su gaba ɗaya. Za kuma a nemo kabeji a yanka ƙanana a zuba a ciki, sai a saka kayan ƙamshi da gishiri da man gyaɗa . Za a ɗauko kifi da hantar da aka tafasa a yanka ƙanana-ƙanana a zuba a ciki. Daga nan za a zuba gwangwani ko leda a jera a cikin tukunya  domin dafawa. Yayin da ya nuna, za a ga ledar ta sake ƙullin alalen.

Alale Mai Miya

Kayan haɗin da za a tanada:

i. Alayyafu

ii. Albasa

iii. Gishiri

iv. Kayan ciki

v. Kayan yaji

vi. Magi

vii. Mai

viii. Ruwa

ix. Tarugu

x. Tattasai

xi. Tumatur

xii. Wake

Za a surfa wake  kamar yadda ya gabatar, sai a wanke  shi sosai. Haka ma, za a wanke tarugu da tattasai da albasa  a haɗe a markaɗa. Idan an kawo, za a zuba ɗan gishiri kaɗan a juya shi sosai a saka mai soyayye a cikin ƙulun a sake juyawa. Sannan a saka ƙulun a cikin gwangwani ko a leda. Yanzu mafi yawanci ana amfani da robobi  ƙanana maimakon gwangwani da leda duba da kula da lafiyar jama’a. Dalili kuwa shi ne, gwangwani zai iya yin tsatsa, wanda hakan na iya illa ga lafiya. Daga nan kuma za a hura wuta  a aza tukunya  a zuba ruwa a ciki sannan a jera robobin; wata saman wata. Sai kuma a samu leda a rufe a saka marfin tukunya a rufe.

A ɓangare guda kuwa, za a jajjaga tarugu da tattasai da tumatur a soya a saka kayan yaji a ciki. Sai a saka kayan ciki waɗanda da ma an riga da an tafasa su ba da ruwa ba. Za a yi sanwa a saka magi a ciki, idan ta tafaso, za a iya watsa alayyafu ba mai yawa ba. Wannan miya  da ita za a ci alalen wake .

Alale Mai Ƙwai a Tsakiya

Kayan haɗin da za a tanada:

i. Albasa

ii. Gishiri

iii. Magi

iv. Mai

v. Ƙwai

vi. Ruwa

vii. Tarugu

viii. Tattasai

ix. Wake

Shi ma wannan  nau’in alale ana samar da shi ne kamar dai yadda aka yi bayanin sauran da ke sama. Bambancin kawai shi ne, kafin a zuba ƙullun cikin leda ko gwangwani ko roba, to za a dafa ƙwai da gishiri. Bayan ƙwai ya dafu, sai a ɓare bayan. Wannan ɓararren ƙwai ne za a riƙa ɗauka ana sanyawa a cikin ƙullin alalen. Bayan ya dafu, ƙwan zai kasance a tsakiyar cikin alalen.

Alale Mai Ganye

Kayan haɗin da za a tanada:

i. Albasa

ii. Ganye

iii. Gishiri

iv. Kayan yaji

v. Magi

vi. Mai

vii. Ruwa

viii. Tarugu

ix. Tattasai

x. Wake

Shi ma alale mai ganye kamar yadda ake yin alale mai ƙwai a tsakiya ake yin sa. Inda suka bambanta shi ne, a wurin niƙa za a yanka ganye a saka cikin ƙullun alale. Daga nan za a jajjaga ƙullun sosai duk ya haɗe tare da ganyen , sai kuma a saka sauran kayan haɗin da ake buƙata.

Alale Mai Kayan Ciki

Kayan haɗin da za a tanada:

i. Albasa

ii. Gishiri

iii. Kayan ciki

iv. Kayan yaji

v. Magi

vi. Mai

vii. Ruwa

viii. Tarugu

ix. Tattasai

x. Wake

Shi ma haka za a yi kamar sauran alale da aka bayyana a sama. Sai dai a wurin sa kayan cikin za a tafasa su ba tare da ruwa ba, sai a saka albasa  da ɗan magi a ciki. Idan an niƙa ƙullun waken za a saka kayan ciki a ciki a motse. Bayan nan sai a saka sauran kayan haɗi a dafa da su tare.

Alalen Ƙwai da Kifi

Kayan haɗin da za a tanada:

i. Albasa

ii. Attarugu

iii. Gishiri

iv. Kayan Ƙamshi

v. Kifi

vi. Kori

vii. Magi

viii. Man gyaɗa

ix. Ƙwai

x. Ruwa

Shi ma wannan  alalen, ƙwai za a fasa a jiye gefe guda. Sai a ɗauko kifi a cire masa ƙaya sosai a juye a ciki a zuba magi da gishiri da kayan ƙamshi cikin ƙwan. Sannan kuma sai a jajjjaga tarugu da albasa  a zuba ciki, sai a ƙuƙƙulla a cikin leda kamar za a yi alale a ɗora kan wuta . Idan ya dahu sai a sauke a cire leda domin ya sha iska. Bayan ya sha iska ne kuma za a yayyanka. Daga nan a sake fasa wani ƙwai kamar guda uku ko huɗu, sai a dinga tsoma wannan alale cikin ruwan ƙwan ana soyawa da mangyaɗa mai zafi .

Kammalawa

Alale  dai ya kasance abinci ne sananne sosai a ƙasar Hausa . Kamar yadda aka bayyana a sama, wake  shi ne babban kayan haɗin irin wannan  nau’in abinci. Sai dai zamani ya zo da hanyoyi daban-daban da ake sarrafa shi.  

Citation (Manazartar Littafin):   Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

Get a copy:
To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
+2348133529736

You can also write an email to:

Post a Comment

0 Comments