An Saka Min Rana Sai Kuma Na Kamu Da Son Wata Daban

    TAMBAYA (83)

    Aslm Allah ya kar6i aikin malam Dan Allah tambaya ta shine inada budurwa hartaki an kai ga samin Rana sai Na ga wata taburgeni shin zan iya zuwa zance wurinta kokuma saidai bayan bikin nawa ya halarta nasake kula wata

    AMSA

    Waalaikumussalam warahmatullahi wabarakatuhum

    Alhamdulillah

    Idan na fahimce ka, kanada ra'ayin auren mace sama da daya saboda wani dalili na kashin kanka. Hakan koyi da Sunnah ne amman fa in kayi da kyakkyawar niyya sannan kuma idan kanada ikon yin adalci garesu

    Idan kyau ne silar da tasa ka kula waccan sabuwar budurwar to ka sani a kullum za ka yi ta kule kulen yan mata ne, domin kuwa kyawawa dai kam in har kullum zaka fita to sai ka gaji da ganinsu

    Hanzarin me kake. Ba kyau yin gaggawa a cikin al'amura. Sannu sannu bata hana zuwa. Idan kanada ra'ayin auren mata biyu a lokaci guda wannan ba laifi bane ba indai har kanada sana'ar da zaka iya kulawa da su. To amman tunda an saka maka rana ka tsaya mana ka san abinda ya kamata kayi wajen shirye shiryen ganin komai ya tafi yanda ya kamata

    Sannan kuma yawan zuwa zance yana iya bude kofar barna. Abinda yake a shari'ah shine: idan ka ga mace ta kwanta maka a ranka. To kada ka bi son ranka, a'a, ka tattara al'amarin ka miqa shi zuwa ga Allah Azzawajallah ta hanyar yin addu'ar da Annabi Sallallahu alaihi wasallam ya koyar damu wato addu'ar Istikhara. Ka fara bawa Allah zabi tukunna. Idan akwai alkhairi zaka gani akasin haka ma zaka gani. Sannan kuma sai ka bincike halayenta da alaqar ta da iyayenta. Ka fara duba yaya halin mahaifiyar ta yake, ya take biyayya ga mijinta. Saboda ai da na gaba ake gane zurfin ruwa. Dabi'un mahaifiya suna da matuqar tasiri wajen gane halayen yayanta musamman mata. Sannan sai ka tura waliyyanka suyi magana gemu da gemu. Kafin wani late comer yazo ya kasa ka, azo ana ta dana sani, da hausawa kan kira ta da keya. Daganan sai kuje asibiti ayi muku test saboda kada aje soyayya ta yi dadi azo ace ai waninku yanada cuta iri kaza da kaza, maganin kar ayi kar a fara. To ammanfa duk da haka kowacce cuta saidai Allah ash-Shafi' ya saukarda maganinta tun ma kafin ya halicci cutar

    Ka ci gaba da miqawa Allah zabinSa akan neman auren ta farkon saboda kada kaje ka saki reshe ka kama mujiya, aje ayi ba wan ba kanin, ma'ana garin neman gira ka rasa ido, kai baka auri ta farkon ba kuma idan ta tabbatar da kana zuwa wajen wata zance, abinda zai fara zuwa ran ta shine; zan auri miji mai yaudara, mai kule kulen yan mata

     

    Wasu mazajen suna kafa hujja da ai namiji mijin mace 4 ne, eh wannan haka yake amman indai zai iya adalci a tsakaninsu ba (Kamar yanda hakan ya tabbata a cikin Qur'ani Mai girma)

    Idan waccan baiwar Allah din ta tabbatar da halinka na yawan kule-kulen yan mata to gaskiya kimar ka zata zube a idanunta. To don gudun hakan ta faru, gwara ka riqe dahir ka saki gaibu

    Wannan shine yar taqaitacciyar shawarata a gareka. Sannan kuma a karshe zanso ka shiga makarantar koyar da rayuwar auratayya a musulunci bisa koyarwar sunnar Annabi Sallallahu alaihi wasallam. Karanta littafin "Guidelines To Intimacy in Islam" zai taimaka matuqa da kuma littafin "Rijali Haular Rasul"

    Ina roqon Allah ya yi maka zabin alkhairi

    Masu aure kuma, Allah ya basu ikon cin jarabawar haqurin zamantakewa. Gwauraye kuma Allah ya kawo manema nagari

    Wallahu ta'ala a'alam

    Amsawa:

    Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.