𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Salamun alaikum, Dr. Tambaya ce
aka jefa mani ina gabatar da darasi wa mata a garin Firji: mace ce mijinta bai
yarda ya ɗauki azumi
ba sai ya ga wata da kansa (bai yarda da sanarwar Sarkin Musulmi ba), to inda
mushkilar take shi ne, ita matarsa ta yarda da sanarwar Sarkin Musulmi amma sai
ya ce kada ta kuskura ta dauki azumin, to shin minene matsayinta? Domin ta
ajiye azumin saboda tsoron kada ya wulaqanta ta.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikum assalam A Zahiri ba za
ta masa biyayya a nan ba, Tun da Azumi rukuni ne daga cikin ginshikan
musulunci. Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam yana cewa
إنما الطاعة في المعروف
Ana yiwa jagora biyayya ne idan
ya yi umarni da abinda ya dace da sharia"
Sannan yana cewa: "Ana yin
azumi ne ranar da mutane suke yin azumi"
Allah ne mafi sani
Amsawa✍🏻
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.