Ticker

Banbancin Ruwan Dake Zuba A Gaban Mace

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam yazan gane banbance ruwan dake zuba a gaban mace. Allah ya biyaka taimakon da kake mana.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Toh kamar yanda kowa yasani gaban mace baya rabuwa da jika ko na ni'ima ko kuma na cuta ya danganta da irin ruwan.

Idan akace farin ruwa ana nufin fari kal me kamar ruwan famfo shine yake zama na ni'ima kuma yanada yauki sannan yanada ɗanɗano wani kamar gishiri ya danganta da irin abunda mace kesha.

saidai mata da yawa farkon saduwa akwai wani farin ruwa me kamar nono dan kaɗan yana fitowa wannan wani ruwane wanda ba kowacce mace ke samuba domin da yawa mace daga ta fara haihuwa shikenan kuma wannan ruwane na musamman ga wata mace.

wani ruwan kuma yauki zakaga yanayi kuma haka kawai mace ko zance tayi da namiji zataganshi kuma me irin wannan ruwan bata taɓa bushewar gaba kuma daban take acikin mata

shikuma ruwa na cuta haka kawai yake zuwa agaban mace kuma bayan farine me kamar majina zakaganshi guda guda wani kuma kamar zare zare kuma ruwan yana iya canja kala daban daban wani yakoma Green wani brown kuma sauda dama warinsa yana zama kamar na danye kifi akwai kuma me warin danyen kwai.

wani ruwan kuma kamar mace me ciki tana yawan ganinsa musamman bayan gama saduwa ko kuma bayan ta gama fitsari wannan shikuma dattine na mahaifa shima ba matsala bane

dalilai da yawa suna saka mata kamuwa da ciwon sanyi saboda idan namiji yanadashi zai iya sakawa mace ga kuma shiga kowanne toilet ko wajen tsugo a toilet sannan kuma koda mata huɗu ne agida aka samu ɗaya me wannan cutar tana iya sakawa sauran shiyasa mata masu hikima basa rabuwa da riga kafin cutar wato kamar sabulai da ruwan magarya da amfanida gishiri da sauransu.

Allah ta'ala yasa mudace

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam


Post a Comment

0 Comments