Banbancin Sallar Tarawi Da Tahajjud

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamun alaikum Malam nakanji ana cewa Tarawih da Tahajjud shin menene bambancinsu?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salam Warahmatullahi Wabarkatuhu.

    To bayin Allah Sallar tarawihi da tahajjud duk ana kiransu Sallar dare wato tsayuwar dare kenan illla iyaka lokacin yinsu ne kawai ya bambanta su har sunan nasu shima ya bambanta.

    TARAWIHI: shine ayi sallar dare kafin ayi barci kamar dai yadda masallatanmu sukeyinta bayan isha'i cikin watan ramadan to idan akayi sallar kafin ayi bacci shine ake kiranta da tarawihi.

    TAHAJJUD: itace ake yinta bayan an ɗan yi bacci an farka to wannan baccin da akayi aka farka sannan akayi sallar to shine yasa ake kiranta da tahajjud maimakon tarawihi Amma dai dukkansu A dunkule tsayuwar dare ko kuma ince sallar dare ake kiransu.

    WALLAHU A'ALAM

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/Fc3hX6HoDt65aKhhKOiDpX

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.