𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum. Wane irin
yanayin ciwo ne ke sanya mara lafiya ya ciyar? Ko olsa mai tsanani na iya shiga
ciki?
𝐀𝐌𝐒��❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul
Laah.
Allaah dai cewa ya yi
وَمَنْ كَانَ مَرِيضًا أَوْ عَلَى سَفَرٍ فَعِدَّةٌ
مِنْ أَيَّامٍ أُخَرَ يُرِيدُ اللَّهُ بِكُمُ الْيُسْرَ وَلَا يُرِيدُ بِكُمُ الْعُسْر
Kuma wanda ya zama mara lafiya ko
a cikin tafiya to sai ya biya a waɗansu
adadin kwanaki na daban. Allaah yana nufin sauƙi ne gare ku, kuma baya nufin tsanani a
gare ku. (Surah Al-Baqarah: 185).
A ƙarƙashin wannan ayar duk wanda ya shiga
halin da za a kira shi mara lafiya ko matafiyi, to ya halatta ya ajiye azuminsa,
ya rama a lokacin da ya samu iko.
Al-Qurtubiy a cikin Tafsirinsa:
Al-Jaami’u Li Ahkaamil Qur’aan ya kawo bambancin fahimtar malamai a kan wannan
matsalar ta azumin mara lafiya, a ƙarshe kuma ya zaɓi maganar Muhammad Bn Seereen (Rahimahul
Laah) wanda ya ce:
مَتَى حَصَلَ الْإِنْسَانُ فِي حَالٍ يَسْتَحِقُّ
بِهَا اسْمَ الْمَرَضِ صَحَّ الْفِطْرُ، قِيَاسًا عَلَى الْمُسَافِرِ لِعِلَّةِ السَّفَرِ،
وَإِنْ لَمْ تَدْعُ إِلَى الْفِطْرِ ضرورة.
Duk lokacin da mutum ya shiga
wani halin da ya cancanta sunan rashin lafiya ya hau kansa, to ajiye azumi ya
inganta a gare shi. Wannan ƙiyasi ne a kan matafiyi saboda dalilin
tafiya, ko da kuwa babu wata larurar da ta takura masa ga ajiye azumin.
(Tafseer Al-Qurtubiy: 2/276).
Daga nan sai kuma ya kawo ƙissar
Al-Imaam Al-Bukhaariy (Rahimahul Laah) wanda shi kuma ya ce
اعْتَلَلْتُ بِنَيْسَابُورَ عِلَّةً خَفِيفَةً
وَذَلِكَ فِي شَهْرِ رَمَضَانَ، فَعَادَنِي إِسْحَاقُ بْنُ رَاهْوَيْهِ نَفَرٍ مِنْ
أَصْحَابِهِ فَقَالَ لِي: أَفْطَرْتَ يَا أَبَا عَبْدِ اللَّهِ؟ فَقُلْتُ نَعَمْ. فَقَالَ:
خَشِيتَ أَنْ تَضْعُفَ عَنْ قَبُولِ الرُّخْصَةِ. قُلْتُ: حَدَّثَنَا عَبْدَانُ عَنِ
ابْنِ الْمُبَارَكِ عَنِ ابْنِ جُرَيْجٍ قَالَ قُلْتُ لِعَطَاءٍ: مِنْ أَيُّ الْمَرَضِ
أُفْطِرُ؟ قَالَ: مِنْ أَيِّ مَرَضٍ كَانَ، كَمَا قَالَ اللَّهُ تَعَالَى:" فَمَنْ
كانَ مِنْكُمْ مَرِيضاً"
Na yi ɗan rashin lafiya ba wani mai tsanani ba a
garin Naisabur a watan Ramadan, sai Ishaaq Bn Rahwuyah da wasu ɗalibansa suka zo duba ni.
Sai ya ce mini: ‘Baban Abdullahi, ka ajiye azumin ko?’ Na ce: ‘E.’ Ya ce: ‘Wato
ka ji tsoron kar ka yi rauni a karɓar
sassaucin ne ko?’ Sai na ce: Malaminmu Abdaanu ne ya ba mu hadisi daga Ibn
Al-Mubaarak, shi kuma daga Ibn Juraij, ya ce: Na tambayi Ataa’u: ‘Wai wane irin
rashin lafiya ne yake janyo a ajiye azumi?’ Sai ya ce: ‘Kowane irin rashin
lafiya kawai. Kamar yadda Allaah Ta’aala ya ce: ‘Duk wanda ya zama mara lafiya
a cikinku.’ (Tafseer Al-Qurtubiy: 2/277)
Wannan a kan rashin lafiyar da
ake sa ran yiwuwar warkewa kenan.
Amma idan rashin lafiya mai
tsanani ne wanda ake da marinjayin zaton cewa abu ne mawuyaci a warke, to sai
malamai suka yi kiyasin mai larurar da kamar tsofaffi waɗanda Ubangiji Ta’aala ya faɗa a kansu cewa
وَعَلَى الَّذِينَ يُطِيقُونَهُ فِدْيَةٌ طَعَامُ
مِسْكِين
Kuma yana a kan waɗanda suke ɗaukar
Azumin da wahala bayar da fansa na abincin musakai. (Surah Al-Baqarah: 184).
Kuma babban malamin Tafsiri a
cikin Sahabbai, wato Ibn Abbaas (Radiyal Laahu Anhumaa) ya ce
لَيْسَتْ بِمَنْسُوخَةٍ، هُوَ الشَّيْخُ الْكَبِيرُ
وَالْمَرْأَةُ الْكَبِيرَةُ لَا يَسْتَطِيعَانِ أَنْ يَصُومَا، فَيُطْعِمَا مَكَانَ
كُلِّ يَوْمٍ مِسْكِينًا
Ita wannan ayar ba shafaffiya ba
ce. Tsoho da tsohuwa ne waɗanda
suka yi girma a shekaru har ba su iya yin azumin, sai su ciyar da abinci ga
talaka a maimakon kowane yini guda. (Sahihi ne. Tafseer Al-Qurtubiy: 2/288).
Amma a kan rashin lafiya irin na
olsa malamai sun nuna cewa, da ikon Allaah ana iya warkewa idan aka dace da
magani. A ƙarƙashin
haka, ba za a ce mai fama da larurar ya ciyar ba, sai fa idan bashi da iko da ƙarfin
kai wa ga maganin.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah
Asslafiy
Ga masu tambaya sai su turo ta
WhatsApp number: 08021117734
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.