Dafa-Dukan Shinkafa Da Na Shinkafa Da Wake Da Dafa-Duka Mai Kayan Hadi Da Yawa

    Abubuwan Da Ke Ciki

    Dafa-Dukan Shinkafa

    a. Albasa

    b. Gishiri

    c. Kayan Yaji

    d. Magi

    e. Mai

    f. Ruwa

    g. Shinkafa

    h. Tarugu

    i. Tattasai

    j. Tumatur

    An kawo bayanin dafa-dukan shinkafa a Æ™ ar Æ™ ashin 9.1.1 da ke babi na tara. Yana da kyau a lura cewa, dafa-dukan shinkafa a yau na da bambanci matu Æ™ a da ta gargajiya. A zamanance akan sarrafa dafa-dukan shinkafa cikin nau’o’i da salailai daban-daban. Yayin samar da dafa-dukan shinkafa a yau, ana iya ha É— a shinkafar da É— aya ko fiye daga cikin wa É— annan:

    a. Dankalin Hausa

    b. Dankalin Turawa

    c. Doya

    d. Makaroni

    e. Taliya

    f. Wake

    Dafa-Dukan Shinkafa  da Wake

    a. Albasa

    b. Gishiri

    c. Kayan ciki

    d. Kayan yaji

    e. Magi

    f. Mai

    g. Ruwa

    h. Shinkafa

    i. Tarugu

    j. Tattasai

    k. Tumatur

    l. Wake

    Ita ma wannan  dafa-duka kamar wadda ta gabata ta ke. Za a dafa wake  daban a kuma tafasa kayan ciki da Albasa . Sannan za a jajjaga kayan miya  da kayan yaji a soya. Daga nan a tafasa shinkafa daban. Sai kuma a yi sanwa a saka magi da gishiri tare da kayan ciki. Idan ta tafasa sai a saka waken da aka dafa tare da shinkafa. Idan ta yi a sauke tukunya .

    Dafa-Duka Mai  Kayan HaÉ—i da Yawa

    i. Alayyafu

    ii. Albasa

    iii. Doya

    iv. Kabbaji

    v. Karas

    vi. Kayan yaji

    vii. Kori

    viii. Magi

    ix. Mai

    x. Makaroni

    xi. Naman kaza ko nama da kifi

    xii. Ruwa

    xiii. Shinkafa

    xiv. Taliya

    xv. Tarugu

    xvi. Tattasai

    xvii. Tumatur

    xviii. Wake

    Ita ma wannan  dafa-duka zamani ne ya zo da ita, Bahaushe  ya sami fasahar gudanar da ita ne a dalilin cu É— anyarsa da wasu al’ummomi dabn-daban. A duk lokacin da aka Æ™ uduri aniyar gudanar da ita, da farko za a wanke  alayyafu da albasa  da kabeji da karas a yanka a aje a gefe. Sannan a jajjaga tarugu da tattasai da albasa da tumatur wuri É—aya kar a niÆ™a shi sosai kamar na miyar tumatur, ana saka masa ’yar kanwa a ciki kaÉ—an don ta gusar da tsami . Za kuma a tafasa nama da gishiri da magi da kori a aje gefe, idan kuma kifi ne, a É—anyensa za a tafasa shi, in kuma busasshe ne za a saka ruwan zafi  a wanke shi a cire masa Æ™aya ajiye domin ya tsane.

    Za a yanka doya Æ™anana-Æ™anana a wanke  wake  a tafasa sannan ajiye gefe guda. Za a dafa shinkafa tafasa guda a sauke. Daga nan sai a soya nama a cire shi, sai kuma a soya jajjage. Idan ya soyu a saka kayan yaji da tafarnuwa. Za a yi sanwa tare da ruwan nama, idan kifi ne ba za a saka shi ba, sai a saka magi da gishiri da kori. In ya tafasa za a saka shinkafa da doya da wake a bar su zuwa wani lokaci, sai a saka taliya da makaroni. Idan suka É—an jima, sai a saka kabeji da alayyafu da karas sannan a yanka albasa . Yana da kyau a kula da adadin ruwan da za a sa yayin sanwa, domin yawaita ruwa na sanya abincin ya kwaÉ“e.


    Citation (Manazartar Littafin):   Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

    Get a copy:
    To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
    +2348133529736

    You can also write an email to:

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.