Ticker

Dambu Da Ire-Irensa a Abincin Hausawa (Dambun Gero, Dambun Shinkafa, Dambun Acca, Dambun Dankali, Dambun Kuskus)

Gabatarwa

A babi n a goma sha biyu, an kawo bayanan irin dabarun da ake amfani da su a sarrafa dambu a gargajiyance. Har ila yau, an kawo misalan nau’o’in dambun gargajiya a ƙ asan babin. Akwai sauye-sauye tsakanin dambun gargajiya da na zamani. Wa ɗ annan sauye-sauye ba su wuce na nau’o’in kayan ha ɗ i da yanayin sarrafawa ba. Wannan babi na ashirin da shida, zai mayar da hankali ne kan fito da yadda ake sarrafa dambu a zamanance.

Dambun Gero

Dambun gero  na zamani ba shi da wani bambanci na a-zo-a-gani tsakaninsa da na gargajiya. An kawo cikakken bayani dangane da dambun gero na gargajiya a ƙ a r ƙ ashin 12.2.1 da ke babi na goma sha biyu. Bambancin da ke tsakaninsu ya fi shafar kayan ha ɗ i ne. A ƙ asa an lissafo jerin kayan ha ɗ in da ake amfani da su yayin samar da dambun gero a zamanance.

a. Albasa

b. Gero

c.  Kanwa

d. Magi

e. Kayan ƙ amshi

f. Mai

g. Ƙ ulli

h. Rama ko Zogale

i. Ruwa

j. Tonka

Bayan wannan  nau’i na dambu da ke kama da na gargajiya, akwai wasu nau’o’in dambun da suka yi kama da na gargajiya idan aka yi la’akari da yadda ake samar da su. Misali , dambun masa da dambun tsakin masara , yadda ake samar da su a gargajiyance, haka ake samar da su a zamanance. Dambun da ke da matu ƙ ar bambanci ta fuskar kayan ha ɗ i tsakanin na gargajiya da na zamani shi ne dambun shinkafa.

Dambun Shinkafa

a. Albasa

b. Gishiri

c. Kabeji

d.  Karas

e. Kayan yaji

f. Magi

g. Mai

h. Nama (idan da hali)

i. Ruwa

j. Shinkafa

k. Tafarnuwa

l. Tarugu

m. Tattasai

n. Zogale

Shi ma dambun shinkafa a can da ana yin sa cikin sigar da aka yi na masara  ko gero . Wato ba a saka masa komai, sai an gama za a saka mai da yaji sannan a ci. A ta ƙ aice, dukkaninsu dai, da dambun geron da na masarar dafuwa guda ake musu a cire su a ci. Amma yanzu da zamani ya zo, sai aka sauya wa dambun samfiri ta hanyar amfani da kayan lambu iri-iri. Da farko a nau’in wannan  dambu, za a ɗauko shinkafa ta Bature ko tamu ta gida a fece a cire mata tsakuwa . Daga nan sai a ɓarzo ta. Idan an dawo daga barzin, za a tankaɗe a cire garin sannan a wanke . A gefe guda kuwa, za a wanke zogale  sosai a aje; sai kuma a hura wuta .

Da farko, za a gauraya wannan  shinkafar da aka ɓarzo tare da ganyen  zogalen. Daga nan sai a ɗora ta bisa wuta  kamar yadda ake yi ga sauran nau’o’in dambun da aka yi bayanin su a sama, wato cikin madambaci. Bayan shinkafar da wannan ganyen sun dafu, to za a sauƙe a zuba bisa tire ko wani babban wurin zuba abinci domin ya huce. A lokacin da aka fito da shi, za a tarar da duk ya duddunƙule. A saboda haka za a sa hanu ko wani abu domin a barbaza shi.

Bayan an ajiye shi ya sha iska, sai kuma a sake mayar da shi cikin madambaci kamar yadda aka yi a karon farko. Za a bar shi a saman wuta  har sai ya fara ƙamshi, inda za a sake sauƙewa a juye a tire a bar shi domin ya sha iska. A wannan  gaɓa, a gefe guda sai a tanadi:

i. Dakakken kayan yaji tare da tafarnuwa

ii. Dakakken magi

iii. Jajjagen kayan miya

iv. Karas da aka wanke aka yayyanka

v. Soyayyen mangyaɗa

vi. Tafasasshen nama (shi ma za a yanka shi ƙanana-ƙanana, ko ma a ɗan kikkirɓa shi)

Bayan dambun da aka baza kan tire ya bushe, sai a sanya waɗannan kayan haɗi da aka ambata a sama a gauraya. Daga nan za a sake mayar da shi cikin madambaci na ƙanƙanin lokaci, ko da mintuna biyar ne. Da an kammala wannan , to dambun shinkafa ya haɗu.

Dambun Alkama

Wannan nau’in dambu yana matuƙar kama da na gero , duk kuwa da sun bambanta ta wasu ɓangarori. Kayan haɗin da ake tanada sun haɗa da:

i. Albasa

ii. Alkama

iii. Kabeji

iv. Karas

v. Kayan Ƙamshi

vi. Magi

vii. Mai

viii. Ruwa

ix. Tarugu

x. Tattasai

Alkama  za a ɓarza a wanke  da ruwan ɗumi, sannan a tsane da matsani a matakin farko. Daga nan sai a dafa ƙoda tare da hanta da kayan ƙamshi haɗi da magi. Idan sun dafu sosai, za a gungunta nama sai a zuba shi saman tsakin alkama. Sannan sai a yanka kabeji da karas tare da albasa  da tarugu da tattasai a zuba a samansa. Za kuma a sanya sauran kayan ƙamshi da magi. Daga nan sai a zuba su a cikin madambaci. Haka za a bar shi har sai ya dafu.

Dambun Acca

Kusan za a iya cewa yadda ake dambun alkama haka ake yin na acca. Wurin da suka bambanta kawai shi ne, acca ba ta kai alkama ƙarfi ba. Saboda da haka, yayin samar da dambun acca akan ɗan yayyafa ruwa ne kawai. Ma’ana dai, ba a sanya mata ruwa da yawa kwatankwacin yadda ake sanya wa alkama saboda tsoron yadda za ta koma idan ta jiƙe da yawa. Ta ɓangaren kayan haɗi kuwa, za a iya cewa duk ɗaya suke da na alkama.

Dambun Dankali

Wannan ma wani nau’i ne na dambu, kayan haɗin da ake amfani da su yayin samar da shi sun haɗa da:

i. Albasa

ii. Dankali

iii. Gishiri

iv. Kori

v. Magi

vi. Ruwa

vii. Tarugu

viii. Tattatsai

Yadda ake yin wannan  nau’i na dambu kuwa shi ne, za a fere  dankali a soya, amma ba a so ya soyu sosai. Idan an ga ya ɗauko soyuwa , sai a ɗauko tattasai da tarugu da albasa  a yanka su a zuba a saman dankalin. Za a yi ta juyawa yana dagargajewa sannu-sannu.

Dambun Kuskus

Kuskus dai nau’in abinci ne da ba na gargajiyar Bahaushe  ba. Yawanci akan sayar da shi ne a kantuna. Sau da dama ma akan shigo da shi ne daga ƙasashen ƙetare. Yayin sarrafa shi a matsayin dambu, akan tanadi kayan haɗin da suka haɗa da:

i. Alayyafu

ii. Albasa

iii. Attarugu

iv. Karas

v. Kayan Ƙamshi

vi. Kori

vii. Kuskus

viii. Magi

ix. Mai

x. Nama

xi. Ruwa

xii. Tattasai                            

Shi ma dambun kuskus za a yi shi ne kamar yadda ake yin dambun alkama. Sai dai shi ba a wanke  shi saboda a tsaftace yake zuwa a cikin leda ta musamman. Idan an yi jajjage da kayan ƙamshi, za a zuba su a saman kuskus a yanka albasa  da karas da allayyahu duk a lokaci guda. Za kuma a saka magi da kayan ƙamshi a zuba su tare a kwaɓe da kuskus. Ba a saka ruwa a ciki yayin samar da wannan  dambu. Ruwan da ke cikin jajjagen da aka yi ya wadatar, kuma da shi ne za a kwaɓa shi. Saboda kuskus ba shi da ƙarfi sosai, nan da nan yake nuna. Za a saka shi a madambacin tukunya  inda tiriri da zafin ruwan da ke ƙasan madambacin (cikin tukunya) zai dafa shi.

Burabusko

Wannan nau’in dambu ma da shinkafa ake yin sa, sai dai ana niƙo ta ne da laushi. Bayan an yiwo niƙan, za a riƙa gaurayawa a hankali ana yi ana zuba ruwa sannu a hankali har ya zama gudaji-gudaji. A wannan  gaɓa ne kuma za a saka shi cikin madambaci. Sai dai shi akan bar shi da ruwa-ruwa ba kamar sauran nau’o’in dambu ba. Bayan an fitar da shi daga cikin madambacin ne kuma za a sanya masa kayan haɗin da suka haɗa da:

i. Albasa

ii. Attarugu

iii. Kori

iv. Mai

Bayan an sanya waɗannan kayan haɗi, za a sake mayar da shi kan wuta  na ƙanƙanin lokaci. Yayin da ya dahu, zai fito a gudajinsa, ba tare da ya watse ba.

Kammalawa

Kamar yadda aka gani a sama, dambu abinci ne da ya fi kama da na ƙwalama. Yawanci akan ci shi a marmarce, musamman idan an yi masa haɗi na a-zo-a-gani. An fi cin dambu a matsayin abincin rana, koma bayan na dare ko na safe. Kamar yadda bayanai suka zo a sama, yawancin nau’o’in dambun da Hausawa  ke samarwa ba su da wahala. 

Citation (Manazartar Littafin):   Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

Get a copy:
To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
+2348133529736

You can also write an email to:

Post a Comment

0 Comments