Ticker

6/recent/ticker-posts

Furar Gero Da Furar Maiwa Da Furar Shinkafa

Furar Gero

i. Gero             

ii. Kayan yaji             

iii. Nono

iv. Ruwa         

v. Ma ɗ i ko Zuma (idan an ga dama)

Za a surfe  gero  a wanke  domin a cire dusa r da ke jikinsa, sannan a ajiye shi ya tsane. Daga nan za a sanya kayan ƙ amshi domin a daka. Za a iya rage wani adadi na geron kafin a kai ni ƙ a. Bayan an kammala, za a tanka ɗ e garin. Sai kuma a ha ɗ e garin da surfaffen geron da aka rage ( ajiye ) lokacin da za a kai ni ƙ a . Sai dai za a rage gari  ka ɗ an a jiye gefe guda. A wannan  ga ɓ a akan samu za ɓ i guda biyu, ko dai dambu ko kuma gumba.

Ga masu yin dambu, za a zuba wannan  gari  da surfaffen gero  cikin turmi  sannan a yi amfani da ta ɓ arya domin sake rib ɗ awa. Sannan za a ɗ an yayyafa masa ruwa domin y a harha ɗ e ka ɗ an. A gefe guda kuwa , an aza tukunya  da ruwa a bisa wuta . Da zarar ruwan ya fara tafasa, sai a ri ƙ a ɗ auko wannan gari ana dun ƙ ulawa domin tsomawa cikin tukunyar. Kafin a sanya, za a ɗ an hu d a dun ƙ ulen da yatsa wanda hakan ne zai ba wa ruwan zafin damar ratsawa ko’ina. Bayan an kammala sakawa, za a rufe tukunya domin a bar shi ya dahu. Yadda ake gane ya dahu kuwa shi ne, zai taso sama. Bayan ya nuna , za a cire a sanya shi cikin turmi. Za a yi ta dakawa tare da ƙ ara ruwan zafi  har sai ya yi laushi sannan ya yi dan ƙ o. Daga nan za a juye cikin ƙ warya , sannan a sake juya shi , s ai kuma a fara yanka wa  da hannu ana mulmulawa ana ajiyewa cikin wata ƙ warya daban. Bayan an kamala , sai a ɗ auko garin nan da aka rage sannan a zuba kai, a jujjuya domin kowane ƙ wallon dawo ya zama ya baibaiyu da garin.

Idan kuma dawon gumba za a yi, bayan an dawo daga ni ƙ a za a tanka ɗ e a ha ɗ a garin da geron da aka rage. Daga nan za a sanya cikin turmi . A wannan  karon za a kir ɓ a ne ba dakawa ba. Ma’ana , za a sanya ruwa ne adadin da zai ba da damar garin ya k ir ɓ u, duk ya ha ɗ e. Daga nan sai a duddun ƙ ula a sanya cikin tukunya  kan wuta . Sauran yadda ake ƙ arasa wannan nau’in dawo, daidai yake da na dambu kamar yadda aka bayyana a sama. Akan sha dawo da nono da suga ko kuma da zuma.

Furar Maiwa

i. Maiwa         

ii. Nono

iii. Ruwa         

iv. Ma ɗ i ko Zuma (idan an ga dama)

Yadda ake furar gero  haka nan ake t a maiwa . Bambancin kawai da ke tsakanin su shi ne, a nan ana amfani ne da maiwa a maimakon gero. Ita ma wannan  nau’in f ur a ana shan ta da da nono ko da suga ko kuma da zuma.

Furar Shinkafa

i. Kayan yaji              

 ii. Nono           

iii. Ruwa

iv. Shinkafa                

v. Ma ɗ i ko Zuma (idan an ga dama)

Za a gyara shinkafa r a wanke , sannan a sanya kayan ƙ amshi ciki a kai ni ƙ a. Bayan an dawo daga ni ƙ a za a tanka ɗ e garin sannan a sanya a turmi  a rib ɗ a shi. Za a ɗ an yayyafa masa ruwa ka ɗ an daga nan sai a duddun ƙ ula. A wannan  ga ɓ a za a nasa shi cikin ruwan zafi  kan tukunya  kamar yadda ake na gero . Sai dai a nan za a bar shi ya dahu sosai. Bayan ya nuna za a sake sanyawa cikin turmi domin a kir ɓ a. Daga an kwashe , sai a cuccura, sai kuma damu. Shi ma akan sha da nono ko madara da suga ko kuma da zuma. 

Citation (Manazartar Littafin):  Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

Get a copy:
To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
+2348133529736

You can also write an email to:

Post a Comment

0 Comments