Haila A Bayan Shan-Ruwa

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    As-Salaam Alaikum. Tana ta tsammanin zuwan hailarta har kusan minti goma kafin a sha-ruwa amma ba ta gan shi ba. Sai da ta gama shan ruwa kawai sai ga shi! To, yaya matsayin azuminta?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

    Al-Bukhaariy da Muslim da As-Haabus Sunan Al-Arba’ah da sauran malaman hadisi duk sun riwaito da lafuzza makusanta da juna - wannan lafazin At-Tirmiziy ne, kuma ya hassana shi - daga A’ishah (Radiyal Laahu Anhaa) ta ce

     كُنَّا نَحِيضُ عَلَى عَهْدِ رَسُولِ اللَّهِ - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَآلِهِ وَسَلَّمَ - ثُمَّ نَطْهُرُ فَيَأْمُرُنَا بِقَضَاءِ الصِّيَامِ وَلاَ يَأْمُرُنَا بِقَضَاءِ الصَّلاَةِ.

     Mun kasance muna yin haila sannan muna samun tsarki a zamanin Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam), sai kuma ya umurce mu da rama Azumin, amma ba ya umurtan mu da rama sallar.

    Daga wannan hadisin da masu kama da shi ne malamai suka fitar da hukunce-hukunce kamar waɗannan

    1. Bai halatta mace mai haila ko mai nifasi (jinin haihuwa) ta yi azumi ko sallah ba a lokacin da jinin ke zubo mata, kamar yadda bai halatta ta yi sallah a wannan halin ba.

    2. Idan kuma ta yi azumin ko sallar a haka to ta yi laifin da za a rubuta mata zunubi a kansa, kuma azumin ko sallar ba su inganta ba, kuma ba za a karɓe su daga gare ta ba.

    3. Wajibi ne matar da haila ta zo mata a cikin yinin azumi ta dakatar da cigaba da azumi da sallah, kuma ta rama azumin a bayan Ramadan, amma ba za ta rama sallah ba.

    4. Wacce ta samu tsarki daga haila da ranar azumi, to bai zama dole a kanta ta kame baki daga cin abinci ko abin sha ba, amma dai wajibi ne ta rama wannan yinin.

    5. Idan mace ta yi tsarki kafin fitowar alfijir na-gaskiya ko da kuwa da ƙiftawar ido ne, to wajibi ne ta yi niyyar azumin wannan yinin, ko da ba ta yi wanka ba sai a bayan alfijir ɗin.

    6. Haka kuma idan haila ta zo wa mace kafin faɗuwar rana ko da da ƙiftawar ido ne, to azuminta na wannan yinin ya ɓaci, kuma dole sai ta rama shi.

    7. Idan ta ji motsi ko alamun fitowar hailar amma dai jinin bai fito ba sai a bayan faɗuwar rana, to azuminta ya yi. Babu ramuwa a kanta.

     (A duba: Tamaamul Minnah: 2/168-169)

    Allaah ya ƙara mana fahimta.

     WALLAHU A'ALAM

    Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

    Turo tambayar ka ta WhatsApp number, banda kira ko tambayar gaggawa. 08164363661

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.