𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum Don Allah malam
a taimaka min da bayani game da sababin da yasa ake yin azumi??
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikum assalam Azumi ginshiki
ne, daga cikin turakun musulunci, wadanda addinin musulunci, ba zai cika ba sai
da su, Allah da manzonsa sun yi umarni da shi, saboda wasu muhimman manufofi,
ga wasu daga ciki:
1. Samun tsoron Allah, saboda mai
azumi yana barin abinda yake so saboda Allah, hakan zai sa, ya kara samun
tsoron Allah.
2. Samun kariya daga Shaiɗan, saboda azumi yana
takure hanyoyin Shaiɗan,
wannan ya sa zunubai suke karanci a Ramadan.
3. Tuna talakawa da wahalar da
suke ciki, saboda duk lokacin da mai kuɗi
ya ɗanɗana yunwa zai tuna halin
da talakawa suke ciki.
4. Saɓawa rai wajen barin abin da take so, da kuma
hakuri akan abin da take sha'awa.
5. Kankare zunubai da kuma samun ɗaukakar daraja, saboda
azumi yana gyara zuciya, da kuma rai.
6. Samun lafiyar jiki, saboda
azumi yana kariya daga cututtuka masu yawa, kamar yadda likitoci suka tabbatar
da hakan.
7. Ta hanyar azumi mutum zai saba
da yin aikin don Allah, saboda azumi sirri ne tsakanin Allah da bawansa.
Allah ne mafi sani
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎��𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.