Hukuncin Al-Sufrah Ko Al-Kudrah

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu Alaikum warahmatullah Malam Allah ya taimaka nayi wankan daukewar haila bayan naga alamar discharge babu jini sai dai karni-karni kaɗan bayan awanni na kuma dubawa sai naga wani discharge din da yafi na farkon haske sai na kuma sake wankan to Malam yaya ibaduna sannan na taɓa ji ance shi discharge din da yake fita bayan Al'ada yana kanshin hudar dabino wanda yake ni ban san kanshin ba abunda yasa nayi wankan shine sabida azumi kar na wayi gari ba tare da na dauki azumi ba Malam sai na sake wani wankan da kuma azumin da nake yi bayan wankan Allah ya saka da Alkhairi ya taimaka na gode.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salam Warahmatullahi Wabarkatuhu.

    To, wannan nau'in ruwan da kika ga yana fito miki shi ake cema AI-SUFRAH ko AL-KUDRAH, shi ne yake ma mace kamar ruwan Siminti (Cement) ko ruwan ciwo wani lokaci ma gauraye da baki-baki. To, irin wannan ruwan yana da hukunci dayan biyu ne

    1. Idan kin gashi ne a lokacin da kike Haila ko a karshen Haila amma haɗe da Hailar to, hukuncin shi hukuncin jinin Haila ne, kamar yadda ya tabbata a Hadisin Nana Aisha (RA).

    2. Idan kin gan shi ne a cikin tsarki lokacin da baki Haila to, hukuncinsa, hukuncin tsarki ne, kamar yadda ya tabbata a Hadisin Ummu Adiyyah (RA), zaki cigaba da Sallah, Azumi da sauran aiyukan na Ibada, duk abinda aka hana mai Haila bai shafe ki ba, sai dai duk lokacin da zaki yi Sallah sai kin yi tsarki kin sake Alwala har zuwa lokacin da wannan ruwan ya daina zuwa. Allah ya bamu ikon ganewa da gyarawa.

    Amsawa:-Mal. Ibrahim Jushi, Zamfara

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.