Hukuncin Bin Masallaci Sallah Tarawi Daga Cikin Gida

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Ya aiki don Allah tambayata itace mace zata iya bin masallaci sallar tarawi a gida ba tare da taje masallaci ba. Na gode

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    A'a Saidai ta fita izuwa masallacin ko kuma tayi sallar Tarawih ɗinta ita kaɗai a cikin gidanta ba tare da bin liman ba, kai koda a cikin masallaci idan mutum ya ware can gefe yabi liman batare da ya shiga cikin sahu ba to bashi da sallah, Sabida Tirmizi da abu dawud da Imamu Ahamad sun rawaito Hadisi cewa: WANI MUTUM YAYI SALLAH A BAYAN SAHU BAYAN AN IDAR DA SALLAH SAI MNZON ALLAH (Sallallahu alaihi Wasallam) YA UMARCESHI DA YA SAKE SALLAH. To kinga idan har wanda yayi sallah a masallaci sabida be cike sahu ba Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yace masa yaje ya sake sallah Ina ga kuma wacce tabi masallaci sallah daga cikin gida???

    WALLAHU A'ALAM

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.