𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Menene hukuncin shayar da Ɗan da aka samesa ba ta hanyar shari'a ba
- wato Ɗan
Zina ga ijtima'in (haduwar musulmai)? Kuma ga wa ake danganta sa kuma waye yake
zamantowa waliyyinsa? Za'a iya naɗa
shi alkalanci idan ya cancanci hakan? Shin zai aura daga musulma (wacce take
'ya da aka same ta ta hanyar Shari'a)? A ina za'a binne shi idan ya mutu? Shin
(bayan mutuwarsa) za'a yi masa Sallah? A wasu lokuta akwai masu kashe 'ya 'ya
lokacin haihuwa, to shin Menene hukuncin masu aikata hakan?
𝐀��𝐒𝐀❗️
Yaron da aka Haifa ta hanyar zina idan mahaifiyarsa ta
kasance musulma ce hukuncinsa kamar hukuncin sauran yaran musulmai ne, musulmai
za su tarbiyyantar dashi za su kyautata gare shi, Domin akansa bashi da wani
zunubi na mahaifiyarsa ko kuma zunubin Wanda yayi zina da mahaifiyarsa: Wata
rai bata ɗaukar
laifin wata rai
قُلْ
أَغَيْرَ اللَّهِ أَبْغِي رَبًّا وَهُوَ رَبُّ كُلِّ شَيْءٍ وَلَا تَكْسِبُ كُلُّ نَفْسٍ
إِلَّا عَلَيْهَا وَلَا تَزِرُ وَازِرَةٌ وِزْرَ أُخْرَىٰ ثُمَّ إِلَىٰ رَبِّكُم مَّرْجِعُكُمْ
فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمْ فِيهِ تَخْتَلِفُونَ
Ka ce: ''Shin wanin Allah nake nẽma ya zama Ubangiji,
alhãli kuwa Shĩ ne Ubangijin dukan kõme? Kuma wani rai bã ya yin tsirfa fãce
dõmin kansa, kuma mai ɗaukar
nauyi, bã ya ɗaukar
nauyin wani, sa'an nan kuma kõmawarku zuwa ga Ubangijinku take; Sa'an nan Yã bã
ku lãbãri ga abin da kuka kasance, a cikinsa, kunã sãɓã wa jũnã?'' (Suratul An'am aya ta 164).
Laifin zinar da sukayi yana kansu ba shi ba. Domin shi amana
ne tsakanin musulmai, yana kansu su tarbiyyantar dashi tarbiyyar musulunci,
kuma su kyautata masa har ya kai lokacin samartakarsa ya girma, Idan ya balaga
hukuncinsa kamar hukuncin sauran musulmai ne, yana ga daular musulunci ta tsayu
da wannan al'amari kuma ta taimaka akan wannan al'amari har sai an baiwa waɗannan yara kariya har su
tsaru daga cutarwa da kisa.
Amma kasancewarsa kashe shi bayan haihuwa ko kuma yunkurin
kashe sa yayin haihuwa, aikata hakan yana daga cikin munanan ayyuka kuma baya
halatta, Duk Wanda ya aikata hakan kuwa to ya dorawa kansa laifuka biyu wato
laifin zina ga kuma laifin kisa ba tare da hakki ba. Muna neman tsari daga
wajen Allah.
Abinda yake wajibi shine kada a kashesa sai dai ma abasu
kariya ta hanyar damka su a gidan raino ko kuma asamu mace musulma da za ta iya
daukar nauyin shayar dashi, da kyautata masa da tarbiyyantar dashi, zayyi
karatu tare da sauran yaran musulmai kuma a garin musulmai. Za'a yi kokarin
fuskantar dashi izuwa ga aikata Alkhairi, a duk lokacin da ya tsayu da kafarsa
yakai lokacin balaga, kuma ya dabi'antu da kyawawan dabi'un mutanen kirki, to
ya halatta ya zamo cikin masu kira ga Addinin ALLAH.
To ya inganta ya kasance alkali, ya kasance tsarki, kuma ya
kasance miji ga ragowar wanda zai iya ɗaukar
nauyin su daga cikin musulmai, bayi da wani zunubi, zunubin sa yana akan wanin
sa bashi ba, abunda ke akansa kawai tsayuwa idan ya kai ya tsayu akan umurnin
ALLAH, kuma yaji tsoron abunda ALLAH ya haramta, duk lokacin da ya gyaru (Ya
daidaitu akansa) ya tsayu akan sa, hukuncin sa ya zamo irin na sauran musulmai,
yana gare shi abunda ke gare shi, yana akansu abunda ke akansu na hakkoki.
Idan ya mutu yana karami za'a abinne shi a makabartar
musulmai, matukar dai mahaifiyar sa musulma ce, za'a binne shi a makabartar
musulmai, za'a yi masa wanka ayi masa sallah kamar sauran yaran musulmai, ba ya
halatta ayi sakaci da shi, ko tozartar da shi, za'a ambace sa da sunan da ya
dace kamar, Abdullahi, abdurrahman, ko Abdul Malik, da kuma sauran sunaye,
Muhammadu, Zaidu, babu laifi a sanya masa Muhammadu, Zaidu ai sunaye ne daga
sunayen da suka dace, ko ace masa Ibnu Abdullahi, za'a jinginar zuwa ga
Abdullahi ko Abdul Malik, dukkan mutane bayin ALLAH ne !
Tambaya zai auri waye?
zai aure daga musulmai shi musulmi idan ya shiryu (ko da ɗan zinah ne) mahaifiyar
sa ba ta cutar da shi ko wanda yayi zina da ita !
Tambaya, daidai ne shin in wannan yaron ya mutu kuma gashi
an jahilci ba'a san waye ba?
za'a rufe shi tare da musulmai, godiya ta tabbata ga ALLAH,
ALLAH shi zai jiɓinci
sakamakon hisabin sa
Tambaya zai iya jiɓintar
alkalanci?
Amsa eh zai iya alkalanci da wasun sa.
✍Sheikh Bin Baz (ALLAH yayi masa
Rahma)
📒المصدر ⬇
📙الشيخ ابن باز رحمه الله.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.