Hukuncin Dawowar Jinin Haila Bayan Ta Dauke

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Wasu matan jini ba ya ɗauke musu sai na kwana biyu ko uku kawai sai ya sake dawowa, meye hukuncin azumin mace da sallanta a irin wannan yanayin??

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Abunda yake sananne ne awurin mafiya yawan malamai shine idan mace tana al'ada sai tayi tsarki to zatayi wanka ta cigaba da Sallah da azumi, amma abinda zata gani bayan kwana biyu ko uku ba haila bane, domin mafi ƙarancin tsarki awurin waɗannan malaman kwana goma sha uku ne.

     Wasu malaman kuma sukace: aduk lokacin da mace ta ga jini to haila ne, idan taga tsarki to tsarkine, koda kuwa tsakanin hailan farko da ta biyun bai kai kwana goma sha ukun ba"

    Dawowar Jinin Al'ada

    TAMBAYA (151)

    Assalamu alaikum Malam Ina yini ya aiki. Allah ya taimaka Malam dan Allah wata yar tambaya gare ni.

    Nayi alada ne sati 4 da suka wuce har na fara sallah nah Kawai Sai satin da ya gabata jini ya dawo min Amma ba jini din nan dai da muka sani bani wannan wani brown ne haka yau sati daya kenan yaki tafiya ni kuma nayi wanka nah Ina sallah toh bansan ya matsayin sallar nawa take bah

    AMSA

    Waalaikumus salam warahmatullahi wabarakatuhu

    Anan Zaki duba nau'in jinin ne. Idan nau'insa yayi kama da na haila to zaki dakatar da Ibadah ne saboda wannan alamu ne na cigaban al'ada amman idan nau'insa ba na haila bane to zaki dauke shi ne a matsayin jinin Istihadha sannan Kuma zaki ci gaba da ibadarki saidai zaki dinga sabunta alwala a tsakanin kowacce sallah

    (Sahihul Bukhari [Arabic-English] Vol. 1 page 149 - Hadith #228)

    Wallahu taala a'alam

    Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk

    Amsawa

    Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    WALLAHU A'ALAM

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa


    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.