Hukuncin Fitar Maniyyi Ga Mai Azumi

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Mene ne hukuncin Azumin wanda yayi mafarki da rana har Maniyyi yafito masa??

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Dangane da hukuncin Fitar Maniyyi ga wanda yake azumi mafi yawan Malamai cikinsu harda Mazhabobin nan guda huɗu wato

    1. Malikiyya

    2. Shafi'iyya

    3. Hanafiyya

    4. Hanabila

    Dukkansu suntafine akan cewa fitar da Maniyyi da gangan ta hanyar da ba jima'i ba yana lalata azumi, danhaka idan Mai-Azumi yayi Istimna'i, ko ya rungumi Matarsa, ko yayi wasa da'ita, hartakai ga yafitar da Maniyyi to azuminsa ya lalace, danhaka Malamai sukace dukkan Mutumin da yasan cewa Sha'awarsa tana da ƙarfin da indai zaiyi wasa da Matarsa Maniyyi zaifito masa to haramunne agareshi yayi hakan da'ita, idan kuwa yayi har Maniyyi yafita to wajibine sai yarama wannan azumin, amma idan yakasance Maniyyin yafitane ta hanyar mafarki kokuma tunani ko kallon Mace batare da yayi wasa da'itaba, mafi yawan Malamai sukace azuminsa bai lalace ba saidai wajibine yayi wankan janaba, amma Mazhabin MALIKIYYA sukace koda mafarki yayi dolene sai yarama wannan azumin.

    Danhaka Malamai sunyi Saɓani dangane da yanayin ramuwar azumin da Mutum zaiyi, Mafi yawan Malamai suntafine akancewa zai rama azumi guda ɗayane kawai batare da yayi wata Kaffara ba, domin Nassin yin Kaffara yazone akan wanda yayi Jima'i da Matarsa da rana, Saidai Mazhabin MALIKIYYA suntafine akancewa idan Mutum yayi Mafarki har yafitar da Maniyyi to azuminsa ya lalace kuma dolene sai ya rama batare da kaffaraba, amma idan wasa yayi da Mace ya rungumeta ko ya Shafata ko yayi Istimna'i har yafitar da Maniyyi, to wajibine sai yayi ramuwa tare da Kaffara, domin sunyi Ƙiyasine akan hukuncin wanda yayi Jima'i da Matarsa da gangan da rana.

    Amma. Mazhabin ZAHIRIYYA suntafine akan cewa wanda yafitar da Maniyyi da gangan ta dukkan wata hanyar da ba Jima'i yayi da Matarsa ba, sukace azuminsa yana nan bai lalace ba, domin babu wata Hujja afili Ƙarara daga cikin Al-Ƙur'ani ko Hadisi datace azuminsa ya lalace, to amma Saidai maganar Malaman da sukace azuminsa ya lalace tafi Ƙarfi.

    Amma maganar da tafi inganci wacce mafi yawan Malamai sukafi rinjayar da'ita shine, fitar Maniyyi ta hanyar mafarki baya karya azumi, domin Ɗan-Adam bashi da wani iko na ya'iya hana kansa yin mafarki alokacin da yake barci ba, hakanan magana mafi inganci fitar Maniyyi ta hanyar tunani ko kallo shima baya karya azumi, amma duk dahaka ba'ace Mutum yarika sanya irin wannan tunanin acikin Zuciyarsa ba, amma fitar Maniyyi dagangan tahanyar wasa tsakanin Ma'aurata, ko tahanyar Istimna'i, wannan kam yana lalata azumi, kuma za'ayi ramuwane kaɗai batare da Kaffaraba, amma idan Mutum yayi jima'i da Matarsa da gangan da rana, tofa koda baikawo Maniyyiba ramuwa da Kaffara sunhau kansa.

    шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ

    Doмυп пεмαп ƙαяıп вαчαпı sαı αdυвα шαɗαппαп ʟıтαттαғαı καмαя нακα:        

    "المغني لإبن قدامة"

    الشرح الممتع" (6/234)

    "المجموع للنووي" (6/349)

                 AMSAWA

               Mυѕтαρнα Uѕмαи

                  08032531505

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.