Hukuncin Fitar Maziyyi Da Azumi

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Menene hukuncin wanda ya ga wani ɓangare na jikin matarsa ko ya sumbaceta (kissing) ko kuma ya kalli wassu finafinai na tsiraici, sai maziyyi ya fito masa alhali yana azumi? Allah ya sama iliminku albarka.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Fitan maziyyi baya lalata azumi a maganar da ta fi inganci daga cikin maganganun maluma guda biyu, lamarin haka ya ke sawa'un ya fita ne saboda sunbantar mata, ko kuma ta hanyar kallon finafinai, ko kuma makamantan haka, daga cikin abubuwan da su ke tada sha'awa, Sai dai kuma baya halatta ga musulmi ya kalli finanan tsiraici da batsa, ko kuma sauraron abin da Allah ya haramta na sauraron waqoqi, ko kayan kade-kade.

    Amma fitar maniyyi da sha'awa yana lalata azumi; sawa'un hakan ya auku ne sakamako runguma ko sumbanta ko maimaita kallo, ko makamancin haka daga cikin sabbuban da su ke tada sha'awa; Kamar wasan fitar da maniyyi (istimna'i), da makamancinsa.

    Mafarki da tunani, su kuma azumi ba ya ɓaci da su, koda kuwa maniyyi ya fita da sababinsu.

    DUBA FATAWA ISLAMIYYAH, MAJMU'U FATAWA WA MAQAALAAT MUTANAWWI'AH, (15/ 267).

    Allah ta'ala yasa mudace

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.