Hukuncin Huda Hanci Da Saka Zobe Ko Sarka A Kafa

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu Alaikum Warahmatallahi Malam don Allah yaya kwalliya da hudan hanci, gyaran gira, zoben kafa da sarkan kafa suke amusulunci? Nagode. Allah saka da alkhairi

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

    Malamai sunce hujin hanci da hujin kunne duk ya halatta ga Matayen musulmai. Domin kuwa matan Sahabban Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam sun kasance sunayi kuma Annabi Sallallahu alaihi Wasallam bai hanasu ba.

    Acikin FATHUL-BAREE juzu'i na 10 shafi na 407-408, Al-Imam Ibnu Hajrin ya kawo wani hadisi wanda Tabarany ya ruwaito daga Sayyiduna Abdullahi bn Abbas (ra) Ya lissafta abubuwa bakwai sunnah ne ga duk wata 'ya-mace. Daga ciki akwai hudar hanci da hudar kunne.

    Amma malamai sunce wajibi ne kowacce mace ta tabbatar da cewa ruwa yana ratsawa cikin wannan hujin yayin da tazo yin wankan haila ko janabah.

    Dangane da sarkar Qafa da zoɓen Qafa kuwa, rashin sanyasu shine mafi alkhairi. Domin kuwa idan tana tafiya za'a iyajin Qararsu. Sannan kuma indai bata sanya safar Qafa ba, wasu mazajen da ba muharramanta ba zasu iya ganin wannan adon. Yin hakan kuwa haramun ne a Musulunci.

    Allah ya umurci matan muminai cewar su ɓoye adonsu kuma kada surika buga kafafunsu yayin da suke tafiya

    وَقُلْ لِلْمُؤْمِنَاتِ يَغْضُضْنَ مِنْ أَبْصَارِهِنَّ وَيَحْفَظْنَ فُرُوجَهُنَّ وَلَا يُبْدِينَ زِينَتَهُنَّ إِلَّا مَا ظَهَرَ مِنْهَا ۖ وَلْيَضْرِبْنَ بِخُمُرِهِنَّ عَلَىٰ جُيُوبِهِنَّ ۖ وَلَا يُبْدِينَ زِينَتَهُنَّ إِلَّا لِبُعُولَتِهِنَّ أَوْ آبَائِهِنَّ أَوْ آبَاءِ بُعُولَتِهِنَّ أَوْ أَبْنَائِهِنَّ أَوْ أَبْنَاءِ بُعُولَتِهِنَّ أَوْ إِخْوَانِهِنَّ أَوْ بَنِي إِخْوَانِهِنَّ أَوْ بَنِي أَخَوَاتِهِنَّ أَوْ نِسَائِهِنَّ أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُهُنَّ أَوِ التَّابِعِينَ غَيْرِ أُولِي الْإِرْبَةِ مِنَ الرِّجَالِ أَوِ الطِّفْلِ الَّذِينَ لَمْ يَظْهَرُوا عَلَىٰ عَوْرَاتِ النِّسَاءِ ۖ وَلَا يَضْرِبْنَ بِأَرْجُلِهِنَّ لِيُعْلَمَ مَا يُخْفِينَ مِنْ زِينَتِهِنَّ ۚ وَتُوبُوا إِلَى اللَّهِ جَمِيعًا أَيُّهَ الْمُؤْمِنُونَ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ

    Kuma ka ce wa mũminai mãta su runtse daga gannansu, kuma su tsare farjõjinsu kuma kada su bayyana ƙawarsu fãce abin da ya bayyana daga gare ta, kuma su dõka da mayãfansu a kan wuyan rigunansu, kuma kada su nũna ƙawarsu fãce ga mazansu ko ubanninsu ko ubannin mazansu, ko ɗiyansu, ko ɗiyan mazansu, ko ´yan'uwansu, ko ɗiyan ´yan'uwansu mãtã, kõ mãtan ƙungiyarsu, ko abin da hannãyensu na dãma suka mallaka, ko mabiya wasun mãsu bukãtar mãta daga maza, kõ jãrirai waɗanda. bã su tsinkãya a kan al'aurar mãtã. Kuma kada su yi dũka da ƙafãfunsu dõmin a san abin da suke ɓõyewa daga ƙawarsu. Kuma ku tũba zuwa ga Allah gabã ɗaya, yã ku mũminai! Tsammãninku, ku sãmi babban rabo. (Suratun-Nur aya ta 31)

    Shi kuwa gyaran gira ta hanyar ragewa gashin ko askewa, Wannan haram ne. Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya tsine ma duk matar da take tsigewa gashin girarta da kuma wacce take tsige mata ɗin. (aduba Sahihul Bukhary hadisi mai lamba 4886 da sahihu muslim hadisimai lamba 2125)

    DON KARIN BAYANI

    Aduba FATAWA AL-LAJNATUD DA'IMAH (juzu'i na 5 shafi na 195-197).

    Da kuma FATAAWA ULAMA'I BALADIL HARAM shafi na 577.

    ALFATAWAL HINDIYYA juzu'i na 5 shafi na 357.

    RADDUL-MUHTAR juzu'i na 6 shafi na 420.

    MARAQEEL FALAHI shafi na 102.

    BAHRUR-RAA'IQ juzu'i na 1 shafi na 47

    WALLAHU A'ALAM.

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/IqsWWSpUkwk6b8hWJ6vXOO

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.