Hukuncin Wanda Maziyyi Ya Fito Masa Yana Azumi

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Mene ne hukuncin wanda Maziyyi yafito masa yana Azumi, Shin azuminsa ya lalace ko bai lalace ba??

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Alal-Haƙiƙa Malamai Fuƙaha'u sunyi Saɓani dangane da hukuncin cewa Shin Maziyyi yana iya ɓata azumi ko a'a, Sannan dolene sai Mutum yarama wannan azumin kenan kokuma a'a?

    Mazhbin HANABILA da MALIKIYYA suntafi akan cewa Maziyyi yana ɓata azumi idan yakasance Mutum shi ne ya yi Sababin fitarsa da gangan, kamar ya Shash-Shafa jikin Matarsa, ko ya rungumeta, ko ya yi wasa da'ita, ko ya yi mata Kiss (sumbata), kokuma wani abu makamancin haka wanda zai sashi yaji daɗi har Maziyyin yafita sukace azuminsa ya lalace, amma HANAFIYYA sukace idan yakasance bai taɓa jikintaba kawai kallonta ya yi tayi har Maziyyi yafita to azuminsa yananan bai ɓaciba, yayinda sukuma MALIKIYYA suke ganin cewa ai koda ta hanyar kallone yafita to azumi ya lalace, daga cikin Dalilansu sunkafa Hujja da Hadisin A'isha Matar Mαиzoи Aʟʟαн ( Sallallahu alaihi Wasallam ) wanda take cewa

    " ﻛﺎﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ‏( ﷺ ‏) ﻳﻘﺒﻞ ﻭﻫﻮ ﺻﺎﺋﻢ، ﻭﻳﺒﺎﺷﺮ ﻭﻫﻮ ﺻﺎﺋﻢ، ﻭﻟﻜﻨﻪ ﻛﺎﻥ ﺃﻣﻠﻜﻜﻢ ﻹﺭﺑﻪ "

    ‏( ﻣﺘﻔﻖ ﻋﻠﻴﻪ )

    MA'ANA

    Mαиzoи Aʟʟαнn (Sallallahu alaihi Wasallam ) Ya kasance yana sumbatar (Matansa) yana azumi, haka kuma yana rungumar (Matansa) yana azumi, Saidai yafiku mallakar bukatarsa

    Sukace Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) bayayin abinda zai tayar masa da Sha'awa, danhaka kenan duk wanda ya yi abinda yasa har Maziyyinsa yafita to wajibine sai yarama

    Amma Mazhabin HANAFIYYA dakuma SHAFI'IYYA suntafine akan cewa Kwata-Kwata fitar Maziyyi ta kowace irin hanyace baya karya azumi, Misali: yafitane ta hanyar wasa da Matarsa, ko runguma, ko Sumbata (Kiss), ko kallon wani Film ko Hoto na batsa, ko Mutum ya yi wasa da gabansa amma Maniyyi bai fitoba saidai Maziyyi, kokuma wani abu makamancin haka, Hujjarsu anan ita ce, sukace babu wani Dalili daga Al-Ƙur'ani ko Hadisi da yake nuna cewa Maziyyi yana ɓata azumi,

    Saidai magana mafi inganci dangane da wannan Mas'ala kamar yadda dayawa daga cikin Malamai sukafi rinjayarwa ita ce, fitar Maziyyi ta kowacce irin hanya baya lalata azumi, domin kuwa idan akace Maziyyi yana lalata azumi to akwai Mutanen da saboda ƙarfin Sha'awarsu hakan zai kaisu ga sai sun rama kusan dukkan azumi 30 ɗin dasukayi, wanda hakan kuma zai zama wahalane agaresu, ita kuma Shari'a tazone danufin ta sauƙaƙa, domin akwai wanda indai zai kalli Matarsa to kuwa sai Maziyyi yafito masa, Saidai Malamai sukace Makaruhine Mutum ya yi dukkan wani abinda yasan cewa zai iya tayar masa da Sha'awa har Maziyyinsa yafita alhali yana Azumi

    шαʟʟαнυ-α'αʟαm

    AMSAWA

               Mυѕтαρнα Uѕмαn

                  08032531505

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.