Hukuncin Wanda Ya Kalli Mace Ya Fitar Da Maniyyi Alhali Yana Azumi

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Mene ne Hukuncin Wanda Ya Kalli Matarsa Ba Tare Da Ya Taɓa Ta Ba, Sai Ya Fitar Da Maniyyi Alhali Yana Azumi?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Hakika Wanda ya samu Kansa a irin wannan halin zai cigaba da azuminsa, kuma babu kome akansa. dalili akan haka na cikin hadisin jabir  ibn zaid (ra) yace: Wanda ya kalli mace ya fitar da maniyyi, ya cigaba da azuminsa, babu komai akansa.

    Imam al-shafi'i (babban almajirin imam malik), da imam al-thauri da imam al-auza'i duk sun tafi akan cewa babu wani dalili da yazo akan cewar fitar da maniyyi kaɗai yana karya azumi, ba tareda jima'i ba amma idan jima'i ne, koko an fitar da maniyyi ko ba'a fitar ba, yana karya azumi, kuma sai anyi kaffara. haka kuma Wanda ya sumbaci matarsa (kiss) har ya fitar da maziyyi shima azuminsa yana nan. Wannan shine zance mafi rinjaye. Sai dai wasu daga cikin malaman mazhabar malikiyyah sun ce, fitar da maniyyi ta hanyar kallo ko runguma yana karya azumi, kuma akwai ramuwa da kaffara a kai. Amma idan maziyyi ne kawai akwai ramuwa ba tareda kaffara ba. sun kafa hujjar cewa abinda ake bukata a jima'i shine fitar maniyyi. Saboda haka fitar maniyyi ta wannan hanya daidai yake da jima'i.

    Amma sauran manyan malamai sunyi masu raddi cewa hukuncin da nassi yazo dashi ya ambaci jima'i ne kawai, ba fitar da maniyyi ba. Sannan suka kara da cewa idan da mutum zai yi jima'i ba tareda ya fitar da maniyyi ba, ai zai rama azumi ne kuma yayi kaffara. haka kuma da ace fitar da maniyyi ne kawai ake lura da shi, sai ace me bacci ma idan yayi mafarki ya fitar da maniyyi, sai yayi kaffara. (Sharh sahihul bukhari ,na ibn battal al-mālilī, 4 /52-56)

    Daga littafin fatawoyin azumin Ramadan na abdulwahab abdullah

    WALLAHU A'ALAM

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.