𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum, Menene hukuncin
wanda yayi istimna'i da rana ana azumi?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salam, Istimná'i shi
ne mutum ya yi wasa da al'aurarsa har ya fitar da maniyyi ba ta hanyar jimá'i
ba. Yin hakan laifi ne babba, amma laifin yinsa a watan Ramadana yana qara
girmama fiye da a sauran watanni.
An tambayi Allama Ibn Utsaimeen
Rahimahullahu a game da wanda ya yi Istimná'i, shin kaffara ta wajaba a kansa?
Sai Allama ya ba da amsa da cewa: "Idan mai azumi ya yi wasa da al'aurarsa
(istimná'i) har ya fitar da maniyyi, to ya wajaba a kansa ya rama azumin wannan
yini da ya yi istimná'i a ciki, amma babu kaffara a kansa, saboda kaffara ba ta
wajaba sai idan jimá'i ne aka yi".
Duba Majmú'u Fataáwá na Ibn
Uthaimeen 19/233.
Kuma wanda ya sami kansa a wannan
mugun aikin, bai halasta a gare shi ya ci abinci ko abinsha a wannan yinin
saboda an ce azuminsa ya karye ba, wajibi ne a kansa ya kiyaye alfarmar watan
ta hanyar kamewa daga ci ko sha duk da karyewan azumin nasa. Sannan ya wajaba a
gare shi ya yi nadama tare da kyakkyawar tuba zuwa ga Allah, saboda wannan
babban zunubai da ya aikata na Istimná'i da kuma karya azumi, kuma ya yawaita
kyawawan ayyuka, saboda kyawawan ayyuka suna tafiyar da munana.
Allah ne mafi sani.
Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.✍
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.