Hukuncin Wani Ruwa Brown Dake Fitowa Ta Gaban Mace Kafin Tafara Al'ada

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Menene hukuncin wani ruwa brown dake fitowa ta gaban mace kafin tafara al'ada?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    To shidai wannan nau'i na ruwa brown dayake fitowa mata ya kasune gida uku

    -kodai yafito kafin haila.

    -kokuma yafito bayan mace tagama haila.

    -kokuma yafito alokacin da mace take haila.

    Idan yakasance yafitone kafin haila abinda malamai sukace shine, idan yakasance wannan ruwa kamar wata muqaddimace tazuwan jinin haila to hukuncinsu ɗaya da haila, tayadda ruwan yanazuwa kuma kafin ya ɗauke sai jini yabiyo bayansa, kokuma kafin yafito mace taji wata alama datasaba jinta idan zatayi al'ada, dagabaya kuma saitaga wannan ruwa brown yafito to zata dakatar dayin sallah.

    Amma idan mace taga wannan ruwa batare dataji wata alama nazuwan hailaba, kokuma yakasance ansamu tazara kamar kwanaki biyu ko samada hakan tsakanin zuwan ruwan saikuma ya ɗauke to hukuncin tsarkine akanta.

    Hakanan idan mace taga wannan ruwa yazomata bayan tagama al'ada tayi tsarki to shima bakomai akanta zataci gaba dayin sallah dakuma azumi, saidai akwai malaman dasuke ganin cewa zuwan wannan ruwa kafin jinin haila kokuma yazo bayan angama jini to duk hukuncinsu ɗaya awani QAULIN na Malamai.

    Ammadai magana mafi inganci itace zuwan wannan ruwan bayan gama jinin al'ada indai ansamu 'yartazara tsakanin ɗaukewar jinin dakuma zuwan ruwan to wannan baya hana mace tacigaba dayin ibadarta.

    Amma idan yakasance mace taga wannan ruwane atsakanin al'adarta kamar ace tayi kwana biyu jini yana zuwa mata akwana na uku kuma saitaga wannan ruwa yafito sannan akwana na huɗu ko na biyar saitasake ganin jini, to wannan ruwa hukuncinsa ɗaya da jinin al'ada, mace zata jirane harsai ya ɗauke sannan tayi wanka.

    Mai neman karin bayani sai yaduba Waɗannan litattafai kamar haka

    ﺍﻟﺪﻣﺎﺀ ﺍﻟﻄﺒﻴﻌﻴﺔ ﻟﻠﻨﺴﺎﺀ ‏( ﺹ 19 ‏)

    ﺛﻤﺮﺍﺕ ﺍﻟﺘﺪﻭﻳﻦ ﺍﺑﻦ ﻋﺜﻴﻤﻴﻦ ‏( ﺹ 25 ‏)

    ﺍﻟﻤﻮﺳﻮﻋﺔ ﺍﻟﻔﻘﻬﻴﺔ ‏( 18/296 ‏)

    ﺍﻟﻤﻐﻨﻲ ‏( 1/202 ‏)

    ﺍﻟﻤﺠﻤﻮﻉ ‏( 2/422 ‏)

    WALLAHU A'ALAM

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.