𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum malam. Ina da
ulcer kuma bana iya awa huɗu
banci abinci ba kuma ina shayarwa zan iya ciyarwa ko inna warke zan rama kuma
ana bina huɗu nabara
ban rama ba ina laulayi anabina uku danace zan in ALLAH yabiyamin wata
bukatata.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salam Warahmatallahi
Wabarkatahu.
Toh anan abunda yake akanki shine
idan ulcer dince tasa bazaki iya azumi ba toh bazaki ciyar ba jira zakiyi idan
kin warke seki rama. Inkuma likitanki yace miki wannan irin ciwon naki bincike
yanuna cewa ba'a cika warkewaba da ciwon ake mutuwa toh anan shine kawai seki
ciyar kuma koda daga baya Allah yasa kin warke to bazaki ramaba. Amma idan ba
don ulcer ɗin bane
kika kasa azumin A'a ciki ne dake kokuma kina shayarwa shine yasa bazakiyi
azumiba toh wannan kawai ciyarwane akanki bazaki ramaba.
Amma akwai saɓani domin wasu malamai
suna ganin akasin abunda na faɗa,
sedai kuma ni wannan shine na gamsu dashi kuma shine fahimtar me littafin
Alwajiz fi fiqhis sunnah. Amma wadancan guda ukun wadanda ake binki na bakance
toh sukuma wadannan bazaki ciyarba jira zakiyi inkin warke seki yisu. Inkuma
har kika mutu bakiyiba toh magadanki zasuyi miki azumin ba ciyarwaba azumi
zasuyi.
WALLAHU TA'AALA A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
1 Comments
Masha Allah
ReplyDeleteENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.