Mafarkin Kishin Ruwa

    TAMBAYA (84)

    Assalamualaikum Barka da rana malam ya aiki ya kokari allah ya kara basira Amin🙏 malam nine nayi mafarkin matsanancin kishirwa koma kona sha ruwan bana koshi BAYA kashemin kishin inason karin bayani

    AMSA

    Waalaikumussalam, warahmatullahi, wabarakatuhum

    Alhamdulillah

    Babban malamin nan kuma Tabi'i, Imam Muhammad Ibn Seerin, dalibin Imam Maleek (Allah ya jikansu baki daya), yace, a cikin shahararren littafinsa na "Qamus din Fassarar Mafarki"

    Mafarkin jin kishin ruwa na nufin tsayawar kasuwanci, tafiyar wahainiya wajen gudanar da cinikayya, kwantan amfanin gona

    Mafarkin kishin ruwa na nufin; talauci, faduwar farashi, fari, kewar masoyi, kwadaituwar kasancewa da masoyi da kuma kewar rabuwa dashi. Mafarkin kishin ruwa ma iya zama rashin hadin kai a addini

    Idan mutum yana jin kishin ruwa a mafarki kuma yana neman ruwan kuma bai samu ruwan ba hakan na nufin zai tsallake wani bala'i. Idan kuma ya ganshi a kusa da rijiya ko kuma wani idaniyar ruwa kuma ya kasa sha ko kuma ya kasa debowa hakan na nufin zai gaza cimma buqatar da yasa a gabansa. Sannan mafarkin kishin ruwa na nufin halaka ko kuma fatan mutum yayi aure don ya kiyaye al'aurarsa daga fadawa tarkon zinace - zinace

    SHARHI

    La'akari da kince ko da kin sha baya kashe miki kishin ruwan to anan sai ki yi amfani da formular da Annabi Sallallahu alaihi wasallam ya bayar cewar: mafarki mai kyau daga Allah Subhanahu wata'ala ne, mummunan mafarki kuma daga shaidan ne

    A farke ma ace ga ruwa kana sha amman ka gaza koshi ? A mafarke kasan wannan ba abin alkhairi bane ba ko dai daga shaidan ne ko kuma daga gareki ne. Ma'ana: bayan wadancan biyun akwai kuma mafarki daga mutum. Misali: Mai yiwuwa lokacin da zaki kwanta bacci kin ci abinci amman baki sha ruwa ba, zaki iya mafarkin gakinan kina shan ruwa dayawa ko kuma kina kusa da rijiya, gulbi, rafi ko teku. Fassarar anan ta fito

    A shawarce, duk lokacin da kika zo zaki kwanta ki tabbatar da kinyi alwala sannan kada ki manta ki karanta Ayatul Kursiyyu, Amanar Rasulu, Qulhuwallahu 3, Nasi 3 da Falaqi 3, Suratul Kafirun, Subhanallah 33, Alhamdulillah 33 da kuma Allahu Akbar 34 sai ki ce "Bismikallahumma amutu wa'ahya" daganan sai ki kwanta da barin dama

    In Sha Allahu. Ba abin cutarwar da zai iya samunki a wannan daren, a farke ko a mafarki

    Wallahu ta'ala a'alam

    Amsawa;

    Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

     Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.