𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum malam. Menene
Mafificin Aikin Da Mai Azumi Zai Dinga Yi A Watan Ramadan???
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salam Warahmatullahi
Wabarkatuhu.
Aikin da yafi falala ga mai azumi
shine
1. KARATUN AL'QURANI. Ma'ana ya
lazimce shi dare da rana, kuma yadinga izna da abin da yake karantawa. Amma
idan bazai iya karatun Al-Qurani ba, to sai ya rinka lazimtar inda ake karatun
Al-qur'anin ko fassarashi domin hadisi ya tabbata daga nana Fadima 'yar Manzon
Allah Sallallahu alaihi Wasallam da Abu Huraira yardar Allah ta tabbata a
garesu sunce: "Mala'ika Jibrilu ya kasance yana bijirowa da Annabi
Sallallahu alaihi Wasallam Al'Kur'ani sau ɗaya
a kowace shekara, sai ya bijiro masa dashi sau biyu a shekarar da zaiyi wafati.
Bukhari da Muslim ne suka ruwaito (1). (1) Bukhari K=66, Book=7, Hadith=4998 da
Muslim
K=44, B= 15, Hadith=2450.
Wannan yana nuna cewa karatun
Al-qur'ani shine mafificin ibada a cikin watan Ramadan. Allah maɗaukakin Sarki yace:
"Lallai mun saukar dashi a daren Lailatul Kadari.
2. KYAUTA: Ya kamata mai Azumi ya
yawaita kyauta wajen ciyar da jama'a, da sadaka, da taimakon gajiyayyu da
makusanta. Kamar yadda ya tabbata a hadisin ibn Abbas cewa:"Annabi
Sallallahu alaihi Wasallam yafi kowa kyauta, kuma mafi alkhairinsa yana yinsa
ne a Ramadan yayin da yake saduwa da Jibrilu. Kuma ibn Abbas (R.A) yace:
Alkhairin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam yafi sakakkiyar iska".Bukhari
ne ya ruwaito shi (2). (1) Suratul Kadari Aya1 (2) Bukhari K = 1, B = 5, da
Muslim K = 43, B = 12, H = 2308.
3. NAFIL-FILI: Anaso mai Azumi ya
yawaita Nafil Fili musamman kiyamul laili Saboda hadisin Abu Hurairah yardar
Allah ta kara
tabbata a gareshi yace: Manzon
Allah Sallallahu alaihi Wasallam yace: "Duk wanda yatsaya kiyamulaili yana
mai imani, da neman lada an gafarta masa zunubansa da suka gabata".
Bukhari ne ya ruwaito shi (1). Haka kuma Manzon Allah Sallallahu alaihi
Wasallam yace: Wanda yayi sallah dare tare da liman har yagama za'a rubuta masa
ladan kiyamullaili. Kuma anfison duk wanda zaiyi kiyamullaili ya tsawaita
tsayuwar saboda hadisin Khuzaifa (R.A) Targib Wattarhib wanda Albani yayiwa
tahkiki lambar (1078). "Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya kasance
yana tsawaita karatu a sallar dare a watan Ramadan fiye da sauran sallolin
dare, yace, Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam yakan karanta Suratul
Bakarah da Nisa'I da Ali'Imran a raka'a ɗaya,
kuma baya wuce ayar da akayi tsoratarwa a cikinta sai ya tsaya ya roki Ubangiji
tsari. Kuma bai gama raka'a biyu ba sai ga Bilalu (R.A) yazo yana neman izni
ayi sallar Asuba. Ahmad ya ruwaito wannan hadisin kuma ya ingantashi.
4. YAWAN ZIKIRI DA SALATIN ANNABI
(Sallallahu alaihi Wasallam): Abune mai matukar falala mutum ya yawaita Zikiri
da Salati ga Shugaban Halitta
irin wanda ya tabbata daga bakin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam.
Allah Madaukakin Sarki ya ce
أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا
اذْكُرُوا اللَّهَ ذِكْراً كَثِيراً
Ya ku wadanda suka yi imani ku
ambaci Allah ambato mai yawa. (Suratul Ahzab aya ta 4)
وَالذَّاكِرِينَ اللَّهَ كَثِيراً وَالذَّاكِرَاتِ
أَعَدَّ اللَّهُ لَهُم مَّغْفِرَةً وَأَجْراً عَظِيماً
Da masu ambaton Allah da yawa
maza, da masu ambatonsa mata, Allah ya tanadar musu gafara da lada mai girma”.
[Suratul Ahzab, aya ta 35]
ﺇِﻥَّ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻭَﻣَﻠَﺎﺋِﻜَﺘَﻪُ ﻳُﺼَﻠُّﻮﻥَ ﻋَﻠَﻰ
ﺍﻟﻨَّﺒِﻲِّ ۚ ﻳَﺎ ﺃَﻳُّﻬَﺎ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﺁﻣَﻨُﻮﺍ ﺻَﻠُّﻮﺍ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠِّﻤُﻮﺍ ﺗَﺴْﻠِﻴﻤًﺎ
Lalle, Allah da mala’ikunSa sunã
salati ga Annabi. Ya ku waɗanda
suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a
gare shi. [Suratul Ahzab, aya ta 56]
An karbo daga Abu Huraira Allah
ya kara mishi yarda ya ce Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a
garew shi ya ce:- (Mafi dacewan mutane gare ni ranar alkiyama shi ne wanda yafi
yawaita min salati).
An karbo daga Abdullahi bn Amru
bn Al-As (RA) cewa lallai ya ji Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) yana
cewa: “Wanda ya yi min salati daya, Allah zai yi masa salati goma a madadinta.
Kuma wanda Ya yi min salati goma Allah zai yi masa salati dari a madadinta.
Wanda kuma ya yi min salati dari, Allah zai yi masa salati dubu a madadinta.
Wanda kuma ya yi min salati dubu za mu yi kafada-da-kafada da shi wajen shiga
Aljanna.”
5. CIYAR DA MAI AZUMI ABIN BUƊA
BAKI: Yana daga cikin mafificiyar ibada mutum yayi kokari wajen bawa ɗan'uwansa abin Buɗe baki saboda hadisin da
Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yake cewa: "Duk wanda yaciyar da mai
Azumi abinda zaiyi buɗe
baki yana da kwatan kwacin ladan wanda ya ciyar batare da an rage ladan wanda
ya ciyar ba".Tirmizi yace wannan hadisine hasanun sahih.
6. UMRAH: Yin umrah acikin watan
Ramadan ga wanda Allah ya bashi iko yana daga cikin Aiyukan da ake kwadaitar da
mai Azumi yayi. Amma duk da haka bai kamata mutum yatafi umrah yabar
makwabtansa da danginsa da sauran mabukata a cikin yunwa da halin kakani kayi
ba. Kuma ya kamata mu fahimci cewa, ciyarwa itace abinda Annabi Sallallahu alaihi
Wasallam yafi bawa muhimmanci acikin watan Ramadan.
Ya Allah kasa muna daga cikin
wadanda zaka 'yanta acikin wannan wata, domin darajar Annabi Muhammad
Sallallahu alaihi Wasallam.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.