𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum. Malam yau ina
cikin damuwa, saboda na kwanta baccin rana, kawai sai na ji mijina ya danne ni,
na yi ta kokarin na kwace amma sai ya ci karfina ya sadu da ni, alhalin muna
azumi, don Allah malam a taimaka min da mafita, Allah ya sanyawa zuriyarka
albarka.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus salam, To 'yar'uwa
mutukar yadda kika siffanta, haka abin ya faru, to babu kaffara akan ki, saboda
takura miki aka yi, kuma ba ki da laifi a wajan Allah, amma shi kuwa ya saɓawa Allah, kuma ya keta
alfarmar Ramadana, kuma dole ya yi kaffara, ta hanyar 'yanta kuyanga, in bai
samu ba, sai ya yi azumin sittin a jere, in bai samu dama ba sai ya ciyar da
miskinai sittin, kamar yadda ya zo a hadisin Bukari mai lamba ta : 616.
Allah ne mafi sani.
Amsawa: DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/DIcJIQrWyLP0oBOMSnDi5P
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.