Akan samar da miyar alayyafu ne daga wani nau’in ganye mai suna “alayyafu.” Ba shi da tsawo sosai, sannan yana da ganye mai faɗi. Alayyafu na iya kasancewa mai sabon toho ko mai tsohon toho. Mai sabon toho (yaro) shi ne wanda ganyensa bai yi ƙarfi sosai ba. Irin wannan ganyen ya fi zaƙi da daɗin miya. Mai tsohon toho (tsoho) kuwa, shi ne wanda ya daɗe da shukawa, sakamakon haka, ganyensa kan kasance mai tauri. Irinsa ba a son yin miya da shi saboda ba shi da daɗin miya sosai.
Mahaɗin
Miyar Alayyafu
Akwai abubbuwan da ake tanada, idan za
a haɗa miyar alayyafu waɗanda suka ƙunshi:
i. Alayyafu
ii. Albasa
iii. Daddawa
iv. Gishiri
v. Mai
vi. Ruwa
vii. Sure/yakuwa
viii. Wake
An kawo bayanin yadda ake sarrafa miyar alayyafu a babi na ashirin (ƙarƙashin 20.11). Akan samu bambance-bambance tsakanin yadda ake miyar alayyafu a gargajiyance da kuma yadda miyar take a zamanance. A zamanance, akwai hanyoyi da dabaru daban-daban na aiwatar da miyar alayyafu. Baya ga haka, akan yi amfani da kayan haɗi na zamani da suka haɗa da na ɗanɗano da kayan ƙamshi domin ƙara armashi da kuma ɗanɗanon miyar.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.