Ganyen garafuni shi ma yana ɗaya daga cikin ganyaye da ake amfani da su a ƙasar Hausa. Ganye ne da yake da kunuwa ’yan ƙanana. Bayan haka garafuni yana da wani zare-zare a jikinsa. Shi ma wannan ganye yana yaɗo ne tare da bin danga ko itace ko wani abu kafaffe da ke kusa da tsironta.
Mahaɗin
Miyar Garafuni
Yayin samar da miyar garafuni, akan tanadi abubuwa kamar haka:
i. Albasa
ii. Daddawa
iii. Garafuni
iv. Gishiri
v. Kayan yaji
vi. Mai
vii. Ruwa
viii. Tarugu
ix. Tattasai
x. Wake
Yadda
Ake Miyar Garafuni
Ita ma miyar garafuni akan fara ta ne kamar yadda ake miyar kuka. Wurin da suka bambanta shi ne, yayin da sanwa ta
tafasa, a maimakon a kaɗa kuka, to za a sanya garafuni ne.
Akan wanke ganyen garafunin kafin a sanya shi cikin miya. Kusan ana cin kowane irin tuwo da wannan nau’in miyar, musamman tuwon dawa da shinkafa.
Tsokaci
Miyar garafuni na da matuƙar amfani ga masu jego. Saboda garafuni yana taimakawa wajen ƙara wa mai jego ruwan nono. Baya ga haka, miyar garafuni tana maganin wasu cututtuka da suke shiga a lokacin da mace mai jego ta haihu. A dalilin haka, akan yawaita miyar garafuni yayin da aka yi haihuwa (a wuraren da suke amfani da wannan nau’i na miya). Wannan nau’i na miya dai an fi samunta a ƙauyuka, don haka can ne ta fi shahara.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.