Gudai na ɗaya daga cikin ganyen da ake samu a ƙasar Hausa. Shi ma za a gan shi ɗanyen haki ne mai kunnuwa ƙanana sosai. A wurin ɗibar sa, za a ji shi da ɗan santsi a jikinsa kuma a cikin ganyen yana haɗe da fulawarsa. Sannan a cikin shi in aka fasa ganye yana da ruwa sosai. Ba ko’ina ake samun wannan ganye a ƙasar Hausa ba. Sannan kuma, ya fi tsirowa a wuri mai danshi sosai.
6.20.1
Mahaɗin Miyar Gudai
Akwai abubuwan da za a tanada idan za a haɗa miyar gudai, waɗanda suka
haɗa da:
i. Albasa
ii. Daddawa
iii. Gishiri
iv. Ganyen Gudai
v. Kayan yaji
vi. Mai
vii. Wake
viii. Ruwa
ix. Tarugu
x. Tattasai
xi. Tumatur
xii. Nama (idan da hali)
Yadda Ake Miyar Gudai
A yayin samar da miyar gudai, akan
fara sanwa ne kamar yadda ake miyar alayyafu ko zogale. Sai dai a maimakon a sanya alayyafu,
sai a zuba shi wannan ganye na gudai. Za a wanke shi kafin a sanya. Ba a yanka wannan ganye a
dalilin ƙanƙantarsa, domin kuwa bai fi ganyen zogale a girma ba.
Tsokaci
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.