Miyar guro/ kuɓewa tana daga cikin ’ya’yan wani nau’in tsiro da Hausawa ke shukawa a gida ko a gona da nufin amfani da ita a lokacin da aka buƙaci gudanar wannan nau’i na miya. Akan yi miyar da ɗanyar kuɓewa ko kuma busasshiya. Yayin miyar ta ɗanyar kuɓewa, to sai an yayyanka ta tukuna. Haka ma yayin busar da kuɓewar, ana yayyanka ta ne, a shanya ta har sai ta bushe, sannan kuma a dake ta a mai da ita gari.
Ɗanyar kuɓewa
na iya kasancewa mai laushi, wadda
ita ce ta fi kyau da tagomashi a wajen
samar da nau’in miyar
ɗanyar kuɓewa. Amma
wadda ta riƙa ta yi tauri, akan yanka-yanka ta
ne a shanya domin sarrafa
ta a wurin samar da nau’in miyar busasshiyar kuɓewa.
Mahaɗin
Miyar Kuɓewa
Abubuwan da ake tanada yayin miyar kuɓewa sun
haɗa da:
i. Albasa
ii. Daddawa
iii. Guro
iv.
Kayan Yaji
v. Mai
vi. Ruwa
vii. Tarugu
viii. Tattasai
ix. Nama ko kaza ko kifi (idan da hali)
Yadda
Ake Miyar Guro (Kuɓewa)
Abu na farko da za a yi shi ne a wanke guro sosai a yanka ta da wuƙa. Sannan idan da nama za a yi, ana
iya tafasa shi tare da albasa da magi da gishiri kaɗan. A gefe guda kuma, za a daka daddawa da kayan yaji a
aje gefe ɗaya. Sannan a soya kayan miya kamar yadda aka yi a miyar kuka. Daga nan za a ɗora sanwa, tamkar dai yadda aka
bayyana a nau’o’in miya da aka bayyana a baya.
Bayan sanwa ta dahu, za a kawo kuɓewa a sanya. Idan miyar da kifi za a yi, to ba a sanya
kifin har sai bayan an sanya kuɓewa. Sai a ɗan saka kanwa kaɗan ba da yawa ba, kuma za a buɗe marfin tukunya kaɗan. Buɗe
tukunyar zai hana miyar zubewa, domin da zarar kuɓewar
ta fara nuna, za ta riƙa
kumfa da cika tukunya. Sau da dama akan yi amfani da ludayi domin motsa miyar
gudun kada ta zuba.
Tsokaci
Za a iya cewa, babu wani gari a ƙasar
Hausa da ba a shan miyar kuɓewa. Duk da haka, shan miyar guro yana kawo illa musamman
ga mata masu jego, masu bayar da nono ga jarirai (masu shayarwa). Shan miyar guru ga mai jego na
tsinkar da kaurin nono tare da rage yawansa. A shawarce, ya kamata mai jego ta
nisanci miyar guro, har sai jaririnta ya yi wayo.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.