Kabushi ɗiya (ɗa) ne daga cikin ’ya’yan wani tsiro da yake yaɗo a ƙasa wanda kuma ake amfani da shi yayin samar da miya a ƙasar Hausa. Ɗan kabushi yana da girma sosai, kodayake akan samu wani ya ɗara wani a girma. Launin jikinsa idan yana ɗanye yakan kasance kore. Bugu da ƙari, tsiron kabushi kan yi yaɗo a ƙasa kwatankwacin irin yadda guna ko kankana suke yi. Idan aka yanka cikin nunannen ɗiyan kabushi akan tarar da ’ya’ya a ciki.
Mahaɗin
Miyar Kabushi
Kayan haɗin
miyar kabushi su ne:
i. Albasa
ii. Daddawa
iii. Gishiri
iv. Kabushi
v. Kayan yaji
vi. Mai
vii. Ruwa
viii. Tarugu
ix. Tattasai
x. Tumatur
Yadda
Ake Miyar Kabushi
Akan fara miyar kabushi ne kamar yadda ake fara sauran miyoyi nau’in zogale da alayyafu. Bayan sanwa ta tafasa, sai a kawo
kabushi a zuba. Akan fere wannan kabushi sannan a masa yanka ƙanana. Akan tanadi kabushi da yawa a duk
lokacin da za a yi
miya da shi.
Tsokaci
Akasari mutanen dake zaune a cikin ƙauyuka sun fi amfani da miyar kabushi.
Ba a fiye samun wannan nau’in miya a cikin birane ba. Wannan bai rasa nasaba da
kasancewar a ƙauyuka ne aka
fi shuka kabushi. Akan shuka shi
a cikin gida ko bayan gida ko kuma a gonaki.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.