Rama ganye ne ake samu daga jikin tsiron da ake kira da tsiron rama. Galiban a ƙasar Hausa, ana shuka rama a cikin gida da bayan gida (idan akwai wadataccen fili) da kuma gona. Masana da manazarta sun gano rama tana ɗaya daga cikn ganyaye da ke da amfani ga jikin ɗan Adam. Miyar rama ta jima ana gudanar da ita a wasu ɗaiɗaikun garuruwan da ke cikin ƙasar Hausa. Tsiron rama na ɗan kama da yakuwa (sure), sai dai rama ta fi yakuwa tsawo da faɗin ganye. Ita ma rama ganyenta na da tsami yayin da aka ɗanɗana.
Mahaɗin Miyar Soyayar Rama
Yayin samar da miyar rama, akan tanadi kayan haɗi kamar haka:
i. Albasa
ii. Gishiri
iii. Kanwa
iv. Mai
v. Rama
vi. Ruwa
vii. Tarugu
viii. Tattasai
ix. Tumatur
Yadda Ake Miyar Soyayar Rama
Ita miyar rama ta sha bamban da sauran nau’o’in miya da suka gabata,saboda ita da an soya ta ake cin ta. Da
farko za a wanke rama a saka mata kanwa a dafa ta sannan a
tatse a aje gefe guda. Daga nan, za a jajjaga tarugu da tattasai da tumatur da
albasa (wasu ma ba su jajjagawa sai dai yankawa). Idan an yanka za a soya da mai. Da
zarar sun fara soyuwa, za a saka gishiri da kayan yaji
sannan a ci gaba da soyawa. Bayan ta soyu, sai a ɗauko
rama da ta tsane a zuba a ciki a sake yanka albasa a samanta. Haka za a yi ta soya su tare da rama
har sai sun game sun soyu, wasu suna
ɗan zuba ruwa kaɗan a ciki, wasu kuma haka za a bar miyar a sauke ta. Za a
iya cin miyar da kowane irin tuwo.
Tsokaci
Miyar Soyayyar rama miya ce da akasari manya sun fi shanta saɓanin yara ƙanana. Haka kuma, akan ba wa marar lafiya miyar rama don ya samu ɗanɗano a bakinsa. Ita ma wannan miyar ba ta yawaita sosai a ƙasar Hausa ba.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.