Da busasshen wake ake amfani yayin samar da miyar wake. Akan jiƙa waken da ruwa, a surfe shi, sannan a wanke a cire dusa da hancin waken (wani lokaci kuwa akan bar shi da hancin, wato ba tare da an surfe shi ba). Yayin samar da miyar wake, wake ne babban abin haɗi. Shi ake sanyawa daidai gwargwadon yadda miyar za ta yi kauri. Akasarin miyar wake kuwa na da kauri sosai.
Mahaɗin
Miyar Wake
Kayan haɗin
miyar waƙe sun ƙunshi:
i. Daddawa
ii. Gishiri
iii. Mai
iv. Ruwa
v. Wake
vi. Kayan miya (tumatur, attaruhu, albasa da makamantansu)
Yadda
Ake Miyar Wake
Hanyar da ake bi domin samar da miyar
wake daidai yake da na sauran miyoyin da aka yi bayani a baya. Sai dai a wannan karon, idan sanwa ta tafasa akan sanya wake
ne. Wato wanda aka rigaya aka jiƙa
sannan aka surfe.[1]
Za a rufe tukunyar a bar waken har sai ya dahu ya yi laushi sosai. Daga nan za
a yi amfani da maburkaki a burge shi har sai ya haɗe gaba ɗaya. Da zarar an kammala haka, to
miyar wake ta samu kenan.
Tsokaci
Shan miyar wake na taimakawa sosai a jikin mutum duba da
amfanin wake a jikin ɗan Adam. Wannan ya sa birni da ƙauye duk ake ta’ammuli da miyar wake. Sau da dama
akan ba da shawarar a riƙa
ba wa marar lafiya miyar wake, domin amfaninsa wurin gina jiki. Hasali ma dai,
Bahaushe ya ɗauki wake a matsayin na’ibin nama.
Wato inda ba nama, wake sai ya maye gurbinsa. Haka ma, miyar wake na matuƙar taimakawa ga mata masu juna biyu.
Ko ba komai dai, an yi amanna kan cewa, wake na daga cikin nau’o’in abinci masu
gina jiki sosai. Makaɗa Ali Makaho mai
gurmi ya ɗan fito da wani
abu kaɗan game da
matsayin wake a miya, inda yake cewa:
Jagora:
........................................
:Ba don wake a miya ba,
: Da ka-fi-zabuwa yai tsada.
(Ali Makaho,Waƙar Mandula).
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.