Miyar karkashi na matuƙar kama da ta ayoyo. Saboda haka, kusan za a iya cewa, hanya guda ake bi yayin samar da miyoyin biyu. Sai dai shi ganyen karkashi, ba a wanke shi kafin sanyawa a tukunya. Wannan kuwa na faruwa ne a sanadiyyar yauƙi da ganyen ke da shi. Yayin da aka yi ƙoƙarin wankewa,to kuwa zai lalace cikin ruwa yauƙin ya salwance. Da ma dai, dukkanin miyoyin biyu na da yauƙi sosai. Bahaushen dauri na shuka karkashi a bayan gida ko gona ko ma wani ɓangare daga cikin gida. Har zuwa yau, akan samu gidajen da ke da faɗi inda akan shuka karkashi a cikinsu.
Mahaɗin Miyar Karkashi
Akwai abubbuwan da za a tana da idan
za a haɗa miyar karkashi waɗanda suka
haɗa da:
i. Daddawa
ii. Karkashi
iii. Kayan miya
iv. Gishiri
v. Kayan yaji
vi. Mai (idan an ga dama)
vii. Ruwa
viii. Wake
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.