Miyar zogale, wata nau’in miya ce mai dogon tarihi da Hausawa suke gudanar da ita da ganyen zogale ɗanye ko busasshe. Zogale bishiya ce da ba ta da kauri matuƙa, amma takan yi tsayi gwargwado, wanda kuma take ɗauke da ganyaye ƙanana. Yawanci akan same ta a cikin gidaje ko bayan gidajen Hausawa. A wasu lokuta kuma, akan shuka wannan bishiya a gonaki.
Daga cikin
kayyakin da ake haɗawa a samar da
wannan nau’in miya akwai:
i. Albasa
ii. Daddawa
iii. Gishiri
iv. Gyaɗa
v. Manja ko gyaɗa
vi. Nama ko kifi (idan akwai)
vii. Ruwa
viii. Tarugu
ix. Tattasai
x. Tumatur
xi.
Zogale
A ƙarƙashin 20.12 da ke babi na ashirin an kawo bayani dangane da miyar zogale. Bambancin da ake samu tsakanin yadda ake aiwatar
da miyar zogale a gargajiyance da kuma a zamanance bai wuce na kayan haɗi da kuma yanayin sarrafawa ba.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.