Ticker

Motsa Yatsa Wurin Tahiya

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. A cikin tahiyar Sallah shin mutum zai cigaba da motsa yatsarsa har zuwa wurin yin addu’a ne, ko kuwa dai ba a yi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

A kan mas’alar miƙe yatsa da karkaɗa ta malamai sun saɓa wa juna, amma dai ga abin da Malaman Hadisi suka riwaito, kamar yadda Al-Imaam Al-Mujaddid Al-Albaaniy (Rahimahul Laah) ya kawo a cikin mashahurin littafinsa: Sifatu Salaatin Nabiyy (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) shi ne

Al-Imaam Muslim (2/90-91) da Abu Awaanah (2/223) da Abu-Daawud (1/156) da An-Nasaa’iy (1/186) da Muhammad a cikin ‘Muwattarsa’ (106) da Ahmad (2/65), dukkansu sun riwaito ta hanyar Al-Imaam Maalik (1/111-112) wanda shi kuma ya riwaito da isnadinsa zuwa ga Aliyyu Bn Abdirrahman Al-Mu’aawiy, wanda ya ce

Sahabi Abdullaah Bn Umar (Radiyal Laahu Anhumaa) ne ya ganni ina wasa da tsakuwoyi a cikin sallah, lokacin da na gama sai ya hana ni, kuma ya ce: ‘Ka riƙa yin yadda Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) yake yi mana!’

Na ce: ‘Yaya Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) yake yi?’

Ya ce: Idan Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya zauna wurin tahiya yana ɗora hannun dama a kan cinyarsa ta dama, yana mai shimfiɗa ta a kan cinyar, sai kuma ya dunƙule dukkan yatsun hanunsa na dama, sannan ya yi nuni da yatsarsa da take bin babbar yatsa zuwa jihar alƙibla, sai kuma ya jefa ganinsa gare ta, (watau ya riƙa kallon ta).

A cikin wata riwaya ta Al-Humaidiy: (1/131) da Abu-Ya’alaa: (2/275) da isnadi sahihi daga Ibn Umar (Radiyal Laahu Anhumaa) ya ce: Ita (yatsar) mai korewa ce ga shaiɗan: Duk wanda ke yin haka ba zai yi rafkanuwa ba! Sai Al-Humaidiy ya miƙe yatsarsa.

Haka kuma Al-Humaidiy ya riwaito da isnadin da Al-Albaaniy ya inganta shi daga Muslim Bn Abi-Maryam cewa: Wani mutum ya ga Annabawa an zana su a cikin sallarsu sun yi kamar haka: Sai Al-Humaidiy ya miƙe yatsarsa.

(Aslu Sifatis Salaah: 3/838).

Amma game da karkaɗa yatsar da ya miƙe sai ya ce: Sannan kuma (Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)) ya kasance idan ya ɗaga yatsarsa manuniya, yakan riƙa karkaɗa ta, yana yin addu’a da ita, kuma yana cewa

لَهِيَ أَشَدُّ عَلَى الشَّيْطَانِ مِنَ الْحَدِيدِ

Ita ta fi tsanani a kan shaiɗan fiye da baƙin ƙarfe.

Bayan wannan sai Al-Imaam Al-Albaaniy ya ce: A cikin wannan akwai dalili a kan cewa: Sunnah ita ce mutum ya cigaba da miƙe ta da karkaɗa ta har zuwa sallama. Wannan kuwa shi ne mazhabar Al-Imaam Maalik da waninsa daga cikin Limamai.

Sai kuma ya ce: Daga nan ne kuma yake fitowa a fili cewa: Karkaɗa yatsa a zaman tahiya Sunnah ce tabbatacciya daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam). Al-Imaam Ahmad da waninsa daga cikin Limaman Sunnah sun yi aiki da ita. Don haka, mutanen da suke riya cewa wai hakan wasa ne da bai kamaci a yi shi a cikin sallah ba, sai su ji tsoron Allaah kuma su daina!

(Aslu Sifatis Salaah: 3/853-854).

Wal Laahu A’lam.

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy,

Turo da tambayar ka ta WhatsApp a wannan number. 08164363661

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments