Muhimman Kalmomin Abincin Hausa

Acca: Tsiro ne nau’in hatsi da ke da ƙananan ƙwayoyi farare.

Alabo: Ɓararren rogo da aka shanya ya bushe, wanda ake iya dakawa domin samar da garin alabo.

Alale: Nau’in abinci ne da akan samar daga ƙullun wake. Daidai da alala.

Alala: Dubi alale.

Alallaɓa: Nau’in abinci ne mai laɓa-laɓa.

Alayyafu: Nau’in tsiro ne mai ganye kore da ake amfani da shi wurin miya ko fate da ma wasu nau’o’in abinci na daban.

Albasa: Wani irin nau’in tsiro ne mai dunƙulalliyar saiwa da ganye.

Alkama: Nau’in tsiro ce mai kama da shinkafa, wadda aka fi shukawa a fadama, tana da launi ƙasa-ƙasa.

Amala: Abinci nau’in tuwo da akan samar daga garin ɓawon doya ko rogo da aka shanya sannan aka niƙa.

Aska: Ƙarfe ne da ake amfani da shi yayin samar da alkaki. Yayin da aka ɗebo mulmulallen kwaɓaɓɓen garin alkaki, cikinsa ake sanyawa domin a matse, sai ya fito da shi irin siffar da ake buƙata.

Ayayo: Nau’in ganye ne da ke da yauƙi.

Balugari: Wani ƙaramin ice ne da bai kai muciya girma ba, wanda ake gyarawa tare da sanya masa kunnuwa a ƙarshensa (wasu ƙananan itatuwa da za su fito cako-cako). Ana amfani da shi domin burga miya ko nono ko wani nau’in abinci mai kama da wannan. Daidai da maburkaki ko maburgi.

Barbaɗawa: Amfani da hannu domin ɗebo wani abu (musamman gari) da sanya shi a hankali sannan sama-sama cikin wani abu na daban (misali ruwa cikin tukunya) har sai ya ƙare.

Barwa: Baƙi-baƙin da ake cirewa daga cikin shinkafa kafin a dafa.

Bilanda: Ƙaramin injin na niƙan kayan lambu da zamani ya zo da shi.

Bori: Kumfar da ke fita daga tukunya yayin da ake dafa abinci ko miya.

Burabusko: Daidai da tuwon biski.

Bugawa: Gauraya nau’in mahaɗin abinci da ake yi musamman ƙullu (kamar ƙullun ƙosai) da ƙarfi.

Burgawa: Sanya balugari cikin miya ko nono ko wani nau’in abinci mai ruwa-ruwa tare da murza balugarin domin duk wani gudajin da ke cikin abincin ya baje.

Bushewa (Hatsi): Yin amfani da faifayi wurin fitar da dusa daga surfaffen hatsi.

Bushewa: Yonƙwanewa ko motsewa da abu ke yi sakamakon gushewar ruwan jikinsa.

Ɓarza: Niƙan da aka yi sama-sama, saboda haka abin da aka niƙa bai yi laushi sosai ba.

Ɓawo: Bayan da ake samu na wasu nau’o’in abinci, wanda ake ferewa ko aka ɓare. Misalin abincin da ke ɗauke da ɓawo sun haɗa da masara da rake da dankali da sauransu.

Ɓula: Abinci nau’in tuwo mai santsi da sulɓi da ake samarwa daga gero ko dawa ko masara ko haɗakarsu, wanda ake ajiyewa a ruwa.

Dafa-duka: Nau’in abinci da ake haɗa dukkanin abin haɗin abinci cikin tukunya ɗaya yayin dafawa, galibi shinkafa da aka dafa haɗe da kayan miya.

Dahuwa: Yayin da aka bar abinci saman wuta, to yana ci gaba da dahuwa kenan.

Daka: Sanya wani nau’in abinci (misali gero ko tumatur da sauransu) cikin turmi tare da amfani da taɓarya domin a bubbuga shi har sai ya yi laushi.

Dambu: Nau’in abinci ne wanda akan samar daga wani nau’in hatsi da aka ɓarza.

Dankali: Tsiro ne mai yaɗo da dunƙulallun saiwoyi da ake haƙowa a ci ɗanye ko a dafa. Ya kasance iri biyu, wato dankalin Hausa da ake kira kudaku da kuma dankalin Turawa.

Dankalin Hausa: Dubi dankali.

Dankalin Turawa: Dubi dankali.

Dawa: Tsiro ne nau’in hatsi da ke yin kara mai tsawo kamar gero. Sai dai zangarniyarta ta fi ta gero kauri da kuma girman ‘ya’yan tsaba.

Doya:Ɗaya daga cikin abinci nau’in saiwa, wanda kaurinsa ya fi na rogo, kuma ganyensa na yaɗo musamman yayin da ya samu ice ko wani abin da zai kanannaɗe.

Dunƙulawa: Daidai da mulmulawa.

Dusa: Haki ko bawon da ake cirewa daga jikin hatsi ko makamancinsa yayin da aka bushe shi bayan surfe.

Dutsin Niƙa: Duba magurji.

Ɗaci: Nau’in ɗanɗano ne marar daɗi.

Ɗanɗano: Lasar wani abu (musamman abinci) don a ji yadda ɗanɗanonsa yake. Zai iya kasancewa ɗaci ko zaƙi ko tsami da dai sauransu.

Ɗanye: Duk wani abin da bai nuna ba ko abin da bai bushe ba.

Ɗata: Nau’in tsiro mai ‘ya’ya, wanda ake ci ko a yi amfani da ‘ya’yan domin samar da miya. Daidai da gauta.

Ɗumi: Kalmar da ke nuna abinci ko ruwa na da zafi sama-sama, wato ba zafi sosai ba.

Egushi: ‘Ya’yan wani tsiro da ake amfani da su domin samar da miya.

Faranti: Faffaɗan abin zuba abinci wanda ba shi da marfi, daidai da tire.

Fate: Nau’in abinci da ake yin sa ruwa-ruwa, wanda ake haɗa shi da tsaki da ganyaye da kayan haɗi daban-daban yayin sarrafa shi. Daidai da gwate.

Ferewa: Yin amfani da wuƙa(yuƙa) ko wani abu mai kama da ita domin cire ɓawon wani abinci nau’in dankali da doya da rogo da makamantansu.

Figewa (Ganye): Cire ganye daga jikin itacen wani tsiro kamar su alayyafu ko yakuwa da makamantansu.

Figewa (Tsuntsaye): Cire gashi daga jikin tsuntsun da aka yanka, misali kaza ko agwagwa ko baru da makamantansu.

Filebo: Wani sinadari ne da ke ƙara wa abin sha ƙanshi da ɗanɗano. Ya fi shafar kayan sha ba na ci ba.

Fure: Hudar tsiro ko bishiya da ke fitowa kafin ‘ya’ya. Daidai da huda.

Gagaya: Duba gurgura.

Ganyen Aduwa: Ganyen da akan samu daga bishiyar aduwa.

Ganyen Albasa: Dubi lawashi.

Garahunu: Wani nau’in tsiro mai yaɗo, musamman a jikin danga.

Garas-garas: Kalma ce da ke nuna abinci ba shi da laushi, ko bai dahu ba.

Garau-garau: Shinkafa da wake (ko wani nau’in abinci mai kama da wannan) da akan dafa ta zalla domin a sanya mai da yaji a ci.

Gari: Niƙaƙƙe ko dakakken busasshen abinci nau’in hatsi ko busasshen rogo da makamantansu.

Garin-kwaki: Nau’in gari da ake samarwa daga rogo.

Gasara: Garin ƙullu da ake ragewa, wanda ake zubawa cikin kunu bayan an gama damawa saboda ya ƙara masa ɗanɗano.

Gasawa: Sanya nama a saman wuta har sai ya dahu yadda za a iya ci.

Gaurayawa: Yin amfani da muciya ko balugari ko ludayi domin jujjuya wani abinci musamman wanda ke cikin tukunya a saman wuta, daidai da jujjuyawa.

Gauta: Duba ɗata.

Gero:Tsiro ne na abinci nau’in hatsi dangin maiwa, wanda ake tuwo ko fura ko kunu da shi.

Gudai: Nau’in ganye ne mai kauri da ake amfani da shi wurin miya.

Gudaji: Curi-curin gari wanda bai narke ba a cikin tuwo ko kunu, daidai da ƙolallai.

Gujiya 1: Duba lubbatu.

Gujiya 2: Nau’in tsiro ne na abinci mai kama da gyaɗa da ke zuba ‘ya’ya a ƙarƙashin ƙasa. Daidai da mai-ƙoƙo.

Gumawa: Dafa shinkafar da ke cikin kwalfarta domin a shanya ta, wanda daga baya za a kai niƙa.

Gundura: Yayin da mutum ya ji ya daina jin sha’awar abinci alhali bai ƙoshi ba, to akan ce abincin ya gundure shi.

Gurgura: Yin amfani da haƙora a hankali domin gutsura bayan wani abinci tare da barin ƙwallonsa ciki. Daidai da gaigaya.

Gwagwa: Rariyar ƙarfe ko roba ko kaba mai faɗi da huji-huji ɗauke da mariƙi da ake amfani da shi domin tsame soyayye ko dafaffen abinci. Daidai da matsami.

Gwangwani: Ƙaramin ƙarfe mai lafe-lafe mai siffar kofi da ake amfani da shi wurin dafa nau’o’in abinci da suka haɗa da kek da alale da makamantansu.

Gwate: Duba fate.

Gyaɗa: Nau’in tsiro ne na abinci mai zuba ‘ya’ya ƙarƙashin ƙasa. Tana kama da gujiya.

Hura wuta: Daidai da hura wuta.

Hucewa: Yayin da abinci ya yi sanyi, to ya huce kenan.

Huda: Duba hure.

Hura Wuta: Kunna wuta musamman a murhu. Daidai da hura wuta.

Iza Wuta: Turawa tare da daidaita itatuwan da ke ci da wuta cikin murhu, musamman yayin da aka lura wutar na yin ƙasa-ƙasa ko ƙoƙarin mutuwa, ko kuma fitowa waje daga cikin murhun.

Jajjage: Daddaka kayan miya sama-sama ba tare da sun daku sosai ba.

Jiƙawa: Sanya ruwa cikin wani nau’in abinci domin ya yi laushi ko ya kumbura. Akan jiƙa gero ko dawa ko masara da dai sauransu.

Jirkitawa: Duba juyawa.

Jujjuyawa: Dubi gaurayawa.

Juyawa: Amfani da cokali domin juya wani abinci (musamman wanda gefensa guda ya soyu) domin gefensa da ke ƙasa ya koma sama. Daidai da jirkitawa.

Kabeji: Wani nau’in ganye mai kama da salat.

Kabewa: Duba kabushi.

Kabushi: Nau’in tsiro da ke samar da ‘ya’ya manya masu kama da ƙwarya, akan yi amfani da waɗannan ‘ya’ya domin miya, daidai da kabewa.

Kafa (Kafa): Nau’in tuwo da ake samarwa daga masara.

Kafa (Ɓula): Garin ɓula da aka dafa aka tuƙa kafin a nasa shi.

Ka-fi-likita: Nau’in bishiya ne da ake amfani da ganyenta wurin samar da miya.

Kalaci: Abincin dare, cin abinci.

Kalkashi: Duba yoɗo.

Kankarewa: Yin amfani da wuƙa ko cokali domin fitar da dattin bayan wani abinci, misali citta ko karas da sauransu.

Karas: Nau’in tsiro ne mai yin ‘ya’ya ƙarƙashin ƙasa da ke da ɗan tsayi.

Karkashi: Duba yoɗo.

Karo-karo: Haɗo wani abu da mutane daban-daban kan yi domin a tara wa wani ko wasu daga cikinsu.

Kauri: Yayin da miya ko wani abinci nau’in ruwa-ruwa ya yi kauri, to bai tsinke ba kenan.

Kayan Lambu: Kayan miya da akan shuka a lambu irin su tumatur da albasa da attaruhu da sauransu.

Kirɓawa: Sanya abinci musamman kayan lambu cikin turmi tare da amfani da taɓarya wurin daka shi. Yawanci abin da aka kirɓa yakan kasance jajjage daga ƙarshe.

Kudaku: Dubi dankali.

Kuka: Ganyen da akan samu daga bishiya da ke da suna ‘kuka’. Akan yi amfani da kuka wurin miya da ma wasu nau’o’in abinci na daban.

Kumbura: Tasowa da wani nau’in abinci ke yi ya ƙara yawa yayin da aka sanya masa nono mai tsami (ko yis a zamanance) ko kuma aka jiƙa shi.

Kunu: Nau’in abinci mai ruwa-ruwa da ake damawa.

Kuskus:Ɓarzajjen shinkafa da ake dafawa wasar-wasar domin a sanya mai ko miya a ci. Yanzu akwai kuskus na zamani.

Kuɓewa: Tsiro ne da yake fitowa tare da samar da ‘ya’ya, wanda akan yi amfani da ganyen ko ‘ya’yan domin samar da abinci.

Kuyafa: Duba ludayi.

Kwalfa: Daidai da dusa.

Kwalshi: Abin da akan samu yayin da aka fasa ƙwallon goriba.

Kwando: Wani abu ne da ake saƙawa da geza (yanzu an fi samun kwandon roba ko ƙarfe da ake samarwa a zamanance). Akan yi amfani da kwando domin kife kayan cin abinci da aka wanke, ko kuma tace wasu nau’o’in abinci.

Kwashewa: Ɗebe wani abinci daga cikin tukunya tare da sanya shi cikin ƙwarya ko kwano. Akan yi amfani da mara ko ludayi domin kwashe abinci.

Kwata: Wani abu mai kama da dutse da ake samowa daga daji, wanda ake amfani da shi yayin samar da miya.

Kwaɓawa: Sanya ruwa cikin nau’in abinci (misali gari) tare da cakuɗawa domin ya haɗe wuri guda.

ƘAmshi: Tashin abinci mai daɗin sheƙa a hanci da ake samu daga abinci.

Ƙanƙara: Ruwa ne da ya daskare wuri guda sakamakon sanyi da ya yi sosai.

Ƙasari: Ruwan da ake samarwa bayan an wanke gero. Ƙasari ake tarawa wuri guda domin a yi amfani da shi wurin samar da tuwon ƙasari.

Ƙolallai: Daidai da gudaji.

Ƙoshi: Yayin da mutum ya ji cikinsa ya cika kuma ya gamsu da abinci, to ya ƙoshi.

Ƙulla Dambu: Idan aka ce an ƙulla dambu, to an haɗa dambu kenan.

Ƙulli: Ɗaure wani nau’in abin haɗin abinci cikin leda, kamar gishiri ko kanwa da sauransu.

Ƙullu: Nau’in hatsi da aka markaɗe ya koma ruwa-ruwa, daidai da kwaɓaɓɓen gari.

Ƙullu 2: Adadin gero ko masara da ake ɗiba a ajiye bayan an surfe an wanke kafin a daka ko a kai niƙa (a amanance).

Hau: Kalmar da ake amfani da ita domin nuna irin kumburin da ƙulli yake yi bayan an ajiye shi ya kwana. Daidai da kumbura.

Dawaki: Wani adadi na shinkafa da ake warewa bayan an wanke yayin da za a yi nakiya. Ba a soyawa ko turara dawaki. A maimakon haka, ana zubawa ne a cikin dafaffe ko turararren shinkafar yayin dakawa.

Ƙwalama: Kalma da ke nuna kwaɗayi.

Ƙyalle:Ƙaramin yadi da ake amfani da shi wurin tata ko goge tanda.

Lalo: Wani nau’in ganye mai yauƙi. Daidai da tungurnuwa.

Lauɗi: Danƙon da akan samu ga abinci kamar tuwon rogo ko sakwara.

Laɓa-laɓa: Duba ruwa-ruwa.

Lawashi: Sunan da ake kiran ganyen da ke jikin albasa da shi. Daidai da ganyen albasa.

Lubbatu: ‘Ya’yan tsiro da ke kama da gyaɗa, daidai da gujiya.

Ludayi: Sunan abin da ake amfani da shi yayin ɗibar miya ko fura ko kunu. Daidai da kuyafa.

Luƙui: Kalmar da ke nuna niƙa ya yi laushi.

Maburkaki: Duba balugari.

Madambaci:Ƙwarya da aka huhhuda, wanda ake amfani da ita domin yin dambu ko tuwon biski.

Magurji: Abin da ake amfani da shi domin markaɗa kayan miya ko zamar da hatsi gari.

Mai-ƙoƙo: Daidai da gujiya.

Maiwa: Wani nau’in gero ne mai launin fari, wanda kan daɗe bai nuna ba.

Marmasawa: Murje wani abu da hannu ko ta hanyar amfani da wani abu na daban, domin abin ya zama gari-gari. Ana marmasa abubuwa kamar magi.

Masa: Nau’in abinci da ake samarwa daga ƙullin hatsi a toya shi a tanda, daidai da waina.

Masara: Tsiro ne nau’in hatsi mai tsaba manya-manya. Sai dai masara na yin goyon ‘ya’ya a bayan karanta.

Mataci: Sunan abin da ake amfani da shi domin tace ƙullu ko makamancinsa.

Matsami: Dubi gwagwa.

Matsewa: Sanya abinci tsakanin tafin hannu guda biyu tare da matsa shi da nufin fitar da ruwan da ke jikinsa.

Miya Soyayyiya: Wannan nau’in miya ne da ake yin ta ba tare da sanya ruwa ba.

Muciya: Sanda ce madaidaiciya wanda ake gyara ta musamman saboda tuƙin tuwo da makamancinsa.

Mulmulawa: Yin amfani da hannu ko ƙaramar ƙwarya domin murza abinci zuwa dunƙule (gewayayyen curi).

Murhu: Wurin da ake hura wuta da itace tare da aza tukunya. A gargajiyance duwatsu uku ke samar da murhu, sai dai akwai nau’o’in murhu da zamani ya zo da su.

Murjewa: Yin amfani da hannu ko wani abu na daban domin marmasa wani nau’in abinci sama-sama da niyyar ɓare ɓawon da ke jiki. Akan murje abubuwa nau’in gyaɗa da makamantansu.

Nama: Nau’in abinci da akan samu daga dabbobi ko tsuntsaye yayin da aka yanka su.

Nasawa: Tsoma mulmulallen abinci cikin tafasasshen ruwa ko mai da niyyar dafawa ko soyawa.

Niƙawa: Yin amfani da dutsin niƙa ko injin niƙa na zamani domin mayar da wani busasshen abinci zuwa gari, misali gero ko dawa da makamantansu.

Nono: Farin ruwa mai kauri da akan tatsa daga hantsar dabbobi, wanda da shi suke shayar da ‘ya’yansu.

Oda: Wani ɓangare ne daga cikin kayan cikin dabbobi.

Ogobonno: Nau’in tsiro ne wanda aka samo shi daga ƙasar Yarabawa.

Ogun: Nau’in ganye ne mai yaɗo.

Rama: Wani nau’in ganye mai tsami yana da dogon kara, kuma ana dafa ganyensa a yi kwaɗo.

Regaya: Yin amfani da ƙwarya ko roba ko makamancinsu domin sanya hatsi ko waninsa, tare da amfani da ruwa cikin hikima domin fitar da tsakuwowi da kuma datti daga cikin hatsin.

Rogo: Wani tsiro ne wanda ake cin saiwarsa ɗanya ko dafaffiya, sannan cikinsa fari ne fat.

Ruwa-Ruwa: Abincin da ya kasance ba mai tauri ko tsararo sosai ba.

Sakwara: Dafaffiyar doyar da aka kirɓa, daidai da tuwon doya.

Samo: Nau’in gari da akan yi daga alkama, wanda yawanci kamfani ke samarwa a cikin leda.

Sanga-Sanga: Nau’in ganye ne mai kama da tafasa, sai dai ganyensa ya fi na tafasa faɗi.

Sanwa: Ɗora abinci bisa wuta bayan an yi shirin girki.

Saukewa: Sauko da tukunya daga kan murhu zuwa ƙasa bayan an kammala dafa abinci.

Sulala (Tuwo): Barin tuwo a rufe kan wuta na wasu mintuna bayan an tuƙa shi kafin kwashewa.

Sulalawa: Duba zabga.

Sure: Nau’in ganye ne mai yaɗo da ake amfani da shi wurin miya ko kwaɗo, daidai da yakuwa.

Surfe: Daka jiƙaƙƙen hatsi cikin turmi da taɓarya don fitar da dusa.

Shan Iska: Barin hatsi ko wani abin da aka wanke domin ya ɗan bushe sama-sama.

Shinkafa: Nau’in tsiro ne da ke yin tsaba da aka fi shukawa a fadama, ana dafa ƙwayoyinta a ci ko a yi tuwo.

Taɓarya: Ice ne da aka sassaƙawa mai ɗan matsakaicin tsawo mai mulmulallen kanu guda biyu, domin amfani da shi wurin daka ko surfa ko sussuke abin da aka sanya a turmi.

Tafasa (ruwa): Zaɓaɓɓakar da ruwa kan yi cikin tukunya yayin da ya yi zafi sosai.

Tafasa (tsiro): Wani nau’in ganye da ke fitowa yayin da aka yi ruwan sama. Yawanci tafasa na fitowa ne da kanta ba tare da an shuka ba.

Talge: Sanya ruwan sanyi a cikin madaidaicin gari tare da zuba wannan gari cikin tafasasshen ruwan da ke kan wuta da nufin ɗaure ruwan kafin a sanya garin tuwo.

Tanda: Kasko mai faɗi na suyar waina, daidai da masa.

Tankaɗe: Yin amfani da rariya domin cire gari daga cikin tsaki.

Tarfawa: Sanya abu ɗan kaɗan ba da yawa ba. Misali, tarfa mai a cikin tandan masa.

Tasar Suya: Tasa madaidaiciya da ake amfani da ita yayin suya, kamar na nama ko ƙosai da makamantansu.

Tauri: Yayin da abinci ya kasance ba ruwa-ruwa ba, daidai da ƙarfi ko tsauri.

Taiba: Abinci nau’in tuwo da ake amfani da garin rogo domin samar da shi.

Tire: Duba faranti.

Tukunya: Mazubi ne da aka gina da laka sannan aka gasa da wuta, wanda ake amfani da shi domin dafa abinci. Yanzu a zamanance an fi amfani da tukunya ƙarfe ko ta dalma ko ta silba.

Tumatur: Nau’in ‘ya’yan tsiro mai yaɗo da ke yin ja yayin da suka nuna. Akan yi amfani da su a yi miyar dage-dage ko a abinci iri daban-daban.

Tungurnuwa: Dubi lalo.

Tunkuza: Gyaɗar da aka markaɗa sannan aka cire manta (man gyaɗa).

Tuƙawa: Yin amfani da muciya domin jujjuya abinci cikin tukunya, musamman nau’in tuwo don ya haɗe ya yi tauri.

Turarawa: Sanya zafin tiririn da ruwa ke yi ya riƙa dukan wani abinci da aka aza saman ruwan musamman cikin madambaci.

Turmi: Fafaffen itace wanda aka gyara don a dinga daka hatsi ko wani abu a ciki, ta hanyar amfani da taɓarya.

Turon Rogo: Tuwon da ake amfani da rogo domin samar da shi.

Tuwo: Nau’in abinci ne da ake yi da niƙaƙƙen garin hatsi nau’in gero ko dawa ko masara aka tuƙa a tafasasshen ruwa, aka kwashe.

Tsaba: Sunan da ake amfani da shi wajen kiran casasshen hatsi ko shinkafa da makamantansu.

Tsagawa: Sanya wani abu mai kaifi domin raba wani nau’in abinci (yanka wani nau’in abinci), kamar gwaiba ko mangoro ko kankana da sauransu.

Tsagwaro (Tuwon Ƙasari): Ruwan da ake tsiyayewa bayan ƙasari ya kwanta.

Tsaki: Guragutsai da ke saura saman rariya bayan an tankaɗe niƙaƙƙen gari.

Tsamewa: Yin amfani da ludayi ko hannu ko wani abu na daban domin cire wani abinci daga cikin ruwa na zafi ko na sanyi ko mai ko miya da sauransu. Misali, ana tsame naman da aka soya daga cikin mai.

Tsami: Wani nau’in ɗanɗano mai ta da tsikar jiki, wanda akan samu daga lemo ko tsamiya.

Tsanewa: Jinkirtawa domin sauran ruwan da aka wanke hatsi da shi ya koma ƙasa bayan an tsiyaye yayin da ake wankewa.

Tsaroro: Kalmar da ke nuna tsinkewar abinci mai ruwa-ruwa, wato rashin kauri.

Tsinke: Ƙaramin siririn ice ko ƙarfe da ake amfani da shi domin tsira nama ko kifi ko wani nau’in abinci, musamman lokacin da za a gasa.

Tsinkewa: Yayin da wani nau’in abinci ya yi tsaroro wato bai yi kauri ba, to ya tsinke kenan.

Tsiyayewa: Karkata ƙwarya ko roba ko wani abin da ake wanke hatsi ko wani nau’in abinci domin ruwan da aka yi amfani da shi yayin wankewar ya zube ƙasa.

Wake: Nau’in tsiro ne na abinci wanda ke yaɗo kamar rogo; yana da ‘ya’ya ƙanana cikin kwanso. Sai dai akwai ƙalilan daga irinsa da ke miƙewa sama kawai ba tare da yaɗo ba.

Waken Suya: Nau’in tsiro ne na abinci mai matuƙar kama da waken, sai dai bai kai wake girma ba.

Wasa-wasa: Dafa hatsi ba tare da an niƙa ba, domin a sanya mai a ci.

Yami: Daidai da tsami.

Yankawa (Dabbobi da Tsuntsaye): Yin amfani da wuƙa ko wani abu mai kaifi domin yanka a wuyan dabba ta hanyar Musulunci, domin amfani da namanta a matsayin abinci ko wani abu makamancin wannan.

Yankawa (Kayan Miya): Yin amfani da wuƙa ko wani abu mai kaifi domin gututtsura kayan miya zuwa ƙanana-ƙanana.

Yauƙi: Santsi da akan samu ga wani nau’in abinci, misali karkashi ko lalo da sauransu.

Yoɗo: Nau’in ganye mai yauƙi da ake amfani da shi wurin samar da miya. Daidai da karkashi ko kalkashi.

Yunwa: Rarakewar ciki tare da jin buƙatar cin abinci.

Zabga (Nama): Dafa nama sama-sama. Daidai da sulalawa.

Zaɓalɓala: Duba dahuwa.

Zaɓarɓaka: Duba dahuwa.

Zogala: Dubi zogale.

Zogale: Ganye da akan samu daga bishiyar zogale, wanda ake amfani da shi wurin miya ko kwaɗo, daidai da zogale

The book “Cimakar Bahaushe” (Diets of the Hausa People) is a collection of 293 traditional and modern diets of the Hausa people. Detailed explanations of the recipes and ingredients are provided. Comments are provided on the areas of the Hausa land where specific diets are mostly found, the age categories of people that usually use it, as well as the scientific impact of some of the diets to human biology.  Data is collected from interviews with different categories of people including:  i.                    Food sellers within the Hausa land: Mainly to have an idea of recipes on the diets.  ii.                  People of older age: Mainly to have insights on traditional diets of the Hausas.  iii.               Hausa scholars: Mainly to verify and justify the validity of the information obtained as well as provide further expert explanations on the diets.  Moreover, over two hundred (200) pieces of literature were reviewed to have better insight on the topic in question as well as get scientific and professional clarifications on some key concepts relevant to the research. The pieces of literature cover major relevant phenomena such as diet and hunger. Others are on the Hausa land and the Hausas.  The book contains thirty-three (33) chapters. Chapter one is the main introduction in which a concise explanation is provided on the Hausas, their history, their land, social life, and transformations due to globalization, acculturation, and modernity. Chapter two detailly discusses the concepts of diet and food from the Hausa point of view. That includes the meaning and the usage of diets in some Hausa works of literature both verbal and written (i.e. prose, poetry, proverbs, etc.).  Chapters three and four discuss the sources of Hausa diets and their forms accordingly. Chapters five to seventeen discuss some traditional Hausa diets including hard and soft ones. Chapter eighteen concentrates on the influence of modernity and globalization on Hausa diets. It has been discovered that there have been some significant changes in the Hausa diets ranging from recipes to kitchenettes.  Chapters nineteen to thirty-two discuss modern Hausa diets. Some traditional diets are still retained with little modifications, while on the other hand, there are a lot of new ones. Chapter thirty-three discusses “hunger” from the Hausa point of view. The relationship between hunger and food is examined. Additionally, the use of hunger in various Hausa literary works is studied. It is concluded that hunger is like a disease whereby its cure is food.  7th November 2022
Citation: Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

Post a Comment

0 Comments