𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamou aleikoum, malam ina
tambaya, ni ce na kasance na haihu wata daya kafin Ramadan, da Ramadan ya zo
ban yi azumi ba, ban ma gwada ba ballantana in ga zan iya ko kuwa, kawai sai na
fake da ciyarwa ban yi azumin ba, to malam ramkaci zan yi ko chiyarwa zan yi?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salamu, Game da
hukuncin mace mai ciki da mai shayarwar da suka sha azumi, malaman Musulunci
sun yi saɓani game
da abin da ke kansu na hukunci, shin ciyarwa za su yi kaɗai, ko ramawa kawai, ko kuma ciyarwa da
ramawa?
Waɗannan
zantuttuka guda uku, wanda ya fi rinjaye a cikinsu shi ne
Mai ciki da mai shayarwa idan
suka sha azumi saboda kasawa ko tsoron kada su jigata, ko saboda tsoron kada
abin da ke cikin nasu ya jigata, to abin da ke kansu shi ne za su rama wannan
azumin ne da suka sha a lokacin da suka sami dama, ko da an sami jinkirin
ramuwar saboda wata lallura. Saboda mai ciki da mai shayarwa ana riskar da su
ne a cikin marasa lafiya da matafiyan da suka sha azumi.
Sheikh Abdul'aziz Bn Baaz ya ce:
"Mai ciki da mai shayarwa hukuncinsu ɗaya
da maras lafiya, idan azumi ya tsananta a gare su an shar'anta masu karyawa,
ramuwa ta tabbata a kansu a lokacin da suka sami damar hakan, su kamar marasa
lafiya ne, wasu daga cikin malamai sun tafi a kan cewa abin da ke kansu shi ne
ciyar da miskini a kowace rana, sai dai wannan magana ce mai rauni wadda aka
rinjaya. Abin da yake daidai a kansu shi ne za su rama ne kamar hukuncin
matafiyi da maras lafiya , saboda faɗin
Allah mai girma da buwaya da ya ce:
فَمَن كَانَ مِنكُم مَّرِیضًا أَوۡ عَلَىٰ سَفَرࣲ
فَعِدَّةࣱ مِّنۡ أَیَّامٍ أُخَرَۚ
"Wanda ya kasance maras
lafiya a cikinku, ko a halin tafiya, to sai ya rama a wasu ranaku na
daban" (Suratul Baqara, aya ta 184.)
Duba Majmú'u Fataawá na Ibn Baaz
(15/225).
Wannan ita ce fahimtar Fataawal
Lajna a mujallad na 10 shafi na 220, kuma ita ce fahimtar da ta fi rinjaye a
wurin mafi yawan malamai.
Allah ne mafi sani.
Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
https://t.me/TambayaDaAnsa
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.