Gabatarwa
A babi na goma sha shida an kawo bayanai dangane da nau’o’in abincin ƙwalama a gargajiyance. Misalan abincin ƙwalama da aka kawo a babin sun haɗa da, alewar gyaɗa da kantun gana da hanjin ligidi da sauransu. Wannan babi zai mayar da hankali kan nau’o’in abubuwan maƙulashe da ake samu a zamanance.
Alewar Madara
i. Filebo
ii. Kwakwa
iii. Madara kwata
iv. Suga
A ɗora suga a wuta a saka ruwa kaɗan a bar shi ya dafu. Idan ya dafu, za a ga ya yi danƙo-danƙo. Daga nan za a gurza kwakwa a saka madara ana yi ana tuƙawa da ludayin miya ko cokali. Za a bar ta da ruwa-ruwa. Bayan nan sai a samu tire a ɗora leda a samansa a shafa mai a jikin ledar, sannan a kwashe alewar madarar a zuba a cikin tiren. Za a bar ta ta sha iska lokaci kaɗan, kafin a fara yanka ta.
Gullisuwa
Za a haɗa
madara da suga a kwaɓa da ruwan ɗumi. Idan za a kwaɓa, da tauri za a yi kwaɓin. Bayan nan a dinga ɗiba
ana mulmulawa kamar ƙwallo amma ƙanana-ƙanana. Da zarar an kammala mulmulawar, sai a ɗora
mai a tukunya. Bayan man ya yi zafi, sai a soya gullisuwa. Ana sanya wuta kaɗan-kaɗan
a lokacin suyar.
Kwakumeti
i.
Kwakwa
ii.
Suga
Za a zuba suga a cikin
tukunya a ɗora bisa wuta ba tare da an saka ruwa ba. Sai a samu ludayi a yi ta juyawa har ya
narke. Daga nan sai a
gurza kwakwa a zuba a ciki a yi ta tuƙawa har ya haɗe gaɓa ɗaya.
Idan ya dafu,
za a ji yana ƙamshi sai a
sauke a rinƙa mulmulawa.
Ɓalɓalo (Carbin Malam)
i.
Kwakwa
ii.
Lemon Tsami
iii.
Suga
Za a zuba suga a cikin tukunya a dafa shi ya dafu. Daga nan sai a goge kwakwa a zuba a cikin sugan tare da lemon tsami. Idan ya dafu, sai a bar shi ya huce, daga nan sai a fara mulmulawa. Bayan nan za a samu farar leda
doguwa a mulmula shi kamar ƙwallo
a saka a ciki a
ɗaure, haka za a yi ta yi har a gama.
Alewar Gyaɗa
a. Gyaɗa
b. Suga
A daka gyaɗa sai ta yi gari, sai a zuba suga a tukunya a ɗora a wuta, ba sai an sa ruwa ba. Za a yi ta
juyawa har sai ya koma ruwa. Daga nan sai a zuba gyaɗar a yi ta tuƙawa
har sai ta yi ja. Bayan ta yi ja, za a samo faranti a shafa masa mai (man zai
hana gyaɗar ta kama shi idan an zuba). Sai a zuba wannan gyaɗar da aka dafa cikin suga a kai. Bayan ta bushe, sai a riƙa ɓallawa ko yankawa daidai gwargwadon girman da ake buƙata.
A Ci Da Mai
a. Albasa
b. Garin masara
c. Mai
d. Ruwa
e. Yaji
Za a ɗora
tukunya da ruwa a bisan
wuta, kuma za a bar ta har sai ta tafasa, sannan a
yi talgen garin masara ko ƙullunta.
Za a bar shi ya dafu sosai sannan a juye a saman tire. Daga nan sai a soya mai a malale samansa, sai kuma a ƙara albasa da yaji. Za a riƙa yayyankawa da wuƙa
ko cokali.
Alallaɓa/Ƙwalan (Ƙwalan Na Taɓi)
i. Albasa
ii. Fulawa
iii. Gishiri
iv. Magi
v. Mai
vi. Ƙwai
vii. Ruwa
viii. Tarugu
ix.
Tattasai
Za a kwaɓa
fulawa tare da tarugu da tattasai da albasa da magi da gishiri sannan a fasa ƙwai a ciki. Idan an kwaɓa, za a saka ɗan mai a saman marfin kwano wanda aka ɗora a saman wuta sai a riƙa soyawa sama-sama.
Ɗan Madaro
i. Madara
ii. Mai
Za a sanya mangyaɗa cikin tukunya a ɗora bisan wuta, sai a bar shi ya soyu ba tare da albasa ba. Daga nan sai a zuba madara a ciki sannan a yi ta juyawa. Za a tabbatar ba ta yi ƙololo/gudaji ba. Za a ci gaba da juya ta har sai ta koma ruwan ƙasa. Daga nan sai a samo tire a shafa masa mai, sannan a juye a cikinsa. Tun kafin ta sha iska, za a fara ɗiba kaɗan-kaɗan ana mulmulawa. Za a ajiye waɗannan mulmulallun a gefe guda. Da zarar an ƙare, an kammala ɗan madaro kenan.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.