Kundin Digiri Na Biyu (M.A Hausa Culture) Da Aka Gabatar A Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya, Jami'ar Bayero Kano (Maris, 2024)
Nazarin Tubalan Turken Zuga A Waƙoƙin 'Yan Tauri Na Sale Kudo Kusada
Aminu Musa
07036420021
ameenumusa12@gmail.com
SADAUKARWA
wannan
aiki nawa sadaukarwa ne ga Mahaifina Marigayi Musa Ibrahim Dansarai da
Mahaifiyata da Matana Kursiya Abdullahi da Rahanatu Yahaya. Haka kuma
sadaukarwa ne ga yara na Jafar da Aminatu da Aisha(mimi) da Asma'u (Husnah) da
Al-Ameen (little) Aminu Musa. Allah ya ji ƙan Baba da Rahama ya
yi wa zuriya ta da ta sauran al'ummar Musulmi Albarka baki ɗaya.
GODIYA
Dukkan
godiya da yabo sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki, tsira da Amincinsa su ƙara tabbata ga
fiyayyen halitta cika makin Annabawa ɗan gata Muhammadur rasulillahi sallallahu
alaihi wassalam.
Ina
miƙa
godiya ta ga Malamina jagoran wannan aiki Dr. Murtala Garba Yakasai wanda cikin
ƙaddarawar
ubangiji da taimakon sa da shawarwarinsa da goyon bayansa wannan aiki ya
kammala, ina godiya da irin karɓa da kulawar dana samu gare sa. Allah ya ƙara masa lafiya da
yalwar arziki. Haka kuma ina godiya ga dukkan malamaina na sashe bisa irin
taimako da haƙuri da jajircewa da su kai wajen koyar da mu muhimman
Al'amura na ilimi da zasu tallafi rayuwar mu ta duniya da kuma lahira, Muna
godiya Allah ya saka masu da mafificin alkhairi Amin.
Sannan
ina godiya ga iyalaina da dangina da sauran abokan aikina da na karatu na a
matakai mabambanta tun daga na secondary dana NCE da na Digirin Farko dana
wannan Digiri na biyu dana gabatar Allah ya tallafi ƙoƙarin kowa ya biya wa
kowa bukatu na alheri Amin.
TSAKURE
Wannan bincike ya yi
bayani a game da tubalan turken zuga ne a waƙar Tauri ta Sale Kudo
Kusada. Tubalan turken zuga na nufin yadda mawaƙa suke bin wasu
hanyoyi daban-daban wajen kambama ko kururuta ko zuga kansu ko iyayen gidansu
ko kuma wasu makusantansu. Mawaƙan Tauri suna amfani da tubalan turken zuga wajen fito da
martaban ɗan Tauri da wasu iyayen gidansu, kamar yadda aka sami
hakan a wasu waƙoƙin Sale Kudo kusada wanda hakan ya haifar masu da wani
tasirin da kwarjini da kuma tabbatar da irin sunan da suka yi a idon duniya. An
yi amfani da ra'in waƙar baka Bahaushiya wadda Farfesa Sa'idu Muhammad Gusau ya
samar a shekara 1993. Binciken yabi hanyoyin tattara bayanai kamar shiga ɗakunan karatu inda
aka dubi ayyukan magabata da suke da alaƙa da wannan aikin. An
kuma saurari waƙoƙin Sale Kudo tun daga na kaset da waɗanda ya yi a fili
wurin wasan tauri da wasu da ya rera a lokacin da ake hira da shi wurin tattara
bayayanan wannan aiki. Binciken ya tabbatar da cewa Sale Kudo Kusada ya bayar
da gudummuwa musamman wajen kare martaban harshen Hausa da kuma adana wa harshen
wasu hikimomi da Mai duka ya hore masa.
Wannan bincike ya
gano 'yan tauri suna amfani da maganganun masu yi masu kiɗa domin samun nishaɗi da ƙara
masu ƙaimi da zuga su domin cire tsoro wajen shiga daji da kuma
tunkarar abokan adawa musamman ta ɓoye sunayensu na ainihi da alaƙanta su
da wasu shahararrun abubuwa masu buwaya ta musamman. Daga ƙarshe
binciken ya bada shawarwari domin samun nasara da ci gaba a cikin aikin sana'ar
tauri da wasannin da ake aiwatarwa na Tauri na yau da kullum.
Muhimman kalmomi:
nazari da tubala da turke da zuga da waƙoƙi
ABSTRACT
This
study eɗplains about the song
Tauri by Sale Kudo Kusada. Zuga refers to how singers follow different ways in
kambam or kukuruta or zuga themselɓes or their parents or some of their close
ones. The Tauri singers use the Zuga bring out the dignity of the Tauri people
and some of their family members, as it was found in some songs of Sale Kudo
Kusada, which caused them to haɓe a certain influence and charisma and to confirm the
reputation they haɓe made in the eye of
the world. The idea of the Bahaushiya oral poetry was used which was deɓeloped by Professor
Sa'idu Muhammad Gusau in 1993. The research praised the methods of data
collection such as entering the libraries where the works of the ancestors
related to this work were looked at. Sale Kudo's songs were also listened to
from the tapes and the ones he made in public at the tough game and others that
he sang during the interɓiew at the gathering
of information for this project. The inɓestigation confirmed that Sale Kudo Kusada
has contributed especially in protecting the reputation of the Hausa language
and preserɓing the language some
of the wisdom taught to him by Mai Duka. This study found out that the
hardliners use the words of eɗtremists to entertain and motiɓate them to remoɓe their fear of going
into the forest and confronting opponents, especially by using their real names
and associating them with popular things. a special buffalo. At the end of the
study, it proɓides recommendations
for success and progress in the work of the tauri profession and the daily
tauri games.
ABUBUWAN DA KE CIKI
Shaidarwa
- i
Tabbatarwa
- ii
Shafin Amincewa - - iii
Shafin Shaidarwa - - iv
Sadaukarwa
- v
Godiya
- vi
Tsakure
- - - vii
Abstract
- viii
Abubuwan Da Ke Ciki - ix
BABI NA ƊAYA
1.0
Shinfiɗa - 1
1.1
Dalilin bincike - - 1
1.2
Manufar bincike - 1
1.3
Muradin Bincike - 2
1.4
Tambayoyin bincike - 2
1.5
Iyakancewar bincike - 3
1.6
Gudummuwar bincike - 3
1.7
Turken Zuga - - 3
1.7.1
Sarrafa Harshe - 4
1.7.2
Ma'anar Kirari - 5
1.7.3
Ma'anar Tauri - - 6
1.7.4
Waƙoƙin Tauri - 7
1.8
Taƙaitaccen
Tarihin Sale kudo Makaɗin Tauri - 8
1.8.1
Asalin Inkiyar Kudo - 8
1.8.2
Yanayin Sale Kudo - 8
1.8.3
Sana'o'in Sale Kudo - 9
1.8.4
Sana'ar Kiɗan Tauri - 9
1.9
Garin kusada - - 10
1.15
Naɗewa - - 11
BABI NA
BIYU
2.0
Shinfiɗa - 12
2.1
Ayyukan Da Suka Gabata - 13
2.1.1
Kundayen bincike - 13
2.2
Mujallu Da Maƙalu - 17
2.3
Bugaggun Littattafai - 22
2.4
Ra'in Da Za A Ɗora Bincike - 24
2.5 Dangantakar Ra'in
Da Bincike. - 25
2.6
Naɗewa - 25
BABI NA
UKU
3.0
Shinfiɗa - 26
3.1
Nau'in bincike - - 26
3.2
Sigar bincike - - 26
3.3
Kayan Aikin bincike - 27
3.4
Ginshiƙan Bayanai - 27
3.4.1
Karanta Ayyuka A Ɗakunan Karatu - 27
3.4.2
Tattaunawa da Wasu 'Yan Tauri - 28
3.4.3
Tattaunawa da Masana Da Manazarta A Kan Tauri - 30
3.4.4
Tattaunawa da Masana ilimin tauri - 31
3.4.5
Juyowa da Sauraren Hira da Aka Yi da Makaɗin Tauri Sale kudo - 33
3.5
Ɗa'ar
Gudanar da bincike - 33
3.6 Naɗewa - 34
BABI NA HUƊU
4.0
Shinfiɗa - 35
4.1
Tubalan Gina Turken Zuga A Waƙoƙin Tauri Na Sale Kudo
Kusada - 35
4.2
Tubalan Kamantawa - 35
4.2.1
Tubalan Kamantawa ta Daidaito - 37
4.2.2
Tubalan Kamantawa Ta Fifiko - 39
4.2.3
Tubalan Kamantawa Ta Gazawa (Kasawa) - 41
4.3
Tubalan Kambamawa - 44
4.3.1
Tubalan Kambamar Zulaƙe - 44
4.3.2
Tubalan Kambamar Yabo - 47
4.4
Tubalan Alamtarwa - 48
4.4.1
Tubalan Alamtarwar Amfani Da Abu Marasa Rai - 49
4.3.2
Tubalan Amfani Da Abu Masu Rai - 51
4.5
Tubalan Siffantawa - 54
4.5.1
Tubalan Gajeriyar siffantawa - 55
4.5.2
Tubalan Doguwar siffantawa - 57
4.6
Tubalan Dabbantarwa - 59
4.6.1
Tubalan Amfani Da Dabbobin Gida - 60
4.6.2
Tubalan Amfani Da Dabbobin Daji - 62
4.7
Tubalan Abuntarwa - 63
4.7.1
Tubalan Abubuwa Masu Motsi - 65
4.7.2
Tubalan Abubuwa Kafaffu - 67
BABI NA
BIYAR
5.0
Shinfiɗa - 70
5.1
Taƙaita
Bincike - - 70
5.2
Sakamakon Bincike - 71
5.3
Gudummuwar Bincike - 72
5.4
Shawarwarin Bincike - 72
5.5
Naɗewa - 73
Manazarta
- 74
Rataye - 77
Rataye
- 80
BABI NA
ƊAYA
1.0 Shinfiɗa
Wannan
babi zai yi bayani ne a kan dalilin bincike da manufar bincike da muradan
bincike da tambayoyin bincike da kuma iyakancewar bincike da gudummuwar
bincike.
Duk
a cikin babin za a kawo ma'anar adon harshe da ta kirari sannan za a yi bayanin
ma'anar Tauri da kuma tarihin makaɗin Tauri Sale Kudo a dunƙule.
1.1 Dalilin Bincike
Bincike
ne da aka gabatar domin ƙara samar da abun bita ga ɗalibai da masu Nazarin Harshen Hausa, musamman
a ɓangaren Al'ada da
Adabi, sannan an gabatar da binciken ne domin cikasa wata ƙa'ida ta samun
takardar digiri na biyu. Haka kuma binciken zai ƙara fito da waɗansu hikimomi na
azancin magana da ke ƙunshe cikin Kirarin makaɗan Tauri domin nusar da mai karatu ko
nazari. Duk yana daga cikin dalilin wannan bincike nazartar waɗansu ɓangarori da suka haɗa wasu turakun zuga
da ya ƙunshi kanantawa wadda ta haɗo da kamance na daidaito da na fifiko
da kuma na gazawa, sannan kambamawa da jinsintarwa da abuntarwa da Dabbantarwa
da Alamtarwa da kuma kinaya a matsayin matakan zuga 'yan tauri a cikin kiɗa.
1.2 Manufar Bincike
Manufar
wannan bincike an gina shi ne a kan fito da wasu abubuwa da suka shafi wasu
sifofi da halaye na rayuwar al'ummar Hausawa kamar yadda makaɗin Tauri Sale Kudo
yake kawo wa a cikin kiɗansa, haka kuma za a
fito da yanayin Zugar kuma za a yi sharhi da bayanin maƙunshiya na zugar da
ya ke furtawa a lokacin da ya ke yi wa Ɗan Tauri kiɗa.
1.3 Muradin Bincike
- Binciko ire-iren hikimomin zance masu
alaƙa da zuga da makaɗin Tauri yake
amfani da su a lokacin da ya ke wa 'yan Tauri kiɗa
- Fito da yadda ya ke sarrafa harshe a
cikin kaɗe-kaɗen 'yan Tauri da
nuna ƙarfin maganinsa ta hanyar danganta shi
da wasu halittu.
- Taskace halayen abubuwan da ya ke alaƙanta
'yan Tauri da su.
- Zayyano ire-iren abubuwan da ya ke
lissafowa domin kambama ɗan Tauri
- Tantance yadda makaɗin ke duba
halayyar wasu abubuwa cikin Waƙoƙin
nasa.
1.4 Tambayoyin
Bincike
Dukkanin
binciken ilimi yana da wasu keɓantattun tambayoyi da ake sa ran zai amsa su, saboda haka
shi ma wannan bincike ya zo da waɗansu tambayoyi kamar haka:
(I)
Yaya Makaɗin Tauri yake sarrafa
harshe cikin Waƙoƙin Tauri?
(II)
Waɗanne abubuwa ne makaɗin Tauri ya fi mayar
da hankali a kansu lokacin da ya ke wa ɗan Tauri Zuga?
(III)
Ta wace hanya makaɗin Taurin yake gina
maganganun zuge-zugensa?
(IV)
Ta ya Ma'anar kalmomin da makaɗin Taurin ke faɗi ke juyawa zuwa ga ɗan Taurin da ya
ambata da wannan kalma?
1.5 Iyakancewar
Bincike
Wannan
Bincike zai samu iyakancewar Nazarin turken zuga a Waƙoƙin tauri na Sale Kudo
Kusada, a cikin kiɗansa da yake wa 'yan
Tauri, Maza da suke a kewayen ƙaramar Hukumar Kusada ta Jahar
Katsina.
1.6 Gudummuwar
Bincike.
Wannan
Bincike ya zo da waɗansu gudummuwa kamar
haka;
I.
Haskawa manazarta da sauran ɗaliban ilimi irin
yadda ake amfani da Halayen dabbobi da sifofinsu domin tsoratar da abokan
hamayya.
II.
Samar da abun bita ga ɗaliban ilimi masu
sha'awar nazari a harshen Hausa domin cikasa wani giɓi da kila binciken
bai rufe ba.
III.
Karawa rubuce-rubucen fannin 'yan
tauri yawa ta hanyar fayyace Ma'anoni na abubuwan da suka shafi Waƙoƙin tauri.
IV.
Adana salon sarrafawa harshe na wasu
'yan tauri ta yadda ba za su salwance ba.
1.7 Turken Zuga
Newman
(2007) ya bayyana koɗa kai da nufin wasa
ko kururuta wani.
Bargery
(1934) a nasa ya bayyana koɗa da wasa kai ko nuna fifiko.
Gusau,
(2008) ya yi bayani a kan turken Zuga
Koɗa kai (wasa kai) a waƙar baka a inda tun a
farko ya fara da cewa „magori wasa kanka da kanka‟, koɗa kai ko wasa kai na nufin mutum yafaɗi wata shahara ko ƙasaita ko ɗaukaka da yake ganin
yana da ita. Wato ambato ne na abubuwan ƙasaita ko burgewa da
mutum yake da su ko yake aiwatarwa. Wani bi akan haɗa da wuce gona da iri
inda mutum zai bayyana fifikonsa a kan sauran jama‟a, ko ya nuna wata
zalaƙarsa ko basirarsa wasu da sauran hanyoyin fifitawa.
A
irin wannan hali mutum yakan zuga kansa da kansa ne. Masanan sun yi bayani
gwargwadon fahimtarsu a kan koɗa kai kuma sun yi tararraya don gane da abin da koɗa kai yake nufi, wato
fito da wata shahara ko isa ko fifiko da wani mutum yake da shi. Kodayake, Gusau
ya yi nazari a kan turken koɗa kai a waƙar baka ya fito da
misalan ire-iren wasu waƙoƙin baka ne da ake samu mawaƙa sun koɗa kansu a ciki amma
shi wannan bincike zai kalli wasu ɗiya ne daga cikin Waƙoƙin Sale Kudo kusada
da kuma irin yadda ya yi amfani da wasu kalmomi domin nuna zuga ko koɗa wani ko wasu jama‟a ko kuma kansa.
1.7.1 Sarrafa Harshe
Sarrafa
Harshe ɗaya ne daga cikin
rassan adabin baka. Masana Harshen Hausa sun bambanta wajen ambatom wannan
reshe na Adabin Baka. Farfesa Ɗangambo (1984), ya ambace shi da
Hikima da sarrafa Harshe, wanda daga nan muka ciro wannan suna. Sai kuma Yahaya,
Zariya, Gusau da 'Yar adua (1992), suka kira shi da ''Azancin Magana".
Zarruk,
Kafin Hausa da Alhassan (1987), sun ambace shi da ''salon Magana". Amma
dukkan su sun yarda da zamowar: Kinaya da Siffantawa da Jinsintarwa da
Abuntarwa da Kambamawa da kuma Dabbantarwa a matsayin rassan Sarrafa Harshe.
Sarrafa
Harshe Salo ne da Bahaushe yake amfani da shi wajen sarrafa magana ta sigogi
mabambanta da ke ƙayatar da zance ko isar da wani babban saƙo ta cikin hikima
kuma a wasu 'yan kalmomi dunƙulallu. Da su ake yi wa zance ( na
baka ko rubutacce) ado; Adon Harshe.
Adon
Harshe dabara ce ta yi wa magana (kirari) kwalliya domin ƙara ma shi armashi da
daɗi wanda shi ne
ma'auni na gwada iya zance da balagar ɗan Adam ke da ita ga Harshensa da kuma sauran
abubuwan da ke kewaye da shi. Adon Harshe dai a taƙaice yana nufin wasu
hikimomi ne ko dabaru da ake bi wajen kauce wa miƙaƙƙiyar hanyar faɗar magana a rubuce ko
a baka.
1.7.2 Ma'anar Kirari
Zarruƙ da Alhassan (1982 :
45), sun bayyana cewa kirari na ɗaya daga cikin wani ginshiƙi ko ɓangare da ake bayyana
al'adar al'umma kuma ya ke adana tarihi da taimaka wa al'umma wajen ci gaba
kamar kuma yadda ya ke taimakawa wajen nishaɗantarwa, ilimantarwa, da faɗakarwa.
Yahaya
(1992) yace kirari maganganu ne na kambamawa da ake yi wa mutum ko kuma shi ya
yi ma kansa, kirari kan ƙara kwarzanta wanda ake yi wa. Ana amfani da ƙwarewar zance wurin
yin kirari.
Sayaya
(2013: 41) yana ganin cewa kirari kalma ce wadda ta samo asali daga kira wato
makaɗi ne zai sa ganga ya
Kira gwarzonsa ko kuma wani lokaci a busa masa ƙaho. Wato a busa ƙaho a Kira shi.
Bunza
(2009) Asalin kalmar daga Kira take a sa kalangu ko ganga ko murya a kira wani
da ƙarfi
don ya fito a ɗebe tababan abunda
ake faɗa a kansa.
Dunfawa
(2004 : 38) yana da ra'ayin cewa kirari shi ne jera jimlolin Adabi masu amfani
da kalmomi waɗanda ko dai su
kasance masu kaifin ma'ana ko masu zurfin ma'ana kuma waɗanda aka tsara salon
siffantawa domin wasa ko kambamawa ko ingiza mutum ko wani Abu.
Junaidu
da 'Yar'adua (2007) sun bayyana kirari da cewa ''wani rukuni ne na salon
sarrafa harshe da Hausawa kan yi amfani da shi wajen nuna gwaninta da ƙimar harshe, ta
hanyar tsara kalmomi da suka dace da halayyan abubuwa a cikin lugga mai ban
sha'awa.
A
tawa fahimtar ina ganin Kirari zantuka ne na hikima da ake furtawa cikin zaɓaɓɓun jimloli domin
kwarzanta kai ko fito da ƙima ko matsayi domin burgewa da tsoratar da abokan
hamayya.
1.7.3 Ma'anar Tauri
Sayaya
(2009 : 40) Ya bayyana Tauri da cewa kalmar tauri na nufin gagara ko ƙin sarrafuwar wani
abu a sakamakon wasu dalilai na musamman da suke bambanta yanayin abubuwa.
Ire-iren waɗannan dalilai sun haɗa da sinadarai da
mutum ke samu daga itatuwa. Ko tsirrai, ko wasu abubuwa ya yi amfani da su
domin kare kansa daga rauni da wani makami da ka iya yi masa.
Bunza
(1995) yana mai ra'ayin cewa Tauri yana nufin abu yaƙi bari a sarrafa shi
ta yadda ake so. ko mutum ya faye ƙin karɓar shawara a kan ce
wane taurin kai gare shi. Mai irin wannan asiri na maganin ƙarfe ana kyautata
zaton wuƙa da takobi da mashi da duk wani makami na ƙarfe ba su fasa
jikinsa ba. Haka kuma yana iya sarrafa ƙarfe yadda yake so, ba
tare da wata wahala ba.
Buhari
(2022 : 12) Tauri tsumi ne na itatuwa da mutum kan sha ya yi wanka domin samun
kariya daga kowane irin kaifi ko tsini da ƙarfe ke da shi. Irin
waɗannan itatuwa akan
sarrafa su wani lokacin har da sassan jikin dabbobi domin bayar da irin wannan
kariya ta rauni da ƙarfe kan iya yi wa mutum.
1.7.4 Waƙoƙin
Tauri
Waƙar Tauri tana daga
cikin rukunin waƙoƙin baka na maza da suka keɓanta ga masu aiwatar da wata sana'a ta
musamman. Waƙoƙi ne da ake shiryawa cikin sigar kirari tare da kiɗa da take a lokaci
guda.
Makaɗin tauri kan ɗauki turken wani makaɗi ya gina nasa turken,
kasancewar su babu wani makaɗin tauri da ya yi wa kiɗan haye sai ya bi wani makaɗi kafin ya fara nasa
kiɗan, duk da cewa da
yawansu sukan yi gado ne a gida wurin mahaifansu.
Kiɗan tauri yana
bambanta dangane da yankin da makaɗan taurin suka fito, kamar a ƙasar katsina makaɗan tauri sukan yi
amfani da Bishi ne wurin kiɗan tauri Saɓanin ƙasar Kano da suke
amfani da Gangi domin aiwatar da kiɗan nasu. Haka kuma waɗanda suka fito
shiyyar Zamfara suna amfani da Kalangu, makaɗan yankin Kebbi sukan yi amfani da Duma ko
Ganga da kuma Kalangu a wurin kiɗan tauri, su kuwa na Katsina ta kudu da wani
yanki na Nijar sukan yi amfani da Kurya wajen kiɗan tauri. Wato dai kiɗan yakan bambanta da
shiyyoyin da makaɗan suka fito duk da
cewa abu ɗaya ne suke kiɗa a kansa.
1.8 Tarihin Makaɗin Tauri Sale Kudo A
Dunƙule
An
Haifi Malam Sale Kudo a Ƙauyen Magami cikin ƙaramar Hukumar kusada
dake a Jahar Katsina kimanin shekaru sittin da suka wuce. sunan mahaifinsa
Malam Audu, sunnan mahaifiyarsa Maimuna mutumiyar ƙauyen Magami ce. Anan
ya tashi ya girma kuma ya fara karatun Allo a hannun abokin Babansa sai dai
daga bisani mahaifin nasa ya miƙa sa hannun wani Malam Adamu, wanda ya
tafi da shi ƙasar Zazzau domin yin karatu, Sale Kudo ya samo karatu
sosai sai dai bai sauke ba suka dawo gida, daga nan ya ci gaba da karatu a
wurin Malaminsa na farko har zuwa wani lokaci.
Sale
Kudo bai yi karatun zamani ba sai dai ya yi yawon neman abinci a kudancin
Najeriya kamar su Lagos da Abuja inda ya yi sana'o'i daban-daban waɗanda suka haɗa da gyaran takalmi
(shoe maker) da yankan farce da sayar da rake da sauransu.
1.8.1 Asalin Inkiyar
Kudo
Sunansa
na Asali Salisu, sai dai mutane na ce masa Kudo saboda tun yana ƙarami abokan wasa
suka sa masa Kudo kuma yake amsa sunan, bayan da ya shahara a kiɗan tauri sai sunan ya
ƙara
fitowa sosai ta yadda in ba an haɗa da kudo ba sunan ba ya tasiri akansa.
1.8.2 Yanayin Sale
Kudo
Sale
Kudo baƙi ne dogo mara jiki ya ɗan duƙa ya yi doro, yana da
gashi a bisa kansa sannan ba ya barin gemu a haɓarsa, yana ajiye gashin baki, ga iya
magana sai dai ba shi da murya sosai ko waƙa yake bakasafai
muryar ke fita ba, yana yawan sa riga kwot kuma duk kayan da zai sa zai ɗora wannan kwot a
sama. Mutum ne mai fara'a ma'abocin cin goro.
1.8.3 Sana'oin Sale
Kudo
Bayan
Sale Kudo ya bar karatun allo, ya fara bin abokan sa zuwa daji da nufin yin
farauta da kuma saro itace suna kawo wa zuwa cikin garin Kusada suna sayarwa, daga
nan suke kamo namun daji su yanka su babbake suna sayarwa a kasuwannin Rimaye
da Kankiya da kuma Kusada.
Wannan
ya yi sanadin faɗawarsu cikin farauta
ka-in-da-na-in wannan sana'a ta sanya shi jarunta ya kasance ba shi da tsoro, har
mahaifinsa ya lura da irin yadda ya mayar da hankali a Kan harkar farauta ya
fara ba shi laƙani na kariyar jiki da sauran tambaya.
Bayan
farauta Sale Kudo ya fara sana'ar noma, tun lokacin da yana taya mahaifinsa
aiki, har bayan da ya yi iyali ya ci gaba da wannan harka ta noma inda ya ware
gonar kansa, haka kuma bayan noman damina Kudo yana yin noman rani, tun a baya
Sale Kudo ya yi sana'oi daban-daban.
1.8.4 Sana'ar Kiɗan Tauri
Sale
Kudo ya gaji sana'ar kiɗan tauri a wurin
mahaifinsa sai dai kafin ya fara kiɗan bishi da can kiɗan kalangu ya ke yi, Sannu
a hankali ya fara amfani da bishi har ta kai ya jingine kalangu ya kama kiɗan tauri.
Ya
tsunduma cikin kiɗan sosai lokacin da
Hakimin Kankiya ya bukaci Babansa da ya je su tafi Katsina hawan sallah, sai
mahaifinsa ya umarce shi da ya ɗauki ganga ɗaya ya bi tawagar Kankiyan Katsina su tafi
domin shi ba zai iya barin tawagar Bebeji ba Hakimin Kusada kasancewarsa a ƙarƙashin gundumarsa.
Haka Sale ya je Katsina aka yi wasan sallah lafiya a ka gama, ganin haka sai
Babansa ya bashi ganga guda ta sa ta kansa kuma ya ci gaba da ba shi dabarun kiɗan har zuwa lokacin
da ya haƙura da kiɗan taurin ya kasance salen ya mamaye duka ƙasar Hakimin Kankiya
da kuma ta Kusada a matsayin shahararren makaɗin taurin yankunan.
Sale
kudo ya yi kiɗe-kiɗen tauri da yawa ciki
hadda irin su:
•
Kiɗan Sarkin ƙyarma Yarima
•
Kiɗan ɗan Sarauta
•
Kiɗan Sarki Gambo
•
Kiɗan Sarkin Dawa
Zubairu
•
Kiɗan Bahago Taushe Dama
Badamasi
•
Kiɗan Saminu Kan Kara
Kafi Ɗaka
•
Kiɗan Musa ba ka san faƙo
•
Kiɗan kwangi
•
Kidan kwakyara
Da
sauransu.
1.9 Garin kusada
Garin
Kusada yana daga cikin ƙananan Hukumomin Jahar Katsina, wadda a ka ƙirƙira a shekar 1996.
Gari ne na Malamai da ake wa kirari da ''Kusada kusa da Kano nesa da Birnin
Katsina'' Al'ummar wannan gari mafi yawansu Manoma ne da makiyaya kuma garin ya
albarkatu da 'yan kasuwa da ma'aikatan gwamnati, in aka duba taswira garin ya
yi iyaka da ƙaramar Hukumar Kankiya daga yamma, daga gabas kuma ya yi
iyaka daTsanyawa ta jahar Kano, a ɓangaren kudu garin na Kusada ya yi iyaka da ƙaramar Hukumar
Ingawa.
A
ƙididdigar
mutane da aka yi a shekarar 2006 garin yana da kimanin adadin mutane miliyan ɗaya da ɗari tara da tisi'in
da biyu da ɗari biyu da bakwai
(1992, 267). Garin yana da ƙauyuka da suke kewaye da shi, Alhaji
Nuhu Sada shi ne Bebejin Katsina Hakimin Kusada na yanzu a ƙarƙashin ikonsa akwai
Dagattai guda goma sha uku da suka hada da: kofa da Tufani da Magami da Yashe
da Ɓauranya
da Kusada da Kafarda da Aganta da Mawashi da Dudunni da Boko da kuma Kaikai.
Haka kuma kowane Dagaci yana da masu Unguwanni kamar yadda tsarin Sarautar
gargajiya ya shinfiɗa.
1.10 Naɗewa
Wannan
babi an bayyana abubuwa kamar haka gabatar da babin wadda a cikinta ne aka
bayyana abinda wannan binciken ya ƙunsa da kuma abubuwan
da babi suka yi magana . Haka kuma bayan gabatarwa babin ya bayyana abubuwa
kamar haka, muhimmancin bincike da manufar Bincike da farfajiyar bincike da
dalilin ci gaba da bincike da tambayoyi da taƙaitaccen tarihin makaɗin Tauri da kuma
garin Kusada.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.