Kundin Digiri Na Biyu (M.A Hausa Culture) Da Aka Gabatar A Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya, Jami'ar Bayero Kano (Maris, 2024)
Nazarin Tubalan Turken Zuga A Waƙoƙin 'Yan Tauri Na Sale Kudo Kusada
Aminu Musa
07036420021
ameenumusa12@gmail.com
BABI NA
UKU
3.0 Share Fage
A
wannan babi za a kawo hanyoyin da aka bi wajen gudanar da wannan bincike sannan
a yi bayanin samfurin bincike da sigar bincike, duk a cikin babin za a kawo
kayan aikin da aka yi amfani da su wajen gudanar da wannan bincike. Haka kuma
za a kawo sunayen waɗanda aka tattauna da
su domin samun bayanai tun daga 'yan tauri da makaɗan tauri da masana da
manazarta da kuma masu alaƙa da aikin tauri. Duk a cikin babin ne
za a kawo ɗa'ar bincike, sannan
a naɗe babin gaba ɗayansa.
3.1 Nau'in Bincike
Wannan
bincike yana ɗauke da nau'in
bincike bi-bayani domin zai yi sharhi ne a kan salon sarrafa Harshe a cikin waƙar tauri tare da
bayyana irin yadda ake sarrafa kalmomi da sunayen wasu halittu yadda ya dace da
tunanin mai sauraro, tare da kawo irin tasirin da wannan salon zai iya kawo wa
a cikin al'umma musamman ga waɗanda su ke sauraren waƙoƙin tauri da masu
kallon wasannin su. Don haka bincike ne bi-bayani kamar yadda (Doryn 2011) da
(Cresswell 2019) suka bayyana sharhantau na cikin nau'in bincike na bayani.
3.2 Sigar Bincike
Wannan
bincike yana da sigogi kamar haka; bayyana yadda makaɗin tauri Sale kudo ke
kallon Halaye da ɗabi'un wasu halittu
yana danganta ɗan tauri da su. Da
kuma yadda yake amfani da hikima da azanci wajen sarrafa abubuwa na amfani da
suke da baiwa ko buwaya, yana alaƙanta masu yin tauri
da su a cikin kirarin da yake masu. Kamar yadda Cresswell (2019) da Doryn
(2011) da Muhammad (2012) suka bayyana cewa ''ana bukatar manazarci ya fito da
inda binciken sa ya dosa kai tsaye''.
3.3 Kayan Aikin
Bincike
Wannan
bincike an yi amfani da kayayyaki kamar su, kundayen bincike, da Littattafai, da
mujallu da aka zaɓa da wayar hannu
domin naɗar bayanai a yayin
tattaunawa da na'ura mai ƙwaƙwalwa da takardu da alƙalamin rubutu.
3.4 Ginshiƙan
Bayanai
Akwai
waɗansu bayanai masu
muhimmanci waɗanda za a bi ta kansu
a gudanar da wannan bincike, ga su kamar haka:
3.4.1 Karanta Ayyuka
A ɗakin
Karatu
A
wannan nazari an yi bitar Ayyukan da suka gabata da suka haɗa da Kundayen bincike
tun daga kundin digiri na ɗaya da na biyu da na uku, haka suma bugaggun Littattafai
an duba su, sannan a ka yi bitar maƙalu da mujallu da
sauran takardun ilimi waɗanda suka danganci
wannan bincike.
Duk
a waɗannan kundaye da
Bugaggun Littattafai da muƙalu an duba su ne a waɗannan wurare:
-
Ɗakin karatu na sashen
koyar da Harsunan Nijeriya, Jami'ar Bayero Kano.
-
Babban ɗakin karatu na Jami'ar Bayero Kano.
-
Cibiyar nazarin Harsunan Nijeriya da
Adabin baka da fassara da ke jami'ar Bayero Kano.
-
Ɗakin karatu na Sashen
Hausa na Jami'ar Umaru Musa yar'adua da ke Katsina.
-
Babban ɗakin karatu na Jami'ar Umaru Musa
yar'adua dake Katsina.
-
Ɗakin karatu na Sashen
Koyar da Hausa na Kwalejin ilimi ta Isa Kaita da ke Dutsinma, Katsina.
-
Babban ɗakin karatu na kwalejin Gwamnatin
tarayya da ke katsina
-
Ɗakin karatu na
Hukumar Adana tarihi ta Jahar Katsina.
Sannan
an samu wasu Littattafai a shagon siyar da Littattafai na Alhikima da ke cikin
garin Kaatsina, an samu wasu a makarantar jeka- ka-dawo ta Gwamnatin jahar
Katsina da ke Rimaye ƙaramar Jukumar Kankia Jahar Katsina.
3.4.2 Tattaunawa Da
Wasu 'Yan Tauri
An
tattauna da wasu 'yan tauri domin bunƙasar wannan aiki, an
nemi bayanai daga bakinsu, domin su ne suke aiwatar da kirare-kirare da kuma
ganin cewa su ne makaɗan tauri ke wasawa da
irin wannan salo na zugawa. Waɗannan bayanai da aka samo daga bakinsu zai taimaka wajen
cim ma manufar wannan bincike. Daga cikin 'yan tauri da aka tattauna da su
akwai waɗannan:
I) Buhari Canko, Ɗan
shekara Arba'in (40)
A
garin Rimaye ƙaramar hukumar Kankia
Ranar
10 /08/ 2022
Kamar
tsawon minti Hamsin (50m)
Mai
sana'ar Gini da kuma huɗɗar Tauri
II) Sama'ila Miloniya,
ɗan
shekara Hamsin (50)
A
garin Naƙawa, ƙaramar Hukumar Kusada
Ranar
12 /08/ 2022
Kamar
tsawon minti talatin da biyar (35m)
Mai
sana'ar harbi da kuma sayar da ƙore
III) Buhari Lawal
Yashe, ɗan shekara Hamsin da biyar (55)
A
garin Yashe, ƙaramar hukumar Kusada
12
/08/ 2022
Kamar
tsawon Awa ɗaya
Ma'aikacin
Gwamnati, kuma ɗan tauri
IƁ)
Nababa UK, ɗan shekara Hamsin da shidda (56)
A
garin tsohuwar Dokoki, ƙaramar Hukumar Kankia
Kamar
tsawon Awa ɗaya
Manomi,
kuma ɗan Tauri
Kuma
an yi masu tambayoyi kamar haka:
-
Waɗanne Irin Abubuwa ne Makaɗin tauri ke siffanta ɗan tauri da su, a
lokacin da ya ke zuga sa domin fitowa cikin fili?
-
Ko makaɗin tauri kan ji kunyar faɗar wasu kalamai kai
tsaye a cikin Waƙoƙin sa, ta yadda sai ya sakaya ma'anarsu?
-
Wace irin zuga ce ta fi Jan hankalin ɗan tauri
-
Ko makaɗin Tauri ya taɓa alaƙantaka da wata
halitta a cikin waƙarka, kuma ya ka ji lokacin da ya ke ma kirarin?
4.4.3 Tattaunawa Da
Masana Da Manazarta A kan Kiɗan Tauri
A
wannan bincike akwai buƙatar tattaunawa da masana, al'adun Hausawa domin samun
bayanai a kan cikakkiyar al'adar kiɗan tauri, domin samun nasarar cim ma wannan
manufar aiki.
Daga
cikin masana da Manazartan da aka tattauna da su da waɗanda ake sa ran
tattaunawa da su a nan gaba har zuwa kammaluwar aikin akwai:
-
Farfesa Aminu Lawal Auta - Jami'ar
Bayero kano
-
Dr, Abdulhadi Uba Gabari - Jami'ar
Bayero Kano
-
Dr, Muhammad Ammani- Jami'ar Bayero Kano
-
Dr, Nura Lawal - Jami'ar Bayero Kano
-
Dr, Mustapha Sha'aibu Dafana- Jami'ar
Umaru Musa yar'adua Katsina
-
Dr, Abubakar Sani Sayaya - Ma'aikatar
yaɗa labarai da ɗab'i, ta Jahar
Katsina
-
Dr Aminu Galadima Ɓatagarawa- Jami'ar
Umaru Musa yar'adua Katsina
-
Dr, Sabiu Alti - Kwalejin Ilimi Isah
Kaita Dutsinma, Katsina
-
Malam Tukur Aliyu - kwalejin ilimi
Isah Kaita Dutsinma, Katsina
-
Malam Umar Ibrahim- GDSS Rimaye, Kankia
Katsina
-
Malam Buhari Lawal Yashe- GDSS Rimaye
Kankia Katsina
Daga
cikin tambayoyin da aka yi wa waɗannan masana da manazarta da kuma waɗanda za a yi masu a
nan gaba akwai waɗannan:
I)
Shin an taɓa yin Nazarin salon
sarrafa harshe a cikin kiɗan tauri?
II)
Ko an taɓa Nazarin Waƙoƙin wannan makaɗi Sale Kudo?
III)
Miye fahimtar ka game da salon sarrafawa a
cikin kiɗan tauri?
IV)
Ko masu kiɗan tauri na duba wasu
halayyar dabbobi a lokacin da suke danganta ɗan tauri da su.
4.4.4 Tattaunawa Da
Masana Ilimin Tauri
Domin
samun ganin kwalliya ta biya kuɗin sabulu, akwai bukatar tattaunawa da masana ilimin
tauri (Masu wasan tauri) domin samun bayanai mabambanta waɗanda za su taimaka wa
wannan bincike ya cim ma manufofinsa. Daga cikin 'yan tauri da aka tattauna da
su akwai:
I) Salisu Rabe, ɗan shekara talatin da
biyar (35)
A
garin Rimaye, ƙaramar Hukumar Kankia
Kamar
tsawon minti arba'in (40m)
Ɗan Tauri
II) Hassan Ya'u, ɗan shekara sittin da
biyu (62)
A
garin ɗankawari, ƙaramar Hukumar Kankia
Jahar Katsina
Kamar
tsawon minti hamsin (50)
Ɗan Tauri
III) Sani Na'aba, ɗan shekara hamsin da
shidda (56)
A
garin Magami, ƙaramar Hukumar Kusada, Jahar Katsina.
Kamar
tsawon awa daya (1)
Dan
tauri
IƁ) Iro ɗan baiwa, ɗan shekara talatin da
biyar (35)
A
garin Sabarawa, ƙaramar Hukumar Kusada Jihar Katsina
Kamar
tsawon minti Hamsin
Ɗan tauri
Ɓ) Musa Leko, ɗan shekara sittin da biyar (65)
A
garin Rimaye, ƙaramar hukumar kankia jahar katsina
Kamar
tsawon minti Hamsin
Ɗan tauri
ƁI) Isihu Auta, ɗan shekara talatin da uku (33)
A
garin Dokoki, ƙaramar Hukumar Kankia Jahar Katsina
Kamar
tsawon minti arba'in
Ɗan tauri
ƁII) Sa'adu Gambo, ɗan shekara arba'in da biyar (45)
A
garin Nasarawa, ƙaramar hukumar Kankia Jahar Katsina
Kamar
tsawon minti talatin
Ɗan tauri
Kuma
an yi masu tambayoyi kamar haka:
I.
Wane kallo ka ke wa Tauri ?
II.
A faɗi yadda ake yin kirari
III.
Yaushe ka fara yin wasan tauri
IV.
A faɗi ire-iren maganganun da ake cikin
kirari
3.4.5 Jugowa Da
Sauraren Hira Da Aka Yi Da Makaɗin Tauri Sale Kudo
Domin
samun ganin kammaluwar wannan bincike da kuma samun madosar aikin da sanin
yadda za a gabatar da shi, an tattauna da makaɗin tauri Sale Kudo Kusada a gidansa da
ke garin magami, tare da yi masa tambayoyi a kan irin salon da ya ke amfani da
shi a lokacin da yake waƙa, ko yake so ya taso da wani ɗan tauri cikin fage.
An yi amfani da takarda da biro da wayar hannu domin naɗo irin amsoshin da ya
bayar. Daga cikin tambayoyin da aka yi masa akwai:
I.
Ko za ka bamu taƙaitaccen tarihin
rayuwarka?
II.
Shin kana amfani da salo wurin aiwatar
da waƙa, musamman sakaya wasu kalmomi?
III.
Ya ka ke yin zuga a cikin waƙoƙin ka?
IV.
Waɗanne abubuwa kafi lissafowa a cikin Waƙoƙin ka?
3.5 Da'ar Gudanar Da
Bincike
Wannan
bincike ne da aka gudanar cikin natsuwa da ladabi da girmama waɗanda aka je neman
bayanan bincike wurinsu. An yi amfani da kalamai masu taushi da sunkuyar da kai
domin inganta aikin da ganin an samu ingantattun amsoshin da ake bukata Haka
kuma an yi amfani da shiga ta mutunci ta kaya na kamala a lokacin aiwatar da binciken.
Bincike ne da ya gudana cikin ladabi da girmama waɗanda aka je neman bayanai wurinsu.
3.6 Naɗewa
A
wannan babi an yi cikakken bayani akan sigar da wannan bincike yake da ita da
kuma bayanin kayan aikin bincike sannan an kawo ginshiƙan bayanai da lissafo
ɗakunan karatun da aka
ziyarta a lokacin binciken haka kuma an yi bayanin tattaunawar da aka yi da
masana da manazarta da kuma masu sana'ar tauri. A cikin babin ne aka yi bayanin
hira da aka yi da makaɗin tauri Sale Kudo
Kusada sannan aka yi bayanin ɗa'ar bincike daga ƙarshe aka naɗe babin da kammaluwa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.