𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum. Wanda aka yi
masa laifi kuma aka nemi ya yafe, sai ya nemi sanin menene amma ba a gaya masa
ba. Sai dai aka cigaba da neman ya yafen kawai, sai shi kuma ya ce, ya yafe. To
hakan ya yi?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul
Laah.
Asali dai kamata ya yi a gaya
masa irin laifin da aka yi masa, domin haƙƙinsa ne. Amma idan aka ɓoye masa saboda waɗansu dalilai, kamar idan
ana ganin bayyana masa zai haifar masa da damuwa ko wani tashin hankali ko
rashin yarda da amincewa da wanda ya aikata masa laifin, duk da ya tuba. Ko
kuma idan zai ɗauke
shi ga rabuwa ko yanke zumunci da shi, ko rashin amincewa da mutane. Ko kuma
shi ma ya shiga aikata hakan ga wani, ko dai waɗansu
matsaloli irin waɗannan.
A duk lokacin da aka yi tunanin
hakan to bai kamata a gaya masa irin laifin da aka yi masa ba, kamar yadda abin
yake a nan. Dalili kuwa, malamai sun yarda cewa ƙofar ɓarna
a cikin al’umma ƙuntata ta ake yi, bai halatta a faɗaɗa
ta ko a yalwata ta ba.
Idan shi kuma da aka yi wa laifin
ya amince har ya yarda ya yafe laifin ba tare da ya san nau’insa ba, malamai
sun nuna hakan ya yi. Kuma ya wadatar ga shi mai neman a yafe masa laifin, in
sha Allah.
Allaah ya saka wa mai irin wannan
halin na yafiya da alkhairi, kuma ya shigar da shi cikin waɗanda yake magana a kansu
cewa
وَلْيَعْفُوا وَلْيَصْفَحُوا أَلَا تُحِبُّونَ
أَنْ يَغْفِرَ اللَّهُ لَكُمْ وَاللَّهُ غَفُورٌ رَحِيمٌ
Lallai (masu daraja) su yafe kuma
su kawar da kai. Ko ba ku son Allaah ya gafarta muku ne, alhali kuma Allaah Mai
gafara ne Mai Rahama? (Surah An-Nuur: 22).
Allaah ya gafarta mana gaba-ɗaya.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah
Assalafiy
Ga masu tambaya sai su turo ta
WhatsApp number: 08021117734
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/K7RkQRMf2b57l3UENoJ1Or
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.