𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Malam, mahaifina ne Allaah ya yi
masa rasuwa, ya yi azumi guda 24, a ranar na 25 ne Allaah ya yi masa rasuwa.
Shin za a biya masa sauran azumin da ya rage ne?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Manzon Allaah (Sallal Laahu
Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce
إِذَا مَاتَ ابْنُ آدَمَ انْقَطَعَ
عَمَلُهُ إِلَّا مِنْ ثَلَاثٍ
Idan ɗan
Adam ya mutu aikinsa ya yanke sai dai ta hanyoyi uku.
Wannan ya nuna: Daga lokacin da
muslmi ya rasu ne ayyukansa suka ƙare. Babu wani aiki kuma da ya hau kansa
daga wannan lokacin.
Don haka, wanda ya yi azumi na
tsawon kwanaki ashirin da huɗu,
kuma ya rasu a ran na ashirin da biyar babu komai a kansa, domin iyakan abin da
Allaah ya ƙaddara
masa kenan a rayuwarsa. Don haka babu wani abin da za a rama masa, kuma ba za a
kama shi da abin da ya rage na azumin watan ba.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaahi
Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.