𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum. Wani ne yake
bin mutum domin ya kashe shi ko ya lalata masa rayuwa ta hanyar sihiri, to ko
ya halatta shi ma ya bi wannan hanyar domin ya ga bayan sa kafin shi ya iya
cutar da shi?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul
Laah.
Bai halata musulmi ya bi hanyar
sihiri domin warware sihiri ko domin ya kare kansa ko ya ɗauki fansa a kan wanda ya
cutar da shi ta hanyar sihirin ba. An tambayi Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa
Alaa Alihi Wa Sallam) a kan ‘an-nushrah’ wato warware sihiri sai ya ce
هِيَ مِنَ الشَّيْطَانِ.
Daga aikin sheɗan ne. (Ahmad ya riwaito
shi, kuma sanadinsa nagrtacce ne).
Abu-Daawud ya ce: An tambayi
Ahmad a kan hakan sai ya ce
ابنُ مَسْعُودٍ يَكْرَهُ هَذَا
كُلَّهُ.
Ibn Mas’ud yana ƙyamatar
dukkan hakan.
Wannan a kan an-nushrah da ake
bin hanyoyin bokaye na mu’amala da sheɗanu
kenan.
Amma idan hanyar ruqya ta Sunnah
ce, kamar a samu musulmin kirki masani ya yi wa mara lafiyan ruqya da ayoyin
Alqur’ani da Sahihan addu’o’in Sunnah, wannan daidai ne ba laifi ba ne.
Qataadah ya tambayi Sa’eed Bn Al-Musayyib (Rahimahumal Laah) a kan mutumin da
aka yi wa sihiri har ba ya iya kusantar iyalinsa, ko za a iya warware masa? Sai
ya ce
لَا بَأْسَ بِهِ، إنَّمَا يُرِيدُونَ بِهِ الْإصْلَاحَ
، فَأمَّا مَا يَنْفَعُ فَلَمْ يُنْهَ عَنْهُ.
Babu laifi ga hakan. Ai gyara
suke nema kawai da shi. Amma abin da zai amfanar ba a hana yin shi ba.
Wannan duk a cikin Fat-hul Majeed
(shafi: 302).
A taƙaice dai: Haƙuri
da dogaro ga Allaah su ne babban magani. Sai kuma kulawa da Zikirori da Addu’o’in da suka tabbata a cikin Sunnah Sahihiya.
Amma komawa ga bin hanyoyin
bokaye domin neman kariya ko ɗaukar
fansa a kan wanda ake zaton yana yin wannan abin, ba daidai ba ne. Kamar wanke
kashi ne da fitsari!
Kuma ƙara ƙarfafa
wa bokaye gwiwa ne da ɗaure
musu gindi a kan ɓarnarsu
da cigaba da yaɗa
sharrorinsu a cikin al’umma. Tun tuni dai Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa
Alihi Wa Sallam) ya yi tsawa a kan zuwa wurinsu, ya ce
« مَنْ أَتَى عَرَّافًا فَسَأَلَهُ عَنْ شَىْءٍ
لَمْ تُقْبَلْ لَهُ صَلاَةٌ أَرْبَعِينَ لَيْلَةً ».
Duk wanda ya je wurin mai duba
kuma ya tambaye shi a kan wani abu, ba za a karɓi
sallarsa na kwana arba’in ba. (Sahih Muslim: 5957).
Sannan kuma ya ce
« مَنْ أَتَى كَاهِناً أَوْ عَرَّافاً فَصَدَّقَهُ
بِمَا يَقُولُ فَقَدْ كَفَرَ بِمَا أُنْزِلَ عَلَى مُحَمَّدٍ
».
Duk wanda ya je wurin boka ko mai
duba kuma ya gaskata shi a kan abin da yake faɗa,
to ya kafirce wa abin da aka saukar wa Annabi Muhammad. (Ahmad (9536), Ibn
Maajah (639), Ad-Daarimiy (1176) daga hadisin bu-Hurairah kuma Sahihi ne in ji
Al-Albaaniy a cikin Sahih Ibn Maajah da Al-Arna’uut a cikin ta’aleeq na
Musnad).
Allaah ya ƙara tsare mu daga
sharrin masharranta na ɓoye
da na bayyane.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah
Assalafiy
Ga masu tambaya sai su turo ta
WhatsApp number: 08021117734
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.